← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 103

Sashe 45

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_SLM, Pls ina ƙara tuni kar wani yace banda mutunci daga wannan satin zuwa wani satin duk wanda bai biya ba, zai iya jin tsit kar kaga shiru ba update mutum yace baiga update ba zan ringa turawa iya waɗanda suka biya, idan ka biya sai intura maka sauran, saboda bana so littafi yazo ƙarshe wasu suƙi biya_
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

*_🅿️26_*

_______zaune suke acikin falo, Papa da Maama,Dadda da gwaggo, Abu da Ummy sai Meer da Ameesha, gaba É—ayan su sun hallara aciki sakamakon umarnin Papa da ya tara su, guri É—aga dan yin magana,

Papa ne tayi gyaran murya tare da buɗe tare da buɗe musu taron da addu'a sannan ya ɗora da cewa "Alahamdulillah basai na ƙara maimaita abun da yafaru ba, abun da ya faru ya riga ya faru, Allah ya ƙara kiyaye gaba, yanzu dai angama da wannan matsalar haran mu na gaba kuma shine mu cigaba da addu'a Allah ya bayyana mana wannan yaron babana yanzu shi kaɗai ne tunanin mu, to amma kafin nan ina so muyi shawara a junan mu wa kuka fi ganin ya dace a ɗora akan karagar mulkin nan dan barin ta haka nan ba daidai bane dole asamu wani ya hau yafara gudanar da aiki dan dawo da ita kamar da, zamanin da yadawo tunda komai ya lafa kafin bayan raina ina so inga anayin mulki kamar yanda muka gudanar da mulki ni da mahaifina ada tsawon shekaru masu yawa komai ya canza amma yanzu ina fatan komai yazo ƙarshe daga nan har bayan raina, in Allah ya yarda nasan bazan taɓa kukan rashin magaji ba......,

ÆŠan dakatawa yayi kaÉ—an yana kallon kowannen su, sannan yace "to ina sauraron ku maiye ra'ayoyin ku akai wa yafi da cewa da hawa kan karagar mulkin nan tsakanin kai da É—anka yayi maganar yana kallon Abu,

Tun kan Abu yayi magana Meer yayi saurin cewa Papa wane ni a sarki gaskiya karma ayi wannan tunanin dan sarauta bata ra'ayina hasalima na tsane ta dan haka bazan taɓa zama sarki ba, gara a bawa Abu dai,

Ɗan murmushi Maama tayi sannan tace "nima dai kai na zaɓa amma naji tun kan aje ko ina ka karaya da wuri, to banda abun ka duk tsanar sa kayiwa sarauta tunda ka zama ɗan cikin ta ai ba kama cewa a bawa Abu to idan ya sauka fa saiwa kaga sai kai tunda yana hawama na daɗewa zai sauka kaga kwa dole kaine next ko kuwa?

Haɗe rai Meer yayi sannan yace "idan ya sauka ai ba dole sai ni ba nasan kafin loƙacin anga ƙanin sa sai a bashi tunda shima ɗa ne,

Gwaggo tace duk goce gocen kadai ai sai ya dawo wajen ka tunda indai da rai da lafiya su ai duk sun girma a ƙa'idama babu wanda zaiyi mulki acikin su saidai kai kaine saurayi kamar yanda ake ɗora sarki tare da auren sa ake ɗorawa ranar ɗaurin auren sa ranar da za anaɗaka sarki haka mukeyi kuma kaima haka zamuyi maka, sai ka shirya,

Wani mugun kallo Meer ya watsa mata jin abun da tace wai za ayi masa aure shi za ayiwa aure hmmm da basu kuma ba kuwa dan sai kowa yayi da nasani, bayan baya son sarautar kuma hadda yi masa auren dole,

"Kalle ni da kyau sarauta ba fashi haka kuma aure ma ba fashi ko ka kawo mana matar aure ko kuma mu aura maka,

"Uhm Gwaggo aikam saidai a aura masa É—in dan wanna da kike gani baya kula ko wacce macen hasalima duk wacce ta nuna tana sonsa sai ya kamata da duka kamar Allah ya aiko sa,

Gwaggo tace "to kuwa saidai ya kasheta idan ankai masa ita É—akin sa, amma ba fashi gwanda ma ya shirya,

Papa yayi Æ´ar dariya shima yace "a'a ba dole, nifa shawara na nema a yanke shawara, amma kunzo kun saka sa agaba, ina ruwan ku tunda baya so ku rabu dashi, yanzu daga yau zuwa wani satin zamu fara shirye shiryen É—ora Abu akan karagar mulki shikenan dai ko, mun gama magana,

Aure kuma loƙaci ne ku barsa duk loƙacin da yasamu matar aure sai yayi auren sa, kar wanda yaƙara takura masa,

Gwaggo zata yi magana, Papa yace "gwaggo dan Allah abar maganar haka, mayita wani loƙacin yanzu dai angama da wannan maganar zamu ɗora Abun Meer akan kujera tunda Meer baya so ko,

Daga nan Papa ya mayar da duban sa kan ko wannen su, yace akwai mai magana amma banda maganar É—ora Meer akai, dan naga wani ya haÉ—e rai to bani son jin komai daga garesa, ya faÉ—a yana saton kallon Abu da ya haÉ—e rai yana son yin magana amma Papa yayi saurin dakatar da shi,

