← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 103

Sashe 3

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita ma Azeema murmushin ta mayar mata dashi sannan tace "ko kefa haka nake son gani ke da zaki zama babbar lauya jaruma ki ƙwatowa ahalin ki fansa da mahaifinki ko kin manta labarin da kika ban kince mahaifin ki yace kiyi karatu kiyi shari'a da maƙiyan sa ki fito dashi daga gidan yari kin tuna?

Kai ta ɗaga mata tana ɗan sakin fuskarta harda murmushi tunawa da tayi zata haɗu da mahaifin ta wataran gashi ana cewa suna kama sai taji kawai ta fara hasaso shi, ta ƙosa ta gansa, sosai tuna hakan yaɗan sata farin ciki, haƙoranta har suna fitowa waje ta gyara zama tana fuskantar bestyn tata da kyau tace "na tuna bestyna Allah ya barmin ke inajinki yanzu ya kike ganin zumuyi da videon nan,

Azeema itama cike da farin cikin ganin ta saki ranta, ta zauna kusa da ita tace yauwa haka nake sonji ƙawalli ta kuma ƙanwata,

Ɗan hararar ta Ameeaha tayi jin tace ƙanwata, tace "a ina nazama ƙanwarki mutaso tare da ke ki wani cemin ƙanwar ki ko wata ɗaya fa baki ban ba..,

Azeema tace "Allah ko Aunty babba to bari kiji loƙacin da aka haife ki da wayona har goya ki nayi abayana nida yaya saleem har faɗa muke akan goyaki, ke har wanka ma namiki kawai maleji nake ƙawance dake amma ruwa ba sa'an kwando bane yarinya,

Dukan wasa Ameesha ta kai mata a kafaɗa tace "wallahi banyarda besty ƙarya kike Allah kuwa amma bari zamu raba musu muje gurin dadd....., Kasa ƙatasawa tayi sakamakon tunawa da ita da tayi ashefa bata nan yanzu Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki yanzu jikin ta taji yayi sanyi,

Lura da hakan yasa Azeema saurin kawar da zancen tace besty kinsan me?

kai ta iya girga za mata kawai, Daman Azeema tasan bazata samu amsar baki ba daga gare ta dan haka saikawai ta share ta,

Ta ɗora da cewa "besty kina saurare na, dole ki tashi tsaye ko ince ku tashi tsaye dake da ɗan uwanki domin ku kaɗai me da zaku iya taimakon dangin ku dole ku haɗa kai wajen yin binciken ku yazama na bakin ku tare duk abun da ɗata yasani ya sanar da ɗaya tsintaiya ɗaya bata shara dole ku haɗa kanku, duk wani wanda zai taimake ku ba kamar yanda zakuyi ba mu namu kawai mu baku wata gudun mawar a wajen binciken ku bamu da ikon shiga wasu hurumin domin bamu ya shafa ba, kune zaku tsaya tsayin daka kuma kuna da damar shiga lungu da saƙo na cikin gidan nan wajen aiwatar da binciken ku, ku taka wanda kukaga dama ba kamar muba duba da yanda yayi ya tara duka mutanen awane ɗaya yana da iko dasu shiyasa yayi musu haka kuma dolen su suje koda ace da makiran acikin su amma mutum bai isa yayi jayayya dashi ba, dole yabi umarnin sa, amma idan bashi ba akwai wanda ya isa yasa su suyi haka idan kika cire manyan gidan, ɗan dakatawa tayi da maganar batare da ta jira amsar taba ta ci gaba,

Yanzu nidai a shawarar da zan baki itace wannan videon da muka ɗauka kar mubar kowa yasan dashi ko zuwa gobe ki sameshi a ɗaki kar kiji tsoran sa kiman ta da wannan babun ki ɗauki babun taimakon junan ku zakuyi naka sai naka dole zai fahimce sa kiyi masa bayanin komai sannan ki bada videon shi zaifi adana Sa akan yana wajen mu, daga nan kuma sai mufara sa ido akan kowa bincike mutane da yawa ganganci ne saboda zuciya bata da ƙashi wataƙil za a iya samun mai ruɓaɓɓiyar zuciya yana cikin ku yagama sanin sirrin ku daga baya kuma azo asiye sa da kuɗi ya canza ra'ayi to irin haka sai kiga ana ta abu amma ankasa cimma nasara akai arasa a inda matsalar take kiga duk abun da aka ƙulla sai ana fatan nasara sai kiga ya warware, amma idan yazamana muhimman abun yakasan ce agurin ku inyaso sauran da zasu taimaka muku kuma irin mu baiwuce na muje wani waje ko mu nemo muku kaza ko mu tsaya muku awaje kaza irin haka duk zai iya faruwa kuma zamu taimaka muku zai zamana ana taimaka muku amma su kansu waɗanda suke taimaka mukun basusan taƙamaimai inda kuma dosa ba ina fatan kina fahimtar inda zance na ya dosa,

Cike da gamsuwa Ameesha ta gyaÉ—a mata kai aranta tana mamakin yanda akai tunanin ta yazo É—aga dana tsohon nan,

Azeema taci gaba da cewa"bari in barki haka kar tunkina fahimta ki daina ganewa yanzu dai abun da zakiyi shine kiyi masa bayanin kuma ki basa sannan abu nagaba shine dole asan abunyi a shekarar nan mu zana jarrabawa gaba ɗayan mu, mu haƙura da sss 3 ɗinnan muyi gaba sannan mudage da karatu musamu result me kyau mushiga University ta yanda zakiyi sauri ki gama karatunki idan Allah ya taimakeki kisamu kifara aiki da wuri kinga koda hanya ne sai ayi mana nima can zantafi ƙafarki ƙafata, nasan tunda akwai kuɗi hakan bazai bamu wahala ba ko jinkirin rashin samun aiki, kinga komai zaizo mana da sauƙi ana tunanin fa amma ke ya kika ce,

