← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 103

Sashe 10

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga suka fara tafiya masu aikin gidan kama daga masu bawa fulawoyi ruwa zuwa ga drivers ɗin daman duk sun sanshi dan haka suma suka shiga gaidashi, amma halin da yake ciki ya hanasa amsa musu, kawai sukayi gaba basuyi nisa ba, suka ƙaraso suna daf da shiga ciki idon Hamza yakai wajen parking lot ɗin su inda yake yaga wata mace da gajeran wando da riga kanta ko ɗan kwali babu badan gashin kanta ba ma zakayi tunanin namiji ne, saboda yanda ta gwame tana ta wanko ƙasan tayar mota gashi duk ta jiƙa jikin ta, ƙafarta ma babu takalmi,

A iya sanin sa yasan mata basa wankin mota ko acan masarauta bare kuma waje ga kuma maza da suke zaune babu abun da suke amma mace na wankin mota,

Sam har yasaka ƙafar sa ɗaya zai tura ƙofar falon Hamza yayi saurin jawo sa baya, Sam har tsorata yayi jin irin jawowar da Hamza yayi masa, ransa har yana ɓaci ya ɗago zai sauke masa kwandon masifa,

Hamza yayi saurin ɗaga hannun sa yana masa nuni da inda yarinyar take tare da cewa kai nan gidan wai har mata ma suna wankin motoci abun da ko amasarauta bantaɓa gani ba,

A hankali Sam ya sauke idanun sa akan ta, jiyayi gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwar gaba, ji yayi zuciyar sa na barazanar tarwatsa masa ƙirji tafito, take idon sa suka fara canza launi ya zaro su suka firfitowaje, ba komai bane ya haddasa masa jin wannan abun ba face tozali da idanuwansa sukayi masa da yarinyar da akace masa ta ɓata ma'ana idanun sa sunyi masa mugun gani, da yake ganin abun kamar a mafarki kamar almara,

Ko kallon gabansa bayayi ya shiga takawa a hankali zuwa inda take,

Hamza tunda yaga irin kallon da yake mata yasamu amsoshin tambayoyin sa, sannan kuma tunanin sa da hasashen sa sun zama gaskiya dan haka yaja gefe ya zuba masa ido, bai ƙara cewa komai ba,

Sam yayi tafiya wajen rabi kafin yaƙarasa wajen ta, saboda akwai ɗan tazara tsakanin inda suke zuwa parking lot ɗin,

Tagama wanke tayar da take wankewa ta ɗago zata wanke ɗayar sai brush ɗin ya faɗi ƙasa, da sauri ta juya ta ɗauka saboda sauri take 10 minutes aka bata tagama wanke ta tas inba hakaba kuma jikinta yagaya mata, tana wankewa da hannu ɗaya take wankewa ɗayan hannun kuma tiyo ne tana wankewa tana ɗaurayewa,

tana ɗauka ta juya da sauri taci gaba cikin sauri tanayi tana Allah yasa loƙaci bai kusaba,

jitayi kamar su tafiya ta a bayan ta da sauri ta juya atunanin ta ko loƙaci yayi antaho dukanta,

Tana juyawa idon ta ya sauka akansa itama gabanta saida ya faɗi ganin sa da tayi, ɗan ƙifƙifta idon ta tayi dan ta tabbatar wa da kanta gaskene ko kuma mafarki ne ganin dai da gaske shine yake tunkarota,

Bata san loƙacin da tayi watsi da brush ɗin da tiyo ɗin kuma ta manta a inda take, ta kwasa aguje ta nufi wajensa tana zuwa tafaɗa jikin sa ta rungume sa ƙam tare da fashewa da kuka tana ƙara duƙunƙune sa, atare suka sauke ajiyar zuciya,

Sam tsaye yayi yakasa motsi ya damƙe idanun sa yana jin wani irin zafi da raɗaɗi acikin zuciyar sa, da ƙyar ya iya ɗaga hannun sa yayi croping ɗinta ya rungumeta shima,

A hankali ya shiga buɗe idanun sa ba zato ba tsammani abun mamaki saiga hawayen masu ɗumi sunfara saukowa daga idon sa.......✍️✍️✍️

   
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

                 *_Typing........✍️✍️_*

                        
_______A hankali ya shiga buÉ—e idanun sa ba zato ba tsammani abun mamaki saiga hawayen masu É—umi sunfara saukowa daga idon sa.......,

Hannun ɗaya yasa yayi saurin share hawayen sa, sannan yaƙara rungumota sosai kamar zai mayar da ita cikin jikinsa sai karkarwa yake,

Saosai take kuka dan ba ƙaramin jin daɗin ganin sa tayi ba yazo a loƙacin da take buƙatar sa,

Kasa jurar kukan nata yayi gashi ya kasa yi mata magana, duba gefe da gefen sa ya shiga kalla yaga yanda maza suke kallon ta abun da yafi ƙona masa rai kenan ganinta da wando da riga ga kanta ba ɗan kwali ga maza dake yawo awajen suna kallon ta a haka,

A hankali ya shiga rabata da jikin sa amma sai taƙara riƙeshi cikin kukan tace please don't go, kar ka tafi kabarni tana faɗar haka ta ƙara rungumesa tana sake fashewa da wani kukan,

