← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 103

Sashe 7

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana sane da ita shima bai ƙara yi mata magana ba, yaje ya ɗauko kayan zaƙin sa yadawo kan gado ya zauna yafara ɓare wata choculate me ɗan girma ya ɓare ledar yafara kaiwa baki yana taunawa a hankali kamar wanda akayiwa dolen sha,

Time to Time tana ɗan satar kallon sa, ganin choculate ɗin kuma sai kallon yayi yawa dan har haɗiyar yawu take saboda ba ƙaramin burgeta ba tayi, ji take kamar taje ta ƙwace a hannun sa,

Shikam ko kallon inda take bai kalla ba amma yana sane da ita a ɗakin so yake yaga iya gudun ruwan ta idan ya gama abun da yake batazo ya tashi zai nuna mata asalin kalar sa kafin zata kiyaye sa tafara jin tsoron sa dan yaga alamun  kamar bata tsoron sa, bai gama wannan tunanin ba yaga alamun tafara takawa daga inda take, a ransa yace "kin taimaki kanki da jikin ki yagaya miki,

A hankali Ameesha ta shiga takawa zuwa inda  yake amma fa ita anata gurin bawai tsoran sane yasa zataje ba face choculate ɗin hannun sa da takasa kawar da kai so take kawai taji ta abakin ta kuma ta ga ba ɗaya ce da shiba akwai wasu agefen sa, shiyasa zataje wajen sa ko ta halin ƙaƙa taci koma tace yabata, dan ba kunyar sa take jiba, kawai dai tana jin tsoron sa tsoran ma ba wai canba tunda su Maama na gidan bai isa ya cutar da ita ba tasan za a hanasa,

A É—an gefen sa ta tsaya sai kuma tayi saurin tsugunnawa saboda tunawa da tayi sai kayi biyayya idan kana son abu tunda kwa abunsa take so dole tayi biyayya badan Allah ba,

Bai kulata ba yaci gaba da shan abarsa, tana zaune tana tunanin tayanda za ayi ta tambaye sa É—in ko kuma tayi masa wayo yanda bazai gane ba har yabata,

Ɗan dagowa tayi taga baya kallon ta sai ta gyara zama daga tsugunnen da take tayi zama dirshen harda tanƙwashe ƙafafun ta, tana ɗan murza yatsun hannun ta, sannan tace "uhmm ya Sameer ta kira da cikin ƙasa ƙasa da murya me cike da ladabin ƙarya,

Cak ya tsaya da shan choculate É—in da yake, tare da saurin mayar da duban sa gare ta cike da mamakin kiran sunan sa da tayi kai tsaye duk da tasa yaya amma dai Sameer É—in da tace shi yafi basa mamaki meyasa bazata faÉ—i yanda kowa yake faÉ—a masa ba, sai wanda ba kowa yake faÉ—a ba,

Sarai tasan kallon ta yake dan haka ta taƙi ɗagowa ta kalle sa, a haka kanta a sunkayi ta ci gaba da maganar, tace "uhmm yaya Sameer daman wata magana nakeso muyi dakai shiyasa nazo amma kafin muyi mufara gama shan choculate ɗin sai muyi, maganar,

Ɗan kallon ta yaƙarayi akaro na biyu yana mamakin jin furucin ta wai mufara gama shan choculate ɗin daman tare da ita suke sha ne ko kuma wani abun zatace tace haka, zuciyar sa tayi saurin bashi amsa da cewa may be tana so tace kafara shanyiwa sai muyi ta manta tace mu fara shanyewa, hakanne ma wata zuciyar ta basa amsa, dan haka sai ya kawar da kai daga kallon da yake mata, yace "ina ruwan ki da shan abuna kawai kiyi maganar ki ina kunne keji ba, ba baki ba ko,

Shiru tayi tana ƙara tunanin yanzu kuma me zatace wata zuciyar kawai tace kisa hannu ki ɗauka ba yayan ki bane, abun sa ai naki ne, da sauri ta girgiza kai aranta tace wannan jarababban mutumin ba imani ne dashiba baisan wannan tsaf idan na taɓa zai iya ci min mutunci,

"Malama kina ɓatan loƙaci idan ki bari nagama baki faɗi abun da yakawo ki ba bazan saurare ki ba kuma sai na saɓa miki kamanni rainin hankali da kikai min kafin kifita kinji ni ko, yayi maganar yana ƙara kai choculate ɗin bakin sa caraf akan idon ta jitayi kamar ta fisgota daga hannun sa,

Jin batun nasa tagane bai fahimci abun da tace masa ba kenan kodai baiji ta da kyau ba, wannan tunanin yasa taƙara cewa, "To taya zan iya magana da abu abakin na,

Wannan karon kwa da sauri ya juyo ya kalle ta yana kallon bakin nata dan yaga abun da take ci É—in dan shidai baiga komai a hannun taba da zata ci dan shi har yanzu bai fahimci inda yaren nata ya dosa ba,

Ganin ba komai yace "meye abakin?

