← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 103

Sashe 51

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasowa Ummy tayi tazo kusa da Meer zata riƙo hannun sa da niyar rarrashin sa sai kawai ya kawar da hannun nasa yana ja baya, yace "kada wanda yaƙara cewa komai kuma babu wanda ya isa ya hanani sakin ta tunda de ba da ita zaku zaun, ni kuma a tsarina babu aure ban shirya aure yanzu ba dan haka babu wanda ya isa yayi min auren dole, auren ma irin wannan wanda ko a tarihi ban taɓa jin sa ba ina aka taɓa aure irin wannan, wannan wacce irin tsana ce zakuyi min haka, sai kace marar gata,

Ummy ce ta ƙara daurewa tace "Meer ba haka bane ka tsaya ka saurara kaji bazamu taɓa yi maka abun da zai cutar dakai ba, wacce aka aura maka baza ka taɓa yin da nasanin auren taba kadena kiran ta da wani sunan marar kyau, domin ita ɗin ƙan...., Da sauri Meer ya dakatar da ita da cewa "Ummy bana so bana so bana sonta kuma bazan taɓa son taba ban damu da sanin ko wace ita ba na tsane ta, kuma ku sanar da ita,

Ni Sameer na saki matar da kuka aura min saki......,

Tabb babbar magana Ameesha will be a widow oooo,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

  
                        *_🅿️30_*

   
     'Ni Sameer na saki matar da kuka aura min saki......,

MEER..!!!!!  Abuu ya daka masa tsawa hakan yasashi dakatawa daga shirin ƙarasa furu cin sa,

"Wallahi kana sakin ta ina tsine maka albarka kuma kai da zama anan har abada saidai ka tafi kaje ka nemi wani gurin ka canza iyaye amma bamu ba, daga yau babu kai babu mu mutiƙar kasaki yarinyar nan wallahi, marar mutunci kawai, Abuu ya ƙarasa maganar yana zazzaro masa ido yana nuna sa da yatsa,

Shima Meer ɗin ido cikin ido yake kallon Abbu ɗin, ko kalma ɗaya ta kasa fita daga bakin sa, saida ya jira abu yayi shiru sannan yace "tsinuwa tsinuwa fa kace to sai me idan kayi min  nace sai me idan nabi duniyar ko daku ko baku zan iya cigaba da rayuwa ta, ni da wannan auren gwara tsinuwar ma dan banga bambanci ba,

Abuu ne ya ƙaraso kusa dashi baiyi aune ba kawai ya kwashe shi da mari cikin ɓacin rai yace "daman abun naka har ta kai haka to indai ka cika ɗan halak ka saketa kaga ni, nima zan nuna maka nawa ɓacin ran sai ka gwammce baka zo duniya ba wallahi, kaji ka sake ta nace!! Yana ɗaga masa murya tare da ƙara sauke masa wani marin, yana shirin kai masa wani Maama tayi saurin dakatar dashi,

   Maama tace "dan Allah ya isa kabari abi komai a hankali kowa ya kwantar da hankalin sa ɗaga murya ko faɗa ce faɗace ba namu bane tunda de kunsan gidan cike yake da mutane, ku rufa mana asiri agama komai ma zauna daga baya,

Babana dan Allah badan halin muba kabar wannan maganar da kake ka taimaka, kaji babana,, haɗa hannu wanta tayi waje guda tana roƙon sa,

Hakan da tayi ne yasa Meer ya daina ikirarin sakin da zai yi,

Juyawa yayi ya fice daga ciki fuuu bai ƙara cewa komai ba kuma har zuwa loƙacin da ya fita baisan matar da aka ɗaura masa aure da ita ba, dan baya son sanin tama bazai taɓa bari yagan taba, yafasa sakin tane kawai saboda darajar roƙon da Maama tayi masa amma badan haka ba sai ya saketa yau, ya ɗaga mata ƙafa zuwa loƙacin da ya ɗibarwa kansa,

Yana fita gaba ɗayan su suka sauke ajiyar zuciya tare da hamdalah Allah yasa bai sake taba da ya zasuyi ayi aure yau kuma ace anyi saki a ranar, ina aka taɓa haka,

Bayan fitar sa, Papa ya shigo shima nan ya sanar dasu su shirya yanzu za afara naÉ—i angama shirya komai,

Nan suka bashi labarin abun da ya faru sannan suka ƙara runguma suka fita daga ciki,

Cikin masarauta damƙam da mutane kowa kagani yana cikin farin ciki kamar gonar auduga, wani ɓangaren suna kiɗa kiɗe wani ɓangaren ana raye raye ga dokuna ana ta shirya su ana musu kwaliya, kar mu ɓata loƙaci, komai ya tafi yanda aka tsara cikin kwanciyar hankali, kowa ya shaida naɗin sarki Sameer Muhammad Sameer, an ɗorasa akan kujerar mulki, bayan an canza komai na cikin fadar amma banda kujerar andai gyarata anyi mata kwaliya an gyara ko ina ya sha gyara,

Meer tunda ya bar cikin falon ko can sashen baije ba ya nufi hanyar parking space ya buɗe motar sa ya shiga, yana shiga Khalid ya taho gurin da gudu yana yi masa magana amma kafin ya ƙaraso Meer yaja motar da gudun tsiya ko horn bayayi kuma ga mutane amma da haka yake gudu saidai kafin ya ƙaraso wajen mutane suyi saurin matsawa, a haka ya fice daga cikin gidan,

