Sashe 53
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Daga al alamin Boss Bature* ~Middle step~ Lokacin da ta ago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta aga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba aramin ru ar da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin Allah su ka ai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji da in wannan Ranar, Ta jima tana addu'a, Sam takasa mi ewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu are Sai sintiri suke yi saman kuncinta "Angel pls stop shedding ur tears" Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shesshe ar kuka ta ago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta wa anda suka kada jawur da su "Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi rayuwar kulle tamkar dabbobi har wara ni akan sauran an uwana tun suna jarirai, wannan ne karo na farko da zasu ani rayuwar anci acikin an uwansu mutane, Iya cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne, saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin rayuwarmu ba" Hankalin likitocin ba aramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda yai silar haifar masu da ciwon damuwa da ba in ciki Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye. Gabanta ne Ya an fa i Jin kukan Jemimah, Nan take shesshe ar kukan da ta ke yi ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo akin hannunta auke da Jemimah Tsabar jaraba ta runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie ka ai Take furtawa, jikin Angel na rawa Ta yunkura ta mi e da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta kar6eta sosai ta rungumeta a irjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata. "Angel" Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta ago tana kallonsu, A jere su ke shigo akin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar suman kawu nan su A hargitse kamar wa anda aka koro daga gidan mahaukata. Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da cannula na drip da aka sanya masu. Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da gudum gaske suka arasa shiga akin gaba aya suka ame Angel kamar zasu kada ita asa. Al'ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah, Aransu suna Mamakin aunar da suke yi ma aramar Yarinyar da su ke kira da Suna Angel. Farin Ciki kamar zai kasheta, Da i take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi da yar take Iya fitarwa "Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe mu" Su parveen ne ke kora mata jawabi "Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga" Maganar Batul tayi matu ar bata dariya, Da yar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta ameta Jikinta sai kerma Yake yi. Azeeza tana ma ale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa auke idanuwanta daga kan faces in Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu. "Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi," Hanna ce ta yi maganar Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin maganar "Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu kuma da kuke gani likitoci ne da nurses ha inmu ne kula da Lafiyarku, Za mu taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku auke mu tamkar an uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku al awarin zamu share maku hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu mi a ku ga Iyayen ku. Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun fara fahimtarta Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya"duk wani abu da kuke bu ata zamu yi maku shi, ku auka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu ha in kai, Ku daina Jin tsoron mu" Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi "Mun ha a ku wuri aya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan har ba Kuna atare da ar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga ku ga Mamanku Angel" Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana kallonsu, daga gani suna da mutunci. "Masoyiya Angel fa a min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba aramin aunar ki su ke Yi ba" Dr Brown ne yai magana ha i da aga mata gira aya, Sunnar da kanta asa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa. "Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki"? Kunyace ta rufe Angel da sauri ta aura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ru e a hannunta. Dariya Dr. laura ta saki"Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi" gaba aya sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta. Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu bayanan da suke so daga gareta. "Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata ayi, Yanzu fa a min me kikeson Ci ke da an uwan naki mu kawo maku" Cikin kulawa Dr. laura ke yi mata magana. Kallon sauran an uwan nata tayi "Ko ba ku jin yunwa ne"? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel, Dariya doctors in suka saki "Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel Fa a mana me kikeso akawo maki keda an naki don bama son barinku da Yunwa" Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta"komai muka samu zamu ci" Jinjina kai Dr Laura Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca"A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan sha" amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce. Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu "Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye min shi duka kaf, zanji da in hakan,' dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace"Zamu dawo Da Anjima, Kyawawan an mata, dole in za6i aya daga cikin ku, irin wannan Kyau haka" Dr Bown Yace"ai ba kai ka ai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar aya, ta ko'ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni" Dariya ce ta kubcewa Angel da Gabriel Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi"bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa ana kamun matan aure a Cikin su' Nisha i sosai suka sanya su. "Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da anki, Ki lallashesu su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku" Cikin sanyin murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga akin suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu. Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana ti ar dariyar Farin Ciki tana fa in"ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN" "Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun addara, Mun zama masu anci" Su Batul sun i sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai suka tsinci kansu a wannan wurin ba. Gabriel ne yai arin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin. Wayyo Allah da i Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu, Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen ha oransu tamkar Gonar auduga "Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya" Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu" warai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye ba in ciki da kunci sun are" Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba aya suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai da i suke ji saman ceilling akin suka urawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a rayuwarshi jin shesshe ar kukansu ta cika akinne Yasa ta soma yi masu magana cikin lallashi "Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a koda yaushe shi maha urci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya kar6i kokenmu yaji anmu ya raba mu da angin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu an ci ne zamu sha i Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita ba" Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu Cikin shesshe ar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin"Ni an uwanmu nake tunanawo wa anda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu, nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi" Naufal ya aura da cewa"babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya fa i, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku....." Kasa arasa maganar Yayi saboda kukan da ya ciyo shi. Javed ya dasa daga Inda ya tsaya"Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! " tunkan Ya rufe Baki Angel ta aura da cewa"Allah Sarki Unaiza ar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin zamu tsira ba tare dasu, Muna aunar an uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana Yankan auna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu ha u da su agidan Aljanna