Duk yanda taso ya fahimce ta sa kwana kwanar ta dan har magana take masa tana kallon choculate É—in dan yafi fahimta amma yanuna mata baisan abun dake nufi ba saboda daga baya ya fahimceta ganin tana takallon abar hakanne yasa ya gane so take ta sha saboda tsabar kwaÉ—ayi irin nata amma sai shima yana nuna mata yafita iyawa ya nuna baisan ma tanayi ba,

Rufe ido Ameesha tana taƙaicin ƙin fahimtar ta da yayi da taga dai da gaske idan ba ofulu ofulu ta fito masa ba tagaya masa kai tsaye bazai taɓa fahimtar taba, dan haka ta rufe ido kawai, tace "Babu yanzu amma yanzu zan saka kaban abar hannun ka ko kaban wata nima ido fa gubane kazo gabana kana tasha to ni kuma fa, ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka tana turo baki saboda ta ƙosa tafara sha, kunsan Ameesha da kwaɗayin zaƙi itama kamar shi take koma ince har ta fishi saboda ita ba iya kwaɗayin bane harda yarinta,

Ƙuri yayi mata yana kallon ta da mamaki daman kwaɗayin nata har yakai haka tayi roƙo ba abata, aikwa zai koya mata hankali akan kwaɗayi kenan ko wani wajen ma taje haka zatayi, saboda bata da hankali, yana sane ya fara sauri ya shanye ta tsaf sauran kuma ya kwashe su daga gefen sa, ya zuba su a aljihu, kuma bai tanka mata ba,

Ameesha ƙwalla har ta fara cika mata ido tana shirin zubowa tayi saurin mayar da ita tana mamakin rowar da yayi mata daman marowaci ne bata sani ba(daman ance 🎶🎶mai ƙwaɗayi shi yasan gidan me rowa inji adamu ɗan gidan su gwanja hakane wallahi🎶) zancen haƙƙun gwanja)

Wata dabarar ce ta faɗo mata dan haka sai tayi saurin miƙewa tsaye ta koma gefen sa ta zauna cike da rashin tsoro sai kawai ta kamo hannun sa, ta ɗora akan cinyar ta,

Shikuma cike da mamaki da taƙaici da jin haushin hakan da tayi masa ya janye hannun da sauri ta ƙara riƙewa tace wai meye haka ka tsaya mana kaga abun da zanmaka ko zan cutar dakai ne to bana cin hannun mutane ni ba mayya bace,

"Sai ƙafa" taji yafaɗa ɗan murmushi tayi tace a'a itama ƙafar ba ci nayi ba tunda ga abarka nan ajikin ka kuma loƙacin ma kai kajawa kanka, da ka ɗaga ni da hakan bata faruba yanzu kuma babu abun da kayi min dan haka ba abun da zan maka nima, dade kayi min wani abun to da sai na rama danni bana yafiya idan aka min sai na rama,

Jinjina kai yayi cike da gajiya wa da surutun da take masa dan har fa Allah ya gaji so yake tafita ta bar masa ɗaki amma tunda yaji tace magana suke so suyi shiyasa ya rabu da ita kuma daman shima yana so tabashi labarin yanda akai ya koma cikin falo jiya da ana ruwa da kuma warke wasa da wuri, warke tasa da wuri ita tafi komai ma tsaya masa arai dan ba ƙaramin mamaki yayi ba da faruwar hakan,

Akaro na biyu yaƙara ƙoƙarin janye hannu nasa batare da ya ce mata ƙala ba, amma still sai ta ƙara riƙewa itama, mai makon tayi abun da zatayi sai ta tsaya tana kallon hannun nasa, da ta riƙe da nata sai kuma ta shiga haɗa sa da nata wai zatayi comparing da nata,

Ɗagowa tayi tana kallon sa tana taɓe baki tace "ashe ma baka fini haske ba, kamar ma na fika Allah kuwa kalli kaga hasken mu ɗaya, kai da kataso ma acan cikin larabawa kana hutawa, nikwa da na tashi cikin wahala amma hasken mu ɗaya, nasan ma idan nasamu hutu na zama ƴan mata sai na fika haske daman na fika kyau nima kuma zanyi karatu inyi aiki inzama me kuɗi shima infika daga nan bazan ƙara jin tsoron kaba tunda nafika da komai idan kace zaka min wani abun insaka bodyguard ɗin su lallasa min kai kuma daman ina nan banmanta ba sai nasa an ramamin muguntar da kayi min loƙacin da naje gidan saboda baka da tausayi ka taka min ƙafa bayan kasan tanayi min ciwo sannan kasa na shafa aboniki a fuska ta saboda ka riƙa a mugun ta, shiru tayi tana ci gaba da kallon hannun nasa,

Sannan ta ɗago ta kalle sa ganin har yanzu bai tanka mata ba, sai gyara zama tana ƙara damƙe hannun nasa sannan tace "wai dan Allah ina tambaye ka, me yasa baka da tausayi idan kana mugun ta daɗi kaji eh? tayi maganar tana kafe sa da dara daran idanun ta,

Tabbb babbar magana yama tafi duniyar tunani wai yaushe yayi sabo da yarinyar nan da har zata na gaya masa magana son ranta kuma wai zata dena jin tsoron sa nan gaba duk wanda zai iya gaya maka maganganu irin haka ai bawani tsoron ka da yake ji, gaskiya yayi sake yarinyar wallahi tagama rainasa, tagama kaishi ƙarshe kuma dan haka baisan ma me zaiyi mata ba ya huce,

yana cikin tunanin ta katseshi tare da ƙara nanata masa tambayar da tayi masa,

Haɗe rai yayi yanda zata tsorata da shi yace ke dalla mahaukaciya sakar min hannu ki fice daga ɗaki kafin in ɓaɓɓalaki agunan kinzo kin isheni da surutun banza ko ni sa'an wasan kine, daman maganar da ta kawo ki kenan kizo kicika min kunne da da surutun hauka,
Chapter 7 · 0% Book details