Sashe 2
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta. "Shikenan Yanzu ki fa a mana Taya za'ae mu ga an uwan mu Danish? Idan ma ta kama Ni zan bi ki mu shiga prison ne don mu nemo shi" Gabriel ne yai maganar da warin gwiwarsa, Har yanzu yana nan da rashin tsoronshi. Girgiza kai Angel tayi"wannan aikina ne, Ni ka aice zan Iya dawo da Danish Cikin mu, In sha Allah, " "But how could you do that? Bayan babu wata ofa da zaki Iya shiga prison"? Har ta bu e baki da niyar Ta amsa Ma Naufal tambayar da yai mata, kwatsam! ba zato ba tsammani Kunnuwanta su ka jiyo mata motsin bu opar akin su, hakan yasa tai saurin Katse maganarta, Idanuwanta azazzare Take kallon su. "Kamar bu ofar akin Mu ake yi? Mun shiga uku, Asirin mu zai tonu, wlh mu gudu daga Cikin toilet in nan," Parveen ce tai maganar, hankalinsu idan yai dubu toh ya tashi, Gaba aya duk sun bi sun ru e, a sukwane Angel ta juya da gudu ta nufi ofar toilet ta bu e ta, Fucewar ta keda wuya suma suka bi bayanta, garin gudu har suna bangaje juna, Adai dai lokacin da suka fa o tsakiyar akin, kowannansu ya tsaya da tafiya, Idanuwansu azazzare su ke bin benan da kallo, sai faman haki suke yi babu mai sauran kwanciyar hankali acikin su, babban abunda su ke jima fargaba kada ace Tsohuwa zafreen ce, Ilai ko hasashen su Ya zama gaskiya, ofar na arasa bu ewa kunnuwansu suka soma jiyo masu takun takalmanta Har wani sauti su ke badawa was was! Jikinsu Ya hau kakarwa zufa ta dinga tsastsafo masu ta ko'ina a jikin su. Cikin muryar ra a Deeja tace"Mun shiga uku Angel mun manta bamu maida tukunyar fulawar nan ba! Yanzu idan ta shiga toilet in ya zamu yi? asa asa da murya Angel ta ce"In sha Allah ma ba zata shiga ba, Idan ma tai yun urin yin hakan zan dakatar da ita," ita kanta da ta ke yin maganar a tsoroce ta ke furtata, arfin halin ne kawai. Ahankali ta ke tunkaro in da suke atsaye Cikin shigarta ta jajayen kaya, Yau babu mask a kan fuskarta, Daga bayanta Giants ne Guda Biyu masu irar Samudawa, ko da ta araso dab dasu saita dakata da yin tafiyar A tsanake ta ke binsu da kallo aya bayan aya, Saboda tsabar ru u da kama kai, Jikin Angel na 6ari ta russinar da kanta asa muryarta babu natsuwa ta furta"Ina kwana" Tun da tsohuwa zafreen ta kafe ta da ido sam ta kasa motsawa, Lamarin ne ya aure mata kai, Yadda Angel ta du a mata wurin gaishe da ita..... Da sauri su Haris suka russinar da kansu tare da gaishe da ita Cikin girmamawa. Babu wanda ta amsamawa a cikinsu, Tsawon mintuna biyar kafin ta an yi gyaran murya tare da basu Umarnin su ago da kawunansu, bayan sun ago ta tsare fuskar angel da blue eyes inta, Suspicious looking ta ke binta dashi Hatta tsigar jikin Angel sai da ta tashi hai am, Sam takasa yarda su ha a ido da tsohuwa zafreen, ta dage tana ta wasa da yatsun hannunta, ta har e su acikin na juna, Su ta urawa ido. Su Deeja duk sun sha jinin jikin su, ganin irin kallon da tsohuwa zafreen ke bin Angel da shi, Kuskuren da Angel ta tafka shine gaishe da zafreen da ta yi, Mace Dattijuwa irin zafreen wadda taga jiya taga yau, Taya zata Iya yi