← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 106

Sashe 62

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_The Prisoners E17 *Daga al alamin Boss Bature* alla sun shafe kusan 30 minutes a akin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta a aki aya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su ara duba shi' jiki asanyaye suka mi e suna tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi. Bayan fitar su daga akin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi, ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a su ba da ko babu inda zasu je, a akinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah yar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba'a ha a mutun fiye da aya a aki, wata' il sai idan ya kama dole, sau in ma kowan nan su akwai nurse aya da ke kula da akin shi, duk wani abu da zasu bu ata zasu yi masu, hatta toilet suna raka mutun In ya bu aci hakan musamman gasu da basu san yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba. A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa. *Daular Alhaji Musa wadata* idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato Ha iyar Daular arzi i ce, Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura afarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ar ubansu, A alla security din dake tsaron Kafcecen Gate in shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada Masu irar sadaukan Ya i, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate in, yadda kasan da zallar goal aka era ginin saboda aukar idon gilassan ofofin da Windows, ko gidan shugaban asa albarka, Babu ce ka ai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin era ginin, don hatta sample dinsa da wararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne. Mamaki da al'ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun Bayan da escords suka auko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke ta fa uwa, saboda sabon gini ne baya a asar Uncle in nasa Ya mallake shi, shiyasa komai yake aure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero addu'o'i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya ro i Allah da ya yi mashi silar barin shi cikin sau i ba tare daya sha Wahala ba. Tun da suka shiga gidan Kamar wani ba auye Haka ya dinga bin ko'ina da kallo, wasu matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu yali tamkar zasu rubzowa mutun saman kanshi, Ga wasu Ha un twins stairs, masu auke da Glass Elevator a gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai asa. A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne an ubansu masu numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne, Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa Idan kana Tafiya, zallar ha uwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya zayyana ha uwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu are middle step da last step acikin gidan Alhaji musa ( Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana aya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar shi ko anshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata Ya ke yi masu. A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta udundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur'anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al' ur ani mai girma. "Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta ago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare al launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya are na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head inta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da aramin baki launin pink, Ba ta da iba ko mis ala zarratin siririya ce, abu ayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon. "Zeenat! Bacci ki ke Yi"? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta mi e tare da wurga wayar idanuwanta kan Mai shigowa akin, babbar macace mai cikar kamala, Ta auki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da iba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta aure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace in wuyanta da earrings inta na zallar diamond ne sai yali suke Yi da aukar ido. Muryarta Adisashe ta amsa mata"mommy karatun ur'ani nike Yi bacci ya auke ni bansani ba" ta yi maganar tana Yin mi a ha i da yin hamma "Ba ki ji dirar motoci ba ne"? Ras Taji gabanta Ya fa i, Muryarta na rawa ta furta"dad... daddy is he back "? Ta6e baki Hajiya Sarah tayi"ya dawo tun azu, yanzu haka yana a akinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa" Hankalin Zeenat Ba aramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko ba in Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da auna. Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa"ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi"? A hanzare ta girgiza kai" "I'm so happy he's back, na yi murna ai shi inne baya son takura" Murmushi tasakar mata"Albishirinki"! Da mamaki ta tsayar da eye balls inta kan face din momyn nata "Goro"! "Fari ko ja" "Fari" Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin ra a ta furta mata"Ba shi ka ai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom in da aka ware masa" Tun kafin Hajiya sarah ta arasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da aura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta "Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada" agowa Zeenat Tayi, tare da mi ewa tsaye Hijab in jikinta sai Ja da asa Yake yi. "Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa" tsantsar farin cikine akan fuskarta "No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a akinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa" Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta agara don a kwa aice take da son ganinsa "Na fa a maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko an gyalene ki yafa a kafa a," turo baki zeenat tayi da ar shagwa6a tace"Mommy ae shima Yaya shureim in yafi son mace mai sanya dogon hijabi" "To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa" ta are maganar da zolaya ta furta"Muslimatun matar limam" Dariya Zeenat ta sanya tana kallon mommyn nata. "Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri" Amasa mata tayi da toh Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab in jikinta, ta nufi toilet ta shige, cikin an mintuna ta fito Sanye da bathrobe (rigar wanka) fara yal a jikinta, hannunta ru e da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin. Zeenatu muguwar sangartacciyace ta saba tun tana arama duk In za ta yi make up ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai na aikin wahala ba, hatta sanya an kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda zumu in zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba, tun tana agaban mirror mai aiki ta wasa ofar akinta ta nemi zinin shigowa, ta tambayeta Ko tana Bu atar wani abu, tace mata a'a taje kawai za ta yi komai da kanta, ashe da rabon tasha wahala. Gaba aya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko mis ila zarratin tana da rawar kai da zumu i, tun daga kan Hoda da ta auko zata shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba aya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire guntulan Ya fa asa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data auka sai ya sil6e asa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba, don ta yi asararsu. Bayan Ta kammala an shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba, tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe inta, daga wajen glass in kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta asha e tamkar a company, Abayas, shadda
Chapter 62 · 0% Book details