Sashe 88
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa ya taya su farin ciki anayi, gwaggwo ma ba abarta a baya ba ta nuna farin cikin ta tsantsa, ga bayyanar ahalin ta gabaɗaya ƙwansu da kwarkwatar su babu wanda aka rasa, sannan anyi maganin duk wani makiri da mugu dake kusa dasu saidai kuma ayi fatan Allah ya kiyaye gaba,
Har ƴar ƙaramar walima aka haɗa akayi saukar Alqur'ani, aka ci aka sha, sannan akayi sada ka ga mabuƙatan wajen masu yawa,
A cikin sati ɗayan kamar yanda akace aka mayar da auren Abban Ameesha da Maman Ameesha, inda aka ware musu part ɗin su domin suje suci gaba da soyayyar su daga inda suka tsaya, part biyu akayi su da su Dadda da Baba, ƙofa ce kawai ta rabasu su da su, Ameesha tana ta murna wai zata koma part ɗin su Maman ta akace mata ai ga nata part ɗin can, suma can zasu koma ita da Meer tunda akayi maganar tayi shiru bata sake magana ba,
A ranar da zata koma can akayi rashin sa'a Bossay yakawo ziyara gurin ta, yasamu mummunan labari, bawan Allah harda su suma, koda ya farfaɗo kam sunbatun ya shigayi akan me yasa za'ayi masa haka bayan ansan shi yake sonta amma shine za'a aura mata, shikenan ancuce sa ankashe shi bazai taɓa aure ba, yasan ƙarshen sa yazo mutuwa zaiyi idan bai rayu da ita ba, kuka kam kamar ƙaramin yaro haka yaringa yi,
itama kuma antaɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi nan ta shiga daru itama akan sai ansa Meer ya sake ta dan baza ta zauna da shi ba, da suna rufawa juna asiri akan sun sa santa junan su, yau sai asiri ya tonu, kowa saida ya shaida rashin son da basuyi,
Dadda da batasan da auren ba daman tace meyasa za'ayiwa jikar ta auren dole to kuwa sai an sake ta tunda bataso, rikici yaso ya ɓalle Dadda itama ta dage sai an sakar mata jika,
Sude su Maama Abban Ameesha basu iya cewa komai ba kowa jan bakin sa yayi yai shiru,
Papa da yaga yarinyar bata so kuka take kamar ranta zai fita, kuma shi yafi son kwanciyar hankali baya son tashin hankali dan shi tun farko ma yaso yace asoke auren sai kuma yaji ance sun sa santa junan su shiyasa ma kawai tabar maganar sai kuma yanzu yaji aka sun haka, da haka sai yace.....
To shikenan indai basa so za'a warware auren dan haka Meer ya sake ta, kowa ta amin ce, Meer yana kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayar sa inka kalle sa sai ka rantse baya cikin falon duk wannan abun dake faruwa, ko a jikin sa,
Papa ne ya kalle sa yace "babana kaji meke faruwa ko ka sake ta dan Allah ko hankalin ta zai kwanta, kaga yanda take kuka,
Ai baba kamar yayi magana da gini, har saida ya kuma yi masa magana, Maama tayi masa, dan itama yanzu ta saduda ta haƙura da auren, baki tasa itama tace "Babana magana ake ma kasaƙe tan kawai tunda nasan kaima bakaso, kar mushiga haƙƙin ku,
Abuu ne yace "Haba Maama wannan wacce irin magana ce kuke yi, ai ba ayi haka ba, ni ina ganin kawai abarsu, idan akace su rabu su suke gaba damu ma kenan, bamu isa muyi musu abu ba suyi mana biyayya ba,
"A'a fa Abu kaman ta a yanda ka auro ni ko kamanta nima iyayena basa so na biyo ka, kaga kwa tunda banyuwa nawa biyayya ba, kar kaga laifin wani in yaƙi yi, daman abun haka yake kama tudeeni tudaan, duk abun da kayi sai anyi maka, duk dani da dalilin su na hanani auren ka, amma duk da haka banyi musu biyayyar ba, tunda akan gaskiya suka hanani dan haka, nima na goyi baya ina ganin kawai kabar kowa ya auri wanda yake so....
