← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 103

Sashe 41

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙafa yaƙara ɗagawa ya sauke ta akan gwaiwar ta da ƙarfi take ta bada wani irin ƙara, itama kanta saida tasamu dama Muryar ta tafito tayi ƴar ƙaramar ƙara, ɗayar ya sake ɗagawa zai sauke Amra tayi saurin tsugunnawa a wajen cikin kuka tace dan Allah ka rabu da ita mai tayi maka,

Tamke fuskar sa ya ƙara yi tare da daka mata tsawa yace ta matsa,

Da sauri ta matsa tare da ƙara fashewa da kuka suma su Ameeshan kuka suke sun nanne waje guda kuma sai kace anyi musu dole ance su tsaya agun sai sun gani sunƙi tafiya,

Meer ba fasa abun da yayi niya ba saida ya karya É—ayar ma, sannan ya É—ago yana kallon su ganin yanda suke kuka gaba É—ayan su hakanne kawai yasashi dakatawa dan sai yanzu da yayi wani tunanin yagano ashefa yaran jikokin tane, dole suyi kuka, ita kuma Ameesha ko uban mai yasa zatayi kuka sai yaji ma ta bashi haushi,
tsawa ya daka musu yace subar gurin gaba É—ayan su,

ba shiri suka tafi suna kuka kamar ƙananun yara.

"Kirasu su fita da ita, Meer ya faÉ—a yana kallon Khalid,

zaro wayar sa Khalid yayi, ya kara a kunne ana É—agawa yace ku shigo, sannan ya sauke wayar,

yana saukewa saiga motar Æ´an sanda nan ta shigo cikin gurin,

a gaban su tayi parking sannan ƴan sandan suka fito, suna fitowa duk suka ɗaga hannu suka sarawa Khalid tare da ƙamewa, shima sara musu yayi sannan yace 'arest har,

Matan cikin sune suka kamata suka yi mata kama kama suka sakata a bayan motar da ƙyar, bayan sun sakata suka ƙulle motat, ɗaya daga cikin su ce taje gaban su Khalid saida ta ƙara sara masa sannan tace "sir baza afara kaita asibiti ba ayi mata treatment kafin mu wuce can ɗin dan naga taji ciwuka da yawa, abun zaiyi hurting ɗin ta da yaw......, Bata ƙarasa ba Meer ya dakatar da ita tare da jefa mata wata muguwar harara, sannan yace ahaka za a rufe ta bance a taimaka mata da komai ba, in ba ruwa ba,

Sunkuyar da kai tayi tace ok sir sannan ta ƙara salute ɗin sa ta juya ta shiga mota suka tafi da ita,

Hannu Meer yasaka ya shafi fuskar sa tare da sakin wani ɗan ƙaramin tsaki yana sauke ajiyar zuciya na gajiya, sannan ya dubi, Khalid cike da gajiyawa da rashin ƙwarin jiki, yace masa "what next,

Khalid ya ɗanyi murmushi yasa yaɗan dafa kafaɗar sa yace congrats mutumi na next shine kaje ka gyara jikin ka, sai muje aji da sauran sai kasamu ka huta gajiyar duka, irin wannan duka gaskiya da soja ka dace da hakan zata faru nasan da masu laifuka da yawa baza suyi ba duk wanda ya haɗu dakai bazai so ku ƙara haɗuwa ba, Allah da hanya sai na kaika soja matsalar kawai shine sar......,

"Enough! Khalid banason irin wannan Allah ya kiyaye uban mai zanyi da aikin soja agarin wallahi ƙasar nan sam batayi ba,

"To ya zakayi kuma É—an cikin tane zama dole bayanda zakayi, "Khalid ya basa amsa,

Meer yace hmmm dole kaf duniyar nan akwai wanda ya isa yayi min dole akan abun da banyi niyaba, shiru yayi kafin kuma Khalid yace wani abun ya É—ora cewa.....,
"kaga malam muje ni ba wani shiri da sanyi sai naba kowa gurin sa, hankalina zai kwanta, yana faÉ—a ya yi gaba bai jira jin ta bakin saba,

Ganin hakan yasa Meer yayi saurin binsa da sauri,

Loƙacin da suka shiga cikin fada nan ma ashe faɗa ake tsakanin Fulani da sauran ta hau masifa itama harda su duka tafara kai musu akan bazata haƙura da abun da sukayi mata ba sun cuceta da farko sun zalince ta sun juyar mata da mahaifa ita da ganin gudan jinin ta sai a lahira, gashi sun jawo mata zaman gidan ƙasa, gashi kowa yana mata kallon muguwa, taso tayiwa Ammah ma tas amma ganin Meer yasa ta rabu da ita iya nasama ya isheta,

Shiyasa yana fita tajawo hajiya Sarah tafara dukan ta saida kyar ka ƙwaceta, ana ƙwatar ta kuma sai ta koma kan wata daga duk wanda takama kawai duka take kai musu zagi kam sun shashi kamar zai fito ajikin su, saida ƙyar Abu ya dakatar da ita dan gurin ma gaba ɗaya haukacewa yayi da haya niya, ga masifar gwaggo itama ba abarta abaya ba,

shigowar Meer ne da yadakatar dasu shima da ƙyar sannan aka samu komai ya lafa,

guri yasamu ya zauna sannan ya kalli Papa yace "wane irin hukunci yake son a yanke musu, yanzu, dan gaba ɗayan su masu laifi ne, da farko yayi tunanin suma duk atarkata su akai su kotu, sai kuma yayi wani tunanin kafin akaisu dole sai sun fara hukuntasu sannan zasu kaisu a ɗaure su agidan yari gaba ɗayan su, babu wanda aka ɗagawa ƙafa,