Ɗan jimm Ameesha tayi tace "eh to banƙi ta takiba maganar gaskiya ce amma dai bari muyi maganar da maama inji me zasu yanke akai sai ayi komai da wuri, amma ba kya ganin kuma yanzu idan na surfafa da karatu taya zamu iya yin wani bincike hakan kamar zai raba min hankalina biyu ne daga ƙarshe inzo inkasa yin ɗaya, ga karatun low da wahala ga kuma tsawon shekarun da zamu ɗauka duk da bansan shekara nawa bane amma dai ina ganin kamar za aɗau loƙacin kafin nan kuma su ai tuni sun aiwatar da ƙudurin su akan mu,

"Haba besty kar ki damu da wannan bakisan ana iya shekara goma ba ana case ɗaya yaƙi kammaluwa saboda rashin shedu da hujjoji sai kiga ana ta ɗaga ƙara, ai babu abun da za afasa na bincike acikin gidan nan karfa ki manta bake kaɗai bace ga yayanki ga maama ga su Abu da ummy ga kuma su sam da su bossay kowafa yana kan bakansa na binciken abun da nake miki magana koda an kamasu kinga dole sai an shigar da ƙara to idan aka shigar da ƙarar kuma babu wanda zai tsaya muku duk da hujjojin da kuka tanada dan ganin sunyi nasara akanku zasu iya biyan ko nawane wajen kawar da waɗannan hujjojin naku su zama basu da amfani ko kuma asiye lauyan da zaku danƙawa case ɗin naku daga ƙarshe a watsar da shari'ar ke duniya fa yanzu cin hanci yayi yawa babu abun da baza a iya yiba mutuƙar aka bawa mutum kuɗi yanzu zaki ga mutum yacanza daga nagari ya koma na wiwi saboda kuɗi,

Ameesha tace "kuma fa hakane to shikenan duk da hakadai zamuyi magana amma ba yanzu ba saboda halin da ake ciki yanzu bata makaranta ake ba ga dadda da ta ɓata kinga hankalin su duk ba akwance yake ba amma da zarar anɗan samu nutsuwa zanyi musu maganar kar kidamu mudai ci gaba da addu'a Allah ya taimake mu ya dafa mana,

"Ameen" Azeema ta amsa mata sannan suka miƙe daga gurin zasu bar gurin juyawar da Ameesha zatayi taga wani ya juyawa da sauri shima yabar gurin gaban ta taji yayi wata irin faɗuwa, cike da fargaba hawaye har sunfara taruwa a idon ta tace besty mun shiga uku wai meyasa abubuwa suke zuwar min a haka,

Cike da rashin gamsuwa Azeema take kallon ta tace "me kuma ya faru?

Cike da rashin nutsuwa bakin ta har yana harÉ—ewa Ameesha tace "besty kingan sa can yanzu yabar wajen nan shikenan asirin mu ya tonu yagama jin duk tattaunawar da mukayi zaije ya faÉ—a musu nasan baza su barmu da rai ba besty ya zamuyi yanzu,

Azeema ma ba ƙaramin razana tayi ba da ganin mutumin basuga fuskar shiba kawai dai sunga bayan sa, dan haka bazasu iya sanin ko waye ba,

Da ƙyar Azeema ta iya aro jarumta da nutsuwar ta ta dawo da ita jikin ta sannan tayi saurin riƙe hannun Ameesha tace zama ko jinkiri ko maida yanda akayi bai taso ba mayi daga baya muyi sauri mutafi muje can tunkan su cinma mu a harabar gidan nan muje mu ɓoye wayar nan kafin ya farfaɗo ayi gaggawar sanar dashi nasandai ai ƙaryar su su shiga ciki suce zasu ƙwata kuma koda sun kama mu ai bazasu taɓa samun abun da suke nema ba, yanzu abu na gaba da zasuyi shine yanda zasuyi su samu wayar nan, tana maganar cikin sauri kuma tana jan Ameeaha suna sauri kamar zasu tashi sama ko gabansu ma basa kallo tafiya kawai suke,

Ameesha ce ta juya bayan ta ɗan ji take kamar ana binta amma da ta juya bata ga kowa ba hakan yasa taƙara ɗaga ƙafa suka cigaba da saurin Allah ya taimake su har suka ƙarasa inda Meer yatara mutanen nan, nanɗinma basu tsaya bi takan kowa ba suka wuce part ɗin maama Saida suka shiga sannan suka samu damar dakatawa da tafiyar da suke,

Loƙacin da suka shiga babu kowa afalon daman sunsan hakan zata faru baza su tadda kowa ba,saboda loƙacin da suke waje azaune su maama suka fito da shirin fita dalilin zuwan su wajen Meer kenan maama ce tace suke su kirashi yazo ya sallami mutanen nan yabari sai zuwa gobe yanzu fitar sauri takama su yadawo ya zauna a part ɗin tare da su Ameesha, suna ai kansu kuma suka fita daga gidan, su Amra kuma daman tunkafin loƙacin momma ta kirasu ahiyasa basu tafi tare da su ba, loƙacin sukaɗai ne, shine su kuma sukaje kiransa daga nan kuma kunnuwan su suka jiyo musu maganganun da Waziri yake Azeema tayi saurin ɗauko ƴar ƙaramar wayar ta tayi musu video da ita, duk da ba agani sosai amma dai ana iya gane fuskokin su,
Chapter 3 · 0% Book details