← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 106

Sashe 96

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karasa maganar, idanuwanta sun cicciko tab da walla, Jikin Angel duk yai sanyi, zuciyarta ta karaya. Cikin murya tamkar tame Yin ra a, dr laura taci gaba da cewa"Abu aya da ban fa a maku ba, dama na yanke shawarar Sai mun ke6e dake in sanar da ke, saboda Na yaba da hankalin ki da kuma kaifin basirarki da wayon ki,' Angel ta natsu tana sauraronta. "Matar da sojoji suka dam a amanarku a hannunta, Mistress ce," kai tsaye sunan Ya daki dodon kunnan Angel, cikin rashin fahimtar ma'anar hakan ta maimaita kalmar mistress. Jinjina kai Dr Laura Tayi"tantiriyar ar bariki ce mai zaman kanta, shaidaniyace a fagen iya karuwanci, ta shahara sosai, babu wanda baisanta ba, tayi aurin suna a America, maca ce mai ha arin gaske, Namiji baya Iya ganinta Ya kawar da idonshi, saboda kyawun surar dake gareta, Nayi arin Fahimtar da sojojin Akan illar dam a amanarku a hannunta amma sun i su amince min Angel, ni nasan da wuya ta Iya baku kulawar daya ce, in ma bata gur6ata maku rayuwarku ba, Musamman an uwanki maza........" Hankalin Angel Ba aramin tashi yai ba, duk da Sanyin A.c na akin zufa ce ke tsastsafo mata saman goshinta, idanuwanta azazzare take kallon fuskar dr Laura dake kora mata jawabi. "Ni damuwata depression din dake damunku, da kuma an uwanku mai fama da ciwon zuciya, idan har aka cigaba da untata maku zaku Iya rasa rayukanku, shiyasa banso suka dam a amanarku a hannun karuwa ba, donni a sanina da matar masifaffiyace tana da girman kai, bata ta6a yin aure ba, kuma bata san ciwon haihuwa ba, abunda ta sani shine wacewa matan aure mazajensu tayi fasi anci da su, matar ta zama tamkar annoba, ta raba aure da dama saboda hatsabibancinta" dakatawa tayi da yin jawabin idonta akan Angel, tsantsar tashin hankali take gani acikin wayar idonta, Jikin Ta aura Yai la'asar, An gudu ba'a tsira ba. Muryarta Na rawa ta furta"Aunty, amma meyasa suka dam a amanar mu a hannunta? Babu wata ne sai ita? Kuma ai mu bamu bu atar wadda zata kula damu, idan ma akwai abunda zamu bu ata bai wuce jami'an da su bamu tsaro ba...." bata arasa maganar ba dr laura ta katse ta da cewa"dalilin dayasa suka dam a amanarku a hannun ummin america, kamar yarda major ya sanar dani, matar tamkar ma'aikaciyarsu take, ta saba yi masu aiki wurin jan hankalin tantiran an ta'addan da suka gagara a asa, suna yin amfani da ummi wurin ana masu tarkon da zasu kamasu, kuma suna cin nasara, Masoyiya Angel ban fa a maki hakan donna tada maki hankali ba face don ki dage damtse wurin Yin ya i da ita akan an uwanki, kada ki kuskura ki bari ta ke6e da aya daga cikin Samarin dake a jikinku, Idan ba haka ba za'a Iya samun matsala, saboda bata da linzami matar, duk da A yanzu ina kyautata mata zo, tun da har sojojin suka aminta da ita suka dam a mata amanar ku, hakan na nufin sun san zata Iya ne, Bayan haka sun ulla yarjejeniya da ita akan baku kula ta musamman da kuma gujewa duk wani abu da zai 6ata maku rai, kamar yarda na gani dai dai da tsawa tayi maku babban laifine, don haka Zan tura maki sharuddan da sojojin suka gindaya mata akanku ta whatsapp, saboda inaso kiyi amfani da su wurin ja mata kunne idan ta sa6a maku," jinjina kai Angel tayi alamar toh ta ara da cewa "bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya, Allah ne ka ai zai Iya biyanki, saboda kyautatawar da kukayi mana, gashi kun auke mu tamkar an ku, " Shafa sumar kanta dr Laura tayi"Kada ki damu yana daga cikin aikin mu!, Yanzu ki shiga kiyi wanka, Mintuna alilan suka rage maku," amsa mata tayi da toh, Bayan fitar dr Laura, Angel ta nufi Jakar Kayan, zuciyarta a hautsine ta girgiza da jin wacece matar da aka dam a ma amanarsu, ita babban abunda ta ke jima fargaba garkuwarsu, tunawa da lokacin da aka kawo masu unaiza a kurkuku, yarinyar ta ru e shi da big boobs dinta, balle kuma matar da taji ance tana tafiya da imanin namiji saboda dirin jikinta, tashin hankalin da ba'a sanya mashi date. ( Har ta fara Imagining abun da zai faru, a gidan da zasu zaune atare da ita, tayi tunanin sun samu sau ine komawarsu Nigeria ashe akwai sauran rina akaba. A hankali ta ruko hannun jakar Kayan, ta zaro kayan dake acikinta, wata ha iyar A-line gown ce launin red colour mai round neck ar ubansu awurin ha uwa, Rigar tayi mata kyau a ido, sai faman jujjuyata take yi, aranta tana ayyana yau wata rana zata sanya kaya na mutunci wanda ba uniform din prison ba, wannan abun farin ciki ne agare ta. Bayan ta gama kallon rigar, ta aurata saman mattress, ta zaro kwalin takalman dake a cikin jakar tare da kwalin sabuwar wayar da dr laura ta siya mata, irar iphone 15 pro, Takalman kuma Ankle strap ne