mata wayau? Yarinyar da bata ta6a gaishe da ita ba, sai yau Hakan ya ara sanya mata zargin wani abu na faruwa a akin nasu, A hankali takawar da idanuwanta daga kan fuskar Angel ta soma bin fuskokin su Batul da kallo, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, sam babu alamun gaskiya atattare dasu, duk wani motsinsu akan idonta. Ba zato ba tsammani suka ga ta tuntsire da dariya mai sautin gaske hankalinsu ya ara ugunzuma, a firgice su ke bin ta da kallo, Lokaci aya ta dakata dayin dariyar ta aure fuskarta tamau babu annuri. "Meyasa ki ka yi gaggawar gaishe dani tun kafin in bu aci hakan? Kamar daga sama Angel taji ta jefa mata tambayar. Yawu ta ha iya kutt a ma oshinta, Idanuwanta na kallon asa azazzare ta soma magana Cikin rashin natsuwa "Nagane kuskure na, kuma Na yi danasanin rashin kunyar da na yi maki a kwanakin baya, inaso na gyara tsakanina dake ne saboda nasan ban kyauta ba.." tunkan ta kai arshen maganar tsohuwa zafreen ta soma sakin bazawarin murmushi, wanda silar hakan yasa ta kasa arasa zancen da ta kamo. "Saboda meyasa kike son gyara tsakanina da ke"? Ras taji gabanta ya fa i, Da yar ta tattara natsuwarta kafin ta ci gaba da magana"Mahafina bai koyar dani rashin kunya ba, Tunkafin rasuwar shi yana yawan yi mini nasiha akan girmama na gaba dani, amma saboda rashin jin magana irin nawa ban bi abinda yake koya mini ba nayi danasani........" Sosai ta fashe da kuka gaba aya idonsu Hibba akanta, Tsabar mamaki yasa suka saki bakunansu suna kallon Fuskarta, Ba aramar ar drama bace. Da bu ar bakin tsohuwa zafreen sai cewa tai"well done Unaisah! Dila sarkin wayau! Da ace ke ar film ce tabbas zaki iya cin gasar wadda tafi kowa Iya wasan kwaikwayo, Tun da nake ba ata6a rainin mini wayau irin na yau ba, aramar yarinyar da na yi jika da ita...." maganar tsohuwa zafreen ba aramin ara aga masu hankali ta yi ba, duk sun sha Jinin Jikin su. "Ku fa a min Me ku ke shiryawa ne" Shiru su ka yi irjinsu na bugawa , Mirmushin gefen fuska ta saki tare da cewa"Dama nasani ba za ku fa a mini ba, Idan naso zan iya yin anfani da sihirin da nake dashi wurin jin abunda zuciyarku ke sa a maku, Ko in sanya ku yi mini magana da kunan ku,' Yanayin yadda suka zazzare wayar idanuwansu tamkar zata fa asa, tsoro da firgici ne tsantsa akan fuskokin su. Ganin tana arin buga sandarta asa Yasa Angel tai saurin cewa"Zan fa a maki gaskiya, " tsayar da ido zafreen tayi akan fuskarta. "Tattaunawa mu ke yi akan yadda zamu ku6uta daga Cikin kurkukun nan saboda mun gaji da rayuwar kulle, Muna so mu ma mu yi rayuwar anci kamar yarda sauran mutane su ke Yi" yar ta kai arshen maganar tana mai ha iyar yawu, Su Batul duk suna sauraronsu babu wani mai natsuwa a cikin su. "Ban yarda da maganar ki ba, A iya sani na prisoners basu da hankalin Yin tunani mai kyau irin wannan balle har su baki ha in kai ku tattauna da junanku, Ke ce kika tsara komai Unaisah, saboda kina son karkatar da hankalina don In yarda da maganar ki, " Tun kan ta arasa maganar ta soma bin akin nasu da kallo, Kamar sakarkaru haka suka dinga