Harar ta Abuu yayi hakan yasa tayi shiru tana juyar da kanta gefe,
Sai yanzu Meer ya kashe wayar sa tare da mayar da wayar sa, aljihu yana miƙewa tsaye,
Cikin isa da taƙama yace "Ni zan wuce, wannan maganar taku ce, loƙacin da kuka ɗaura auren jin sa nayi kawai a masallaci, dan haka idan kun yanke shawara, idan anje sallar asuba gobe sai ku sanar da cewa an warware auren da kuka ƙulla kun aura kuma zaku saki matar, shikenan a wuce wajen, kowa sai ya huta, sai da safen ku yafaɗa yana ficewa daga cikin falon, dan tafiya sabon part ɗin sa, dan baiga dalilin da zai hanasa komawa ba tunda yagama kai komai nasa can,
Kamar ruwa ya shanye su haka suka koma harya fice babu wanda tasamu ƙwarin gwiwar dakatar dashi,
Abban Ameesha ne yace "shikenan ta faru ta ƙare sai kowa yayi haƙuri wanda bazai haƙura ba yakashe kansa, tunda de miji bashi da niyar sakin matar sa, in kuma zaku iya sakin ta kamar yanda yace batare da yawun bakin sa ya furta hakan ba, to bismillah nima de bacci nake ji, Norry muje ko yaja hannun matar sa suka bar galon zuwa nasu part ɗin dan su daman basu da bakin cewa akan wanna maganar duk abun da suka yanke daidai ne agurin su,
Abuu ma niƙewa yayi yace "to nimade babu abun da zance, masu so sai ku saketa, nima nayi nan, ya tashi ya tafi cike da jin daɗin rashin sakin da ba ayi ba, yaude Meer ya faranta masa,
Duk sun fice sun bar su Maama da jin kunya, Maama tasan halin Meer tunda yayi hakafa to sai ta Allah saidai suyi haƙuri ko su lallaɓasa,
Gurin ya rage daga Maama sa Dadda da Papa, sai Ameesha da tunda taji abun da Meer yace kukan nata ya tsaya cak, sai hawaye kawai dake sauko mata,
Papa ne yace to Allah ya kyauta ke kiyi haƙuri yanzu ki tashi kije kawai a san yanda za ayi daga baya, kinji ko, yana faɗa shima ya tashi ya tafi,
Suma duk miƙewa sukayi da niyar gobe kawai sai suyi mata nasiha su mayar da ita cen tunda bazai sake taba,
Tun daga wannan rana babu wanda ya sake maganar kuma har sati ya kusan zagayowa, Ameesha kam inbanda zaman É—aki ba inda take zuwa saboda sun gama exam É—in su, ga shi Azeema ma ta tafi gida,
Sai ta ɗan faki ido ta tabbatar bazata haɗu dashi ba, sannan take fitowa shima tana fitowa zata ƙara komawa, su Maama na sane da ita amma babu wanda ya kulata, sun bata zuwa nan da wani loƙacinne,
Shima a ɓangaren Meer ma bai ƙara bi takan ta ba hasalima harhaɗa kayan sa yake zai tafi ƙasar sa yamen, kuma baya tunanin ma zai dawo nan kusa, dan zaiyi wani muhimmin abu,
Bayan satin su uku da faruwar abun....., yagama shirya komai saida ya fito ma yace zaiyi tafiya akace masa matar saba, yace ai ba daÉ—ewa zaiyi ba, ita kuma karatu zatayi da ya tafi da ita,
Ba yanda aka iya dashi anaji ana gani ya tafiyar sa, ko neman inda take beyi ba,
Tunda ya tafi Ameesha ta samu freedom dan ji take ma kamar babu wani aure akan ta, har gwada kiran Bossay take amma baya ɗagawa danshi tun ranar bai ƙara zuwa gidan ba, kuma aranar da ya tafi ma saida aka kwantar dashi a asibiti kusan sati yayi a asibiti, kafin yaɗan samu lafiya, saboda yanda ya ƙwallafa rai akanta da tunanin ta, har ciwon zuciya ne yakama sa, tunda ya haɗu da ita bai taɓa tunanin zai rasa taba, tun ranar da yaganta ya fara sonta kuma yake hasaso musu rayuwar kasancewa da juna, shima a can ɗin har yanzu baya zuwa ko ina, kullum yana gida, duk yazama wani iri ga rama da yayi da duhu saboda yawan sakawa kansa damuwa,
Ameesha tun tana kiransa har ta daina ta fara fawwalawa Allah, satin Meer ɗaya, su Ameesha suka samu admission a Bez University dake Abuja, da ƙyar aka bar Ameesha zata tafi, dan cewa akayi saidai ta canza tayi nata ana amma ta dage da roƙo da magiya, sai akace saidai ta kira mijin ta idan ya amince sai taje idan kuma bai amince ba sai ta haƙura,
Babu yanda ta iya dole ta rufe ido ta kirasa da sabuwar wayar da Maama taba ta, saida yagama yi mata rainin hankali sannan ya amsa sallamar, daga nan ta gaya masa abun dake tafe da ita, dan rashin mutun sai kawai yace mata zamana kike, ko nace miki inzakiyi abu sai kin tambaye ni, yana faɗar haka ya kashe, kamar tayi kuka haka ta danne baƙin cikin, taje tace ya amince,
Nan suka fara shirye shiryen tafiya, acikin sati ɗaya ka gama shirya, komai har hostel ɗin da zasu zauna, an tanadar musu, kasancewar Abu yayi zaman Abuja kuma yasan mutane da yawa yana da alfarma, sai hakan ba basu wahala ba, suka samu komai cikin ƙanƙanan loƙaci,
Ranar Lahadi aka tafi akai kaisu, su su biyar, Ameesha, Azeema, Sumayya, sai twins Amra da Hamra,
Sumayya da Azeema suma da ƙyar Sam da Shettima suka bari, suka tafi dan su a tsarin su suna gama level 1, za a ɗaura musu aure, loƙaci ɗaya, a hakan ma saida su momma suka saka baki, sannan suka haƙura, amma sunce ana dawowa za a ɗaura auren,
Koda aka tashi kaisu ma tare dasu aka tafi, kowanne ya É—auki tasa budurwar suka ce a mota zasu tafi, su kuma su Ameesha suka shiga wata motar tare da Dadda da Maama, suka tafi, saida suka kaisu sukayi sallama dasu, sannan suka juyo gida, tundaga kan hanya suka fara missing É—in juna,
BAYAN SHEKARA 2,
A cikin shekara biyun nan, baifi sau uku su Ameesha suka zo gida ba, domin karatu soke sosai, kowa karatun sa, me wuya ne shiyasa basu tsaya wasa ba, dan ko samarin makaran ta basa kula kowa, duk da irin harin da ake kawo musu amma basa shiga harkar kowa,
Kuma duk dawowar nan Ameesha bata taɓa haɗuwa da Meer ba, abun har mamaki yaɗan bata, tanaso taji tun tafiyar da yayi baidawo ba ko kuma yana dawowa haɗuwa ce basa yi,
Haka suke komawa, tare da ƙara wata rakiyar,