masu tsini launin black, hada face mask da mayafi aka basu wanda bakowa bane Ya tsara hakan face chief na Isod, Lokacin da dr laura ta bukaci zata siya masu kaya Sai da aka nemi izininshi, yace ya amince bisa shara in idan zasu sanya kayan a ha a masu da Ni ab ko face mask da zasu rufe fuskokinsu, a alla ta shafe tsawon mintuna biyar tana kallon kayan, bakomai yafi burgeta ba face wayar da aka bata kyauta, tunawa da lokaci yasa tayi saurin nufar toilet ta shige ciki, shaf shaf tayi wanka kafin fitowarta, Nurse jessica ta shigo akin hannunta ru e da gift kit aramin akwati na kayan shafa, ta aura shi gefen gadon Angel, ta zauna saman kujera tana Jiran fiowarta, bayan ta fito daga wankan, suka gaisa da nurse din cikin girmamawa, daga bisani tayi mata bayani game da care kit din data kawo mata donta gyara jikinta, godiya Angel tayi mata bayan ta auki kayan shafar da rigar ta juya ta nufi toilet dasu saboda jin kunyar kada aganta tana sanya kaya, murmushi nurse jessica tayi yayin da take binta da kallo. Bayan ta shafe ko'ina na jikinta da body oil mai tsadar gaske, skin dinta har glowing take yi, rigar tayi bala'en yi mata kyau, duk da bata da jiki tana da tsawo, white in red abun ba'a magana, lokacin da ta fito daga cikin toilet in, ita kanta nurse din sai santin kyan Angel take Yi, daga saman rigar ta tsuke daga asanta bazace daga ta jujjuya rigar take bubbu ewa kamar ana hura mata iska, bayan ta kammala shiryawa nurse ta feshe mata jikinta da turaren desired destiny, fragrance din turaren mai da in sha a a hanci. Face mask din da ta sanya black colour ne launin takalmanta, har saman karan hancinta mask din ya haura, Gray eyes dinta ne ka ai suka Bayyana. aura Mayafin rigar tayi asaman kanta tayi rolling dinsa, gyalen yana da tsayi ba laifi, Har saman gwiwar hannayenta yakai mata, shima launin takalmanta ne. "Kin yi kyau masoyiya Angel, sai ki ka yi mini kama da Cinderella saboda rashin ibarki," ayataccen murmushine kwance saman fuskarta, "Na lura kin osa ki bar asar nan, Ni kuma gashi bana son ki tafi, saboda na saba da ke masoyiya Angel," cikin sanyin murya Nurse jessy tayi maganar tana duban fuskarta. "Dr. laura ta bani kyautar waya, kuma ta fa a min akwai phone numbers din ku aciki, zan dinga kiranku akai akai muna gaisawa saboda ni kaina bana son mu rabu don ya zamar mana dole ne mu tafi" Sai da tayi maganar Nurse jessica ta wurga eye balls dinta kan kwalin wayar, zaro ido ta anyi ha i da cewa"wow, gaskiya dr. Laura tana Ji da ke shalelenta, wannan waya haka mai kyau da tsada, Ina taya ki murna masoyiya Angel, Kuma naji dadi da ta baki wayar, Kinga zamu dinga kiran juna muna gaisawa, harma muyi video call" fuskarta dauke da matsanancin farin ciki, ta nufi gefen gadon ta auki kwalin wayar a hannunta, tana are mashi kallo, Angel dai sai murmushi take saki, bakinta ya i rufuwa kamar ta fasa ihu Haka take ji tsabar murnar yau zasu Bar america zuwa asarta ta gado. "Yakamata mu tafi masoyiya Angel, an uwanki suna Jiranki a waje" cike da agara Angel ta amsa mata da toh, shaf shaf ta zura takalman a afarta masha Allah, wankan Angel yabi jiki. A hannu ta ru e wayar bayan ta curo ta daga kwalin, atare suka fito daga akin. Tun kafin ta ago da idonta, Muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta"Genie gamu nan ki dube mu da kyau, mun yi kyau" Da sauri ta wurga idonta kansu, masha Allah har saida gabanta Ya fa i tsabar ki ima da ganin Kyawun da suka Yi acikin sabbin kayansu, jemimah da azeeza launin gown dinsu Royal blue ne, hannah da parveen launin punch pink, Ita kuma Batul launi ayane dana Angel, red colour, kowaccensu akwai Face mask a fuskarta, Anyi masu rolling Veil a saman kawunansu, takalman kafarsu flat ne ba kalar nata ba, aya bayan aya take binsu da kallon mamakin Kyawun da suka Yi, mutun aya ne ke babu a cikinsu, Mazan su hu une, kowannansu ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ta kece raini wato shigar hadaddun Slim fit suit, sun manna mask a fuskokinsu, kwantacciyar sumar kawunansu ta kwanta luf, afafuwansu na sanye cikin tsadaddun takalman fata, ta ko'ina amshin turarensu ne ya kara e ward din da suke. Ganin tayi tsaye tana kallonsu bata motsa ba, yasa kowan nan su sanya hannu a lokaci aya suka Zame mask din dake a saman fuskokin su, sai faman washe mata baki suke yi, wani irin farin ciki ne Mara misaltuwa ya kamata, tun daga kan yadda suke sha ar iskar an ci zaka tabbatar da kwanciyar hankali da natsuwa atattare da su, su kansu sun yaba da kyawunsu, sai faman shafa kayan jikinsu suke Kamar zasu lashesu. Jemimah ce ta ru o hannun Azeeza suka watso da gudu zuwa gabanta, Atare suka fada saman jikinta, Hugging dinta su ka yi suna ti ar
Chapter 96 · 0% Book details