Wani abune yazo masa wuya, baisan loƙacin da ya ɗagata ba gaba ɗayan ta yariƙe ta ƙam yafara tafiya da ita ajikin sa baibi takan shiga cikin gidan ba kuma ya manta da Hamza dake bayansa,

cikin ɓacin rai yake tafiya har yaƙarasa bakin gate ɗin ya fita da ita,

Hamza dake bayansu tunda yaga ya ɗauke ta yana niyar barin wajen shima ya ɗaga ƴan matan ƙafafun sa ya mara musu baya fuskar sa ɗauke da murmushi,

A kusan tare suka ƙaraso gurin motar da sauri Hamza ya buɗe masa ƙofa back seat shikuma yashigar da ita ciki da niyar ya ajiye ta ya fito, amma yana niyar fitowa tayi saurin  riƙeshe saboda gani take idan ya tafi kamar tafiya zai yi yabar ta,

cikin motar ya koma kusa da ita sannan yajawota ya rungumeta ta gefe yafara bubbuga bayan ta, yayin da zuciyar sa take masa wani irin suya,

Kuka ta ƙara saki sakamakon taɓa mata bayan da yayi saboda zafin da taji,

Tana kukan tace, "Dan Allah karka
barni anan wallahi mutuwa zanyi kasheni zasuyi ka mayar dani gidan ka kaini wajen baba na dan Allah mitafi, duk tabi ta rikecemasa sai surutu kawai take kuma ta riƙeshi ƙamƙam kamar yaci mata bashi,

Wasu zafafan hawaye yaƙara ji sun cika masa ido loƙacin da idon sa suka sauka akan wuyan ta yaga wani baƙin shatin bulala jikin nata ya shiga kalla da tun ɗazu bai kulaba ashema gaba ɗaya jikin ta duk ya ɓaci da shatin bulala har su ƙafar ta da hannun ta,

Sosai ya shiga mamakin yanda akai hakan tafaru to daman hajjaju haka take mutuwa ce ko kuma dai akanta ta fara muguntar me yasa zataci amanar sa yakawo mata yarinya amana amma tayi mata haka ta mayar da ita ƴar aiki harda su duka wannan wane irin mugunta ce hajjaju take da ita, shi abun da yafi tsaya masa ma arai da tace wai yarinyar bata gidan ta gudu alhalin tana nan da baizo ba kenan  kasheta suke shirin yi,

Kallon ta yaƙarayi yaga yanda take kuka kana gani kasan daga ƙasan zuciyar sa take yinsa,

Wani abu ya ƙaraji tundaga kan ƙafatsa har tsakiyar kansa ji yake wannnan shatin bulalar kamar ajikin ta kamar ajikinsa kamar shi aka daka kukan ta kwan har can ƙasan zuciyar sa yake jinsa, duk dauriyar sa nema yake yakasa jurewa, gashi yama kasa furta mata koda da kalma ɗaya ne, Daƙyar ya iya ɗago jajayen idanun sa dasukayi masa nauyi, ya kalli Hamza dake waje ya juya musu baya, ɗan dukan glass ɗin yayi dan bazai iya magana ba, Hamza na jin haka ya juyo da sauri, yana kallon sa ta cikin glass ɗin motar, da hannu yayi masa alamar da su tafi,

Zagayawa Hamza yayi ya buÉ—e driver seat yashiga tare da tayar da motar yafara janta Saida ya hau kan titi sannan yace "ina mukayi?

Daƙyar sam ya iya buɗar bakin sa yace "gida, daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba, ya maida dubansa kan sumy dake jikin sa tana kuka har yanzu, ita kanta batasan me yasa takasa daina kukan ba har yanzu,

Hannu biyu yasa ya ɗagota ya zaunar da ita tare da riƙo fuskar ta da duka tafikan hannun sa,ya zuba mata jajayen idanunsa yana ƙarewa fuskarta kallo da tayi sharƙaf da hawaye, sannan ya shiga goge mata hawayen, amma yana goge mata wani na zubowa, kansa yashiga girgiza mata, yana ƙara goge mata, gannin dai hawayen nata sunƙi tsayawa baisan loƙacin da yaƙara jawota jikin sa ba ya ƙara rungume ta, murya cike da rauni dan shima ji yake dama yayi kukan ko zai samu sassaucin raɗaɗin da zuciyar sa take masa, cikin ƙasa ƙasa da murya da yakasa ɗagata yashiga cewa "plss ya isa haka kidaina kukan nan ko kinaso nima kisani kukan, da sauri ta ɗan girgiza masa kai, yace "to kiyi shiru ya isa haka,

itama cikin kukan tace baza ka ƙara tafiya kabarni ba kuma dan Allah ka kaini inda ka ajiye min mahaifina, ina son ganin sa,

"Tohm" kawai yace mata yaƙara yin shiru dan bayajin zai ƙara kaita wani wajen ko gidansu bazai mayar da itaba saboda ɗayar matar da yake kyautata zaton matar ubace shiyasa take gallaza mata azaba, dan haka babu inda zai kaita shima mahaifin nata idan yana sonta to saidai ya canza mata gida amma bazasu ƙara zama guri ɗaya da itaba, 
Chapter 10 · 0% Book details