Maama tace "to duk abun da kace hakan ma yayi nasan dai ƙarahen alawa ƙasa mutum ko yanaso ko baya so dole ya shanye ta,

Nan dai kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa, Papa yana ce akan dole Abu ne zai hau kan mulki, haka suka rabu dashi kowa yayi na'am da hakan,

Taro na shirin tashi har zasu rufe da addu'a Ameesha tayi saurin cewa "Papa ina da magana,

"muna sauraronki, cewar Papa,

Papa daman maganar karatu nane ina son mu koma makaranta,

Papa yace "ina sane da wannan abubuwane sukayi yawa amma yanzu komai alahamdulillah, gobe Friday sai kuje da yayan ku ki zaɓi wacce kike so sai aje ayi magana on Monday sai kinfara zuwa, ba wani ɓata loƙaci, bayan nan kuma sai me kike buƙata,

"Papa ni basai ma antafi nemo wata ba kawai asakamu makarantar su Amra nida ƙawata Azeema,

"Tom shikenan ba damuwa sai ki gaya mata ta shirya zuwa Monday zaku fara zuwa, Amma a wane class kuke,

"S.S 2 muke amma muna so mutafi S.S 3 saboda yanzu ƴan mate ɗin mu ma sunje S.S 3 saboda mu mun daɗe bamu je ba loƙacin da za ayi jarrabawa muka daina zuwa,

"To gaggawar mai kuke yi kuƙara maimaita wa mana, cewar Maama ta faɗa cike da tsokana,

Papa yace "a'a saboda dawowa baya, ai gwanda suyi gaba ko,

Ameesha ta kalli Maama, tace "Maama ni da nake soma mu wuce University amma kike maida mu baya,

Maama tace "nima da wasa nake,

Papa yace "nima da shawarar da nake ƙoƙarin yankewa kenan tunda su Amra ma ai jarrabawa zasuyi wannan watan da sai abiya muku gaba ɗaya kawai kuyi sai anema muku extra lesson kafin jarrabawar ta fito idan kunyi ƙoƙari kunce sai ku wuce tare idan kuma kuntsaya wasa zakuga wasa,

"Eh wallahi Papa hakan ma yayi gaskiya naji daɗi wallahi in sha Allah zamuyi ƙoƙari tana maganar harda su tashi tsaye saboda tsabar murna da jin daɗi...,

Gaba ɗayan su sun goyi bayan yin hakan, tunda daman zuwa yanzu yaci ace tagama secondary amma idan aka tsaya sai tace gaba, zata ɓata loƙaci gwanda kawai indai tana da ƙoƙari tayi gaba,

Papa ya kalli Meer yace to kai kuma fa baka da abun cewa,

"Eh banda shi,

"To masha Allah yanzu a rufe mana taro da addu'a kafin kuma musake zama,

daga nan suka rufe taro da addu'a inda kowa ya tashi yakama gaban sa, Dadda ma ta koma É—aki daman idan suna abun su bata saka musu baki, saboda ba hurumin tabane......,

Ameesha murna akai tayi harda arar wayar Dadda ta kira Azeema dan ta sanar mata amma kuma tana ta kira bata É—auka ba, fita tayi ta tafi wajen su Amra dan ta sanar dasu....,

**********************

______Azeema,

"Tunda taji maganganun sa kuma ya kashe wayar ta shiga tunani maganganun sa to mai yake nufi da hakan wata zuciyar tace mata to kodai sonta yake wata zuciyar kuma tace idan sonta yake ai zai gaya mata, banda kyara da mugunta babu abun da yake mata amma kuma maiyasa zaiji haushi dan ta kula wani,

Ji tayi gaba ɗaya zuciyar ta wani iri duk sai taji ta kasa sukuni gashi sai so take ta ƙara kiran sa amma takasa, ta tashi tsaye takasa zaune takasa tsaye abun sai yawo yake mata akai ta rasa ta yanda zata fassara abun,

Koda mama ta kirata da ƙyar ta iya saita nutsuwar ta taje, suna aiki amma gaba ɗaya nutsuwar ta bata jikin ta kuma har saida mama ta fahimci hakan ta tambaye ta, sai tace mata ba komai,

Hakadai maama ta rabu da ita suka ci gaba da aikin su suna gamawa kuwa ta koma É—aki taci gaba da tunane tunane ta,

Wayar tace tayi ringing da sauri taje hartana tuntuɓe wajen ɗauko wayar saidai tana dubawa taga akasin wanda take so tagani, Hamza ne yake kiran ta amma hakannan taji bazata iya ɗagawa ba, tana kallon kiran har ya katse yana katsewa ta jefar da wayar amma sai wani yaƙara shigowa share shi tayi tana ji har yayi sau uku ana huɗun dai ta daure ta ɗauko wayar da niyar kashewa sai taga akasin number ba number Hamza ba,

Hannun ta ne ya shiga yin karkarwa wayar har saida ta suɓuce ta faɗi ƙasa tayi saurin binta ta ɗauko ta, tare da amsawa ta sakata akunne tana sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tana rufe idanun ta,

jitayi yace "kifito ina ƙofar gidan ku,

Jitayi daram daram gaban ta ya faɗi hakan ya hanata basa amsa har ya kashe wayar, sauke wayar tayi ta ɗauki hijabi ta saka, tare da fitowa waje tana fitowa ta leƙa tagaya mama zata karɓo abu awaje sannan ta fita,
Chapter 45 · 0% Book details