Papa yabawa Meer dama yace ya yanke musu duk hukuncin da ya dace, dasu,

Ana agaban kowa Meera yace ya yanke musu hukunci zaman gidan yari na dindin daga nan har ƙarshen rayuwar su, sannan kafin afita dasu zasu fara amsar hukunci acikin gidan nan za akaisu ɗakin ƙasa kamar yanda suke sawa akwai wasu suma zasu shiga ciki a horasu horo mai tsanani sannan a fito dasu akaisu prison dan babu wanda yakamata yaci gaba da rayuwa cikin mutane domin zaman su aguri haɗarine kowa mummunar zuciya garesa, idan aka barsu nan gaba ma zasu iya yin son zuciyar tasu su kara cutar da al'umma,

Nan kowa yayi na'am da hukuncin nasa, sannan aka nemi inda wanda yake da magana yayi kafin zama yaƙare,

Kande ce tace tana da magan, aka bata izni,

Sannan tace dan Allah tana neman alfarma kafin a yanke mata hukunci tana so taga ƴaƴan ta anemo mata koda nan cikin gidanne ta gansa kafin ta tafi sannan tagaya masa abun da Ammah tace ya koma garin su, dan tasan batasan inda ɗayan yake ba, ta haƙura da ganin sa idan kuma Allah yayi haɗuwar su Allah yasa su haɗu,

Da farko Meer ƙin amincewa yayi saida Maama tasaka baki sannan, ya yarda, nan suka shiga tunanin mai irin siffofin da ta lissafo, amma duk da haka basu gano ba, a loƙacin Meer ya fita da kansa aka tara masu aikin gidan, ya shiga dubasu yana tambayar su amma aka rasa,

haka ya dawo cikin fadar yake sanar dasu ba'a samuba wata ƙil ƙarya take, har anyi shiru da maganar za afara wata, Sarki Salahudeen yace "yana da magana, nan aka bashi izni,

Cikin sanyin yanayi ya tashi ya fara da cewa "bana tunanin ƙarya take domin abubuwan da ta faɗa a halayen sa da kamannin sa a yanda tafaɗa akwai mai irin su agidan nan, sai yanzu naƙara tabbatar da hakan da nayi tunani, to amma abun mamakin anan shine, shi wannan mai halayen yana da mahaifiya indai kuma ba shima ƙarya akayi masa ba.....,

Da sauri Fulani ta tashi ta karɓeshi da cewa ƙwarai kuwa wallahi wanda kake zance shine ma duk yanda ta faɗa haka yaron nan yake ni zan baku labarin sa,

Wallahi wannan munafukar zaku tuhuma tasan komai, tunda tace ɗanta ne nidai tunda nake da ita ban taɓa ganinta da ciki ba, hasalima bata taɓa yin aure ba, wai amma loƙaci ɗaya tace min ɗanta ne alugunguma shegiya zo nan dan kutumar ubanki kiyi mana baya ni uban waya baki ɗa ta ƙarasa maganar tana jawo kan Hajiya Sarah ta dungurar da ita agun tana nuna ta da yatsa tace Wallahi itace wannan fa tafi kowa mugwar munafuka ce sheɗaniya anya ma nikam matar nan bata haɗa dangi da sheɗanu ba (oh Fulani da masifa mai hali baya fasa halin sa)

Nan kallo ya koma kan Hajiya Sarah da Fulani, Fulani ce ta ƙara dungurin ta tace "bazakiyi magana ba, shiru Hajiya Sarah tayi bata tanka mata ba,

Papa ne yayi mata magana da kansa sannan tace "Eh ɗanta yana cikin gidan nan ba ɗa na bane ɗanta ne, Ammah ce ta bani shi tace in riƙeshi har zuwa girman sa idan ya girma kuma zata karbesa ya shigo cikin masarautar amma bada sanin ko shi waye ba kawai zata na bashi kulawa ne sannan ba ko wane aiki zai ringayi ba agidan, daga nan kuma da yayi wayo sosai tasa nace masa ya daina yin komai sannan ya ringayiwa Fulani rashin mutunci duk ranar da tace zata yi masa wani abu yace mata yasan sirrin ta kuma zai tona idan taci gaba da abun da take anan zai ƙara samun damar yin duk abun da yaga dama, marabar sa da ƴan gidan kawai shi su suna part ɗin ƴan gida shi kuma yana part ɗin bayi masu aiki,

Duk abun da tabani ni kuma sai inbashi amatsayin sa na ɗana tunda tun yana ƙarami yake hanuna ni na ƙarasa rainon sa shiyasa yayi tunanin nice mahaifiyar sa,

Ranar da kuma yakira ni yace zasu kasheshi, duk tsarin mune saboda a loƙacinne burin kowa yake daf da cika ta haka kawai za asauke sa daga mulki su kuma su ɗora waɗanda suke so, shiyasa aka kamasa ranar da yarinyar ta shiga ɗakin sa mukuma mukayi amfani da wannan ranar muka tura mutane aka gaya wa sarki abun dake faruwa shi kuma ya ɗau zafi dalilin da yasa akayi musu wannan dukan kenan mutanen ma su suka shirya su, sukayi musu wannan dukan,

Shiyasa da ya kirani nazo dan in tona asirin kowa yaji hakan ma tsari ne, daga nan kuma sai abu ya taɓaɓɓare rishe ya juye da mujiya, dan a loƙacin so nayi ingudu sai kuma hakan bai yiyuba........,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣
Chapter 41 · 0% Book details