← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 106

Sashe 24

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai arfi naji ..."Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi matu ar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu ba, ha a ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da yin firar, aya bayan aya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya ke....... *UNCLE ABDALLAH* alla yau wata aya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ara iba abunta. Ta natsu tana kallon portrait artist in dake zu unne agaban Drawing board Yana gudanar da aikinsa, daga asa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da hajiya adama ta mi a mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a shekarunta na yanzu don su samu sau in gane ta "Ranki shi da e, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu"? Me zanan ne yai mata tambayar. "I think 15 to 16 years," amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan shi, "Mijina ya fa a min cewa kai wararre ne a 6angaren zana mutane, so please don't disappoint me" murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta mata"In sha Allah" "Assalamu Alaikum"! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi, Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri ayane. Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara'a ya ago ya kalli Hajiya adama"mu shiga ciki ina son magana da ke" amsa mashi tai da toh, Yai gaba ta mi e tabi bayanshi, A cikin bedroom insu su ka tsaya suna fuskantar Juna "Tun azu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na wallafa raina akan son ganinshi, " "Duk yadda kika kaiga agara da son ganinshi ba ki kaini ba," "Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani a da zamu dinga kallo muna jin da i" fuskarta amarairaice tayi mashi maganar, girgiza mata kai Uncle Abdallah yai"idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta"? aure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci"Abdallah baka son farin cikina, Ni zan koma palour wurin mai zanan can" Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi, Har takusa kaiwa bakin ofa muryarshi ta katse mata hanzarinta"ba zan ta6a manta irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin bana son farin cikin ki"? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta "A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama, na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da anta ba, haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai" idanuwanta ne suka cuko tab da wallar farin ciki. Fasa fita ta yi daga Cikin akin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta saman irjinshi, Hannun shi Ya aura saman bayanta yana cigaba da gayamata da an kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta ago dakai Tana kallon shi "Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea, Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matu aunarta, kuma zatayi mamakin ganinta a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun ware a iya zane" tana magana Hannunta ru e da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta "Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu ari akayi maki shi fa" murmushi ta an saki"saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na auke shi," yace"mai zai hana ki bata sabon zanan da za'ayi ke sai ki ru e na koriyan? Girgiza kai ta yi alamar "a'a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da tsada, Farin cikinta kawai nakeso," yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata a asar korea, ba ta kawo komai aranta ba saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba. "Hajiya an kammala" daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su arasa shiga Ciki idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel jikin allon zanan nashi, Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana tajudden Hasken fatarne ka ai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta. "Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over" hajiya adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin zanan, Suffar Angel sak sai dai an ara mata girmanta, takai dai dai age inta na yanzu 15 to 16 years, Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke yabon aikinsa "Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru nayi maka al awarin zan ninka maka ku inka" fuskarta auke da murmushi tayi maganar tana kallon mai zanan, washe baki yai yana fa in"In sha Allah ranki ya da ar ki zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina ro on Allah yasa zanene ya zama silar ganinta" atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan saida suka ha a mashi sha tara na arzi *EVIL FOREST* *the Prisoners Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah ka ai yasan awanni da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya duhun dajin ya an washe, A hankali ta soma mutsun mutsun bu e idanuwanta a yayin da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai da yar ta ke iya bu e shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, ka an ta ke iya bu e shi tana kallon Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun addara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take arin walawa an uwanta kira aya bayan aya, duk tabi ta furgice. "Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne"? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da arfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya an ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya irjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta"My Angel" jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, ari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffa irjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, ka an ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na an rawa ta furta sunanshi"Da..Nish" fatanta Allah yasa ba mafarki bane. Dogayen yatsun hannun shi ya aura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta aura nata hannun saman nashi dake akan face inta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, ago da ita yai zuwa saman irjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri, "I can't explain how much I miss you. I'm sorry for what happened, it's all my fault. I'm sorry, Angel." Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shesshe ar kuka ta soma yi mashi magana"ba laifinka bane Danish, ka daina fa in hakan, ni abunda yafi damuna rashin an uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu al awarin da na aukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran an uwan mu da mu ka rasa" da yar ta arasa maganar, zafin jikin su duk ya umamasu, Yanayin weather in dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa. aura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi ka ai yasan ra in da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta ago da kanta daga saman irjinshi ta aura eye balls inta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke arewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, ' "Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun
Chapter 24 · 0% Book details