← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 106

Sashe 78

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_The Prisoners E20 *Daga al alamin Boss Bature* Hankalinta a matu ar tashe take kallon fuskarshi, Numfashinta na hauhawa zuciyarta na bugawa da sauti mai arfin gaske tamkar zata tsaga irjinta, tsabar tsoratar da ta yi, Nurse Jessica da ke a zaune ta rasa gane meke faruwa ne? taga dai tun da Angel ta yi mashi rumfa ta i motsawa, kamar an daskarar da ita, idanuwanta ba su hango mata hannun Danish da ya dam i Qugun Angel da shi, sakamakon Sumar Kanta da Hijabin jikinta sun lullu6e shi. "masoyiya Angel, Ke nake Jira, kusan arfe goma na dare, Yakamata Muje ki kwanta ki kwanta ki huta" Cikin Kulawa ta yi mata maganar Tana le en fuskarta sai dai bata samu damar ganinta ba, saboda wuyan Hijabinta Ya zame tuntuni sumar kanta ta zazzago gefe da gefen fuskarta, ta rufe su. Yun urin kubcewa tayi daga ru on nashi sai dai ko gizau wannan bai yi ba, kuma bai motsa ba, Ya matseta A jikinshi, tamkar an aureta da igiyoyi, duk da sanyin A.c na room din hakan bai hana ta zubda gumi ba, zufar dake wanko fuskarta kaitsaye take sauka saman fatar face nasa, idanuwanta azazzare, yayin da acan cikin zuciyarta ta ke ta ambaton"INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN"! Ba autawa. Muyar Nurse Jessica ce ta ara fargar da ita"Lafiya kuwa Angel? Ya akai naji Kinyi shiru? Ko kinyi bacci ne a jikin shi" ta are maganar tare da yun urawa ta mi e daga saman chair in ta nufi gaban gadon ta tsaya tana ci gaba da yi mata magana, tsabar yadda la66anta ke yin kerma ta kasa bu e baki ta fa a mata Halin da take a ciki. Mi a Hannu nurse jessica ta yi da niyar ta ago da Angel, saboda ta yi tsammanin bacci ne Yai awon gaba da ita, Sai dai Kafin ta ru o ta, Angel Ta yi arin Yin magana Muryarta A hargitsa ba natsuwa ta furta" an Uwana Ya farka! Shine Ya ru e Ni" Mamaki Ne Yasa Nurse jessica Zaro Ido ha i da bu e Baki, Ta Furta" Are u serious Ya farka? "Ya farka, but he didn't open his eyes. He held me so tightly that I couldn't separate myself from him" cikin shesshe ar Kuka Angel ta furta maganar. Jin haka Yasa Nurse jessica fa in"Bari Na taimaka maki ki mi Hannu Biyu ta sanya ta ru e Angel ta soma kiciniyar 6an6arota daga Jikin Danish da Iya arfin ta na arshe sai dai takasa ta6uka komai, Mugun ru o Yai mata, Hatta dogayen nails insa sun yi mata shatu saman bayanta, Lamarin ya aurewa Nurse Jessica kai, ganin ta sanya Iya arfinta na arshe Amma abanza, hakan ba aramin ru ar da ita yai ba, Muryarta na rawa ta furta"Bari naje na kira doctor" Da sauri ta fuce daga Cikin akin hada an gudunta A lokacin da bata Yi tsammani ba, Sexy voice insa ta ratsa kunnuwanta muryar da ta da e tana mararin Jinta "My Angel" Iya abunda ya furta mata kenan. nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ya ambaci sunanta, hakan na nufin Yana acikin Hayyacinsa, ura ma fuskarshi ido tayi ganin yana mutsu mutsun bu e idanuwanshi, sannu A hankali yake arin ware su, sunyi mashi nauyi saboda baccin da yai na tsawon kwanaki, Ta yi matu agara da son Yin tozali da kyawawan Reddish-brown eyes insa, ka an Ya bu e su bai arasa ware su ba, sun ciza launinsu, hakan ba aramin kyau suka ara ma shi ba, Tsabar farin ciki batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya, tana ha awa da dariyar farin Ciki, ya natsu yana kallonta da wata irin kasala a jikinshi, sam bai san a ina suke ba Iya fuskarta Yake Iya gani. Cikin shesshe ar kuka ha i da shagwa6a take fa in"Nayi missing inka My man, sai yau zaka farka? Kabarmu da kewarka da fargabar a wani hali zaka tashi, sannan kuma ka tsoratar dani sosai...." lumshe idanuwanshi ya anyi tare da ware su saman fuskarta, Hawayenta sai ji a masa face dinshi suke Yi, har cikin bakinsa, hakan bai dame shi ba, tamkar ya samu ruwan sha, haka ya ke yin swallowing dinsu. Kallon da ya ke yi mata kallo ne dake nuni da tsantsar aunarta da kewarta da yayi, hucin numfashinsu sai gaurayewa yake yi dana juna, hakan bai sha masu kai ba. Idanuwanta sharkaf da hawaye sun rune jawur taci gaba da cewa"dan Allah ka fa amin ba abunda ke damunka? Naga kanata kallona ka i kula ni" ta are maganar still da shagwa6a, yamutsa fuskarshi ya anyi ha i da motsa tausasan la66ansa calmly ya furta "ke ce damuwata, kinsan bana son zubar hawayenki, ki daina yi min ku ka or else I'll go back to sleep yai maganar yana arin lumshe idanuwanshi da zolaya yai mata hakan aiko da sauri ta shanye kukanta, tana fa in"na daina My man, kaine ka i kwantar min