binta da ido Cike da fargabatar karta fa a sashen toilet insu asiri Ya tonu, A hankali take tafiya tana arewa akin Kallo Kafin Ta Juyo a sukwane Ta tun kari sashen toilet in su, Tashin hankalin A matu ar tsorace suke kallon bayanta, Giants in dake atare da ita basu motsa ba, suna atsaye Kamar gumaka Su Angel Ido ya raina fata, Sai faman Cizon yatsa ta ke Yi, Ji take kamar ta watsa aguje tasha gaban zafreen. "Innalillahi Ya Allah ta makance kafin ta shiga, Ya Allah ka taimake mu! ya Allah ka hanata gani" Acikin zuciyoyinsu suke furta hakan, Suna ganin ta shige Ciki, Zufa ta soma wanke fuskokinsu, Azeeza tuni ta fara matse kwallo, sun san dole Taga abunda suke aiwatarwa, Idan kuwa harta gano zasu ani ku arsu ne, Kowa zaiji a jikin shi, Babban abunda yafi damun Angel garga in da Salsabeel ya yi mata akan su yi takatsantsan Yanzu idan asiri ya tonu gaba aya taja masu masifa da bala'e. Runtse idanuwanta ta yi sosai, hawaye ta ko'ina suka shiga wanke fuskarta, idanuwansu Deeja akanta, Tausayin kansu ne ya kama su, Har sun fara hasashen irin Azabtarwar da za'ayi masu kafin akashe su, Sai bin Juna su ke yi da ido babu mai magana saboda Giants in da ke tsaye akansu. Fitowa tsohuwa zafreen ta yi daga sashen toilet insu, Fuskarta auke da shu'umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa, girgiza mata kai su ka dinga yi ba tare da sun iya furta komai ba, Sun riga da sunsan taga ofar nan shikenan ta faru da ta are, Watan Cin ubansu ya tsaya, sun kirawa kansu mutuwa tunkafin lokacin su yayi. "Wallahi Allah!....' Azeeza ce ta yi su6ul da baka, da sauri Gabriel Ya toshe mata bakinta da hannun shi, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwansu, duk sun agara su ji wani hukunci zata yanke masu tun da ta gano plan insu. Walking magestically ta araso gabansu Tare da tsaida sandarta a asa, Daya bayan aya ta ke kallon su tsawon mintuna Uku kafin ta soma magana atsanake "Furennin da ku ka shufka sunyi kyau sosai, Wanene ke basu ruwa A cikin ku? Zaro ido su ka yi akan fuskarta Mamaki Ya kamasu, Aransu suka shiga ayyana cewa" ko dai bata ga ofar ba ne? Ko kuwa Allah ne yaji kokensu ya hanata ganin komai. "Kun yi shiru baku bani amsa ba"? Yawu Angel ta ha iya Muryarta Na rawa ta ce"am..um..ni..nice..Ni nake bata ruwa, tare da an uwana," Murmushi tsohuwa zafreen ta saki tare da cewa"Ku cigaba da bata ruwa inason furenni, Nan da wani lokaci zan auke tukunyar fulawar in mayar da ita akina..." tsabar zalama tunkan ta arasa maganar Angel tai wuff wurin cewa"idan ma kinaso Yanzu saina auko maki ita ki tafi da ita, ai mu mun fi son duk wani abu da zai faranta maki rai" kallonta tsohuwa zafreen ta yi da tsoffin idanuwanta"Kamar baki da gaskiya? Ina magana kina katse ni"! A kausashe tayi maganar. Sunnar dakai asa Angel tayi a tsananin ru e Batul ta aura da cewa"Ae tun lokacin da aka canza mana abinci zuwa ganye, Angel ta soma Fita hayyacinta, sam babu natsuwa atattare da ita, Hakanan zaki ga ta zauna tana sambatu ita ka ai" ta arasa maganar hada murmushinta, (Yara sun zama an wasan kwaikwayo)