A ɓangaren Ameesha kam har zuwa wannan loƙaci labari bai iske su ba domin tunda suka shiga ɗaki yin Sallah basu fito ba hira kawai suke kamar babu gobe abincin ma can aka kai musu suka ci, ko da aka fara gudanar da naɗin duk basu fito ba, daman kuma Maama bataso a sanar da su shiyasa ta ƙara bada umarnin idan bata nan kar abar kowa ya shiga cikin gurin saboda kar wani ya shiga da maganar ɗaurin auren ciki,

Meer nayin wannan mahaukacin gudun dan ko gaban sa baya gani yana cikin yi bai ankara ba yayi sama da wata mata yayin da ta shigo gaban sa cikin gudu,

Da sauri ya taka burki yana dukan steering ɗin motar yana cije baki sannan yayi saurin buɗe motar ya fito tun kan yaƙarasa gurin shima yaƙaraso gurin da gudu yana haki, tsayawa sukayi atare tare da kallon junan su,

Da sauri Meer ya tsugunna yana shirin ɗago matar tsohon yace Sameer barta karka ta ɓata kaje kawai Allah ya kiyaye gaba,

Sak Meer yayi saboda jin tsohon da bai sani ba ya kira sunan sa.......,

Kawar da tunanin yayi saurin yi atunanin sa kodai kunnuwansa ne basu jiyo masa daidai ba, dan haka sai ya ƙara yunƙurawa yakai hannu zai ɗauke ɗago da ita, sai tsohon yaƙara cewa bana son taurin kai Sameer ka barta nace kayi tafiyar ka kawai bata ji ciwo ba suma ne kawai......,

Da kallon mamaki Meer yake kallon sa dan mutumin baiyi kama da mutanan da yakamata su san saba, ko ba agaya masa ba kayan jikin sa sun nuna masa yafi kama da mafarauci domin kayan fata ne ajikin sa irin na masu zaman daji, wandon jikin sa yaɗan ɗage masa ba har ƙasa ba sai takalmin danƙo baƙi rigar jikin sa kuma doguwa ce har zuwa gwaiwar sa shap ɗin ta kamar irin ta mata saboda na ɗaurin da akayi mata a tsakiya sai ƙasan ya buɗe bazar,
Sai gashin kansa da ba'a aske shi da yawa shima yayi wani iri dashi ga kuma wani uban kwalli da ya damɓara a idon sa,

Saida Meer ya gama ƙare masa kallo tundaga sama har ƙasa,

Shima kuma tsohon shi yake kallo yana ganin yanda yake binsa da kallon ƙurlla, tsoho da yagade Meer bashi da niyar daina kallon sa sai kawai ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa idan ka gama kallon nawa zaka iya tafiya ko,

ÆŠan sunkuyar da kansa Meer yayi tare da saurke ajiyar zuciya ya furzar da iskar bakin sa yana É—an karkaÉ—a kai, yana kallon gefen sa gurin shiru har yanzu babu mota ko É—aya da tazo ta wuce daman gurin ba a fiye wucewa ba saidai kaga mutane jefi jefi,

Tsugunnnawa tsohon yayi zai ɗauko matar dake kwance aƙasa har yanzu ko motsi batayi,

Da ƙyar ya ɗagota ya cicciɓe ta ya rataya ta a kafaɗa yana shirin barin wajen,

Meer yace "dakata,

Cak tsohon ya tsaya batare da ya juyo ba,

Sai shi Meer ɗinne ya taka yaje ta gaban sa yatsaya yana ƙara kallon sa na ƴan sakanni, kafin daga bisani yace "waye kai?

"Bawan Allah" 'tsohon yabasa amsa,

"A ina kasanni? Meer ya ƙara tambayar sa,

"Hmmm saninka ai ba abune mai wahala ba, tunda gidan ku ba ɓoyayye bane yaro taya zakayi min wannan tambayar,

ÆŠan jinjina kai Meer yayi sannan yace "amma ai kai bakai kalla da masu zama cikin mutane ba taya zaka sanni, kuma mai yasa ka hanani in taimake ta bayan kuma ni na kaÉ—ai ta,

"A'a yaro kabari kawai zanyi mata magani saboda kai ango ne bai kamata kasha wahala ba gurin ɗaukar ta, kuma tabbas ni bamai zama acikin mutane bane kamar yanda kaga yana yina amma kasani kaf mutanen gidan ku babu wanda bansani babu wanda bansan tarihin sa ba, dan haka kama daina mamaki, saboda gidan ku ba ɓoyayye bane kowa ma zai iya sanin ku da wanda yake zaune cikin mutane da wanda baya zaune saboda kimar ku da martabar ku dole kowa yasan ku,

Kallon sa kawai Meer yake har saida yajira yakai ƙarshen maganar sa sannan yace "ban yarda ba kagaya min gaskiya waye kai? kuma waye yabaka labarin tarihin kowanne mu taya hakan zata kasance,

Murmushi tsohon yasaki yace kana son sanin ko ni waye kabari duk sanda muka ƙara haɗuwa zaka san ko ni waye, shawara ta kuma agare ka ka riƙe Khadijatu da kyau domin itace hasken rayuwar ka idan kaje kace ina gaida ita, ita tasanni,
Chapter 51 · 0% Book details