da hankali na" ba zato ba tsammani taji ya manna mata peck saman fore head dinta, farin ciki duk ya cikata. Muyarta har sha ewa ta ke yi saboda kukan da tasha"ka sake ni, Ka matse ni" tayi maganar tana arin kubcewa daga ru on da yai mata, so ta ke yi ta nuna mashi sabon wurin da suke acikin shi, ameta Ya ara yi yana fa "Ki jira, zan sake ki, ina samun natsuwa atare da ke" ayataccen murmushi ta saki, ta an dakata suna kallon cikin idon junansu, lokaci aya taga Ya ha e face dinsa. "Lafiya"? Tai tambayar tana cigaba da kallon shi "Namanta, ban sama maku abincin da zaku ci ba, Na bar ku da Yunwa" Murmushin gefen fuska ta sakar mashi"Ka kwantar da hankalin ka, Muna cin Lafiyayyan abinci har sai mun ture, shiyasa nace ka sake ni inason nuna maka wani abu" slowly ya zame hannunsa daga ru on Da yai Mata, Light bulb akin Ya haske mashi ido, saukowa tayi daga saman gadon ta fuskanci gabas Ta du a tayi sujjada tana godewa Allah daya farkar mata dashi cikin oshin Lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba. Alhamdulillahi Ala kulli Halin. Ya yi matu ar Yin mamakin ganin room in da ya ke aciki, a kasalance ya yun ura Ya mi e zaune yana arewa ko'ina Kallo, tunani ya shiga yi Ina ne nan? Waye ya kawo su? Fuskarshi da alamun ru ani ya Tura yatsun hannunshi cikin yalwatacciyar sumar kanshi yaci gaba da caku ata tamkar yana sosata, saukowa ya yi da ga saman gadon. Jikinshi yayi mashi nauyi da yar yake taka afarshi, yayin da yake arewa akin Kallo, Angel tana a du e tun da tayi sujjada bata ago ba, addu'o'i take tayi masu. Yana arin bu e baki da niyar ya yi mata magana, Sai ga doctors da nurses sun shigo akin da saurin su, Kusan atare su ka ci uban burki suna kallon kallon a tsakanin su da shi, Mutumin da suka da e suna mararin ganin Ya farka, sai yau Allah ya nufa zai tashi, Sun yi matu ar girgiza da ganin Shi a tsaye kan afafun shi, kyan fasalin shi Ya yi masu warjini. Da hannu Yai masu Alamar su wanene su? Sai an kame kame suke Yi An rasa me Iya bu e Baki Yayi mashi magana. Juyawa yai da sauri Yaje gaban Angel da ta yi sujjada, Da hannu aya ya ru o damtsen ta, Ya ago da ita tsaye kamar wata ar baby, nuna mata likitocin Ya yi da hannun shi "Who are they, and where are we?" da yar ta samu natsuwar Fayyace mashi komai tun daga kan Yadda aka tsunto su a daji aka zo da su asibitin kamar yadda Gabriel Ya sanar da ita. Bayan ta gama kora mashi jawabi ta kalli fuskokin likitocin tace "ku ta ya ni murna an uwan mu Danish Ya farka" murmushi kowan nan su Ya saki Nurses din dake a cikinsu kamar sun samu tv haka suke Binshi da mayataccen kallo, ba mazan ba ba matan ba. "Muna ta ya ki Murna masoyiya Angel, munga brother inki Ya farka cikin koshin Lafiya" nurse jessica ce Tayi maganar Da yar wani dr ya iya bu e baki yace"Danish Fatan Ka tashi Lafiya, tsawon lokaci muna jiran ranar da zaka bu e idanuwanka, Sai yau muka samu damar ganin ka, Mun ji da i sosai" yai maganar tare da mi a mashi hannu don su gaisa, Man in fa bai yarda da su ba, dama yana da wuyar sha'ani ga iwuya kamar aramin Yaro. "Danish Ka mi a mashi hannu ku gaisa" Angel ce tayi mashi magana, goya hannayenshi yai saman broad chest dinsa, Alamar ba zai mi a mashi hannun ba" murmusi ya e ta an saki"ku yi ha uri, Danish baisan ku ba, Har yanzu baccin bai sake shi ba, nasan kafin zuwa gobe zai Warware' Nurse rebecca tace "badamuwa, Dama mu fatan mu Ya farka da ranshi da lafiyarshi, Hakan ma ya wadatar" Dr. Anthony Yace"Calm down, Danish. No one will bother you. We are doctors, and we have the right to check your health until you feel better." still bai tanka masu ba. Dr harry yace"ni dama tun kafin Ya farfa o raina Ya bani zai yi wuyar sha'ani, sai gashi maganata ta tabbata, mutane masu irin Kyanshi bakowa suke kulawa ba" da zolaya yai maganar, Ya ara da cewa "mu dai yakamata asaki jiki damu tunda malaman lafiya ne, muna so ka bamu dama mu ara bincika Lafiyarka" tun da suka fara Magana bai tanka masu ba sai kallo da yake binsu dashi kamar yaga wasu halittu daba na mutane ba. "Ko akwai Inda ke yi maka ciwo yanzu"? Dr anthony ne yai mashi maganar, Angel sai arin ingiza hannunshi take Yi don yayi masu magana amma Ya iya, Nurse jessica tace"ga dukkam alamu rowar muryarsa yake yi mana, Ni inaga Mu yale shi zuwa gobe nasan zai warware kuma zai saki jiki da mu" Kamar za su yi hauka wurin yi mashi magiya don yayi masu magana yayi shiru abunshi, har so sukayi su bincika lafiyarshi amma Ya hana, duk wanda yai gigin matsowa kusa dashi, zazzare masu ido yake
Chapter 78 · 0% Book details