← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 106

Sashe 103

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ne, Aunty Aneeleh fatima ta matsa mini akan muje muyiwa mommynta magana tasan idan na sanya baki zata bamu tallafin da zamu bu e, saboda muna mutunci da ita, duk cikin awayen fatima tafi sakewa dani har idan nayi kwana biyu banzo gidan su ba takan tambayi fatima ina awarnan taki mai dimple da yake haka take kira na, sai tace mata zata kira ni idan tana son ganina, Aunty aneelerh tsautsayi ne ya kai ni ga amincewa da maganar fatima, muka kwasa muka je wurin mommynta, muka fada mata dangane da beauty salon din da muke so za mu bu e gashi bamu da ku i, matar nan tayi dariya tace mana ai ba wani abu, ta ji da i da mu ka yi tunani mai kyau, ita tana son mutun me burin ya nemi na kansa, don haka zata bu e mana company da zamu dinga gudanar da kasuwancin mu harma mu zuba ma'aikata acikin sa da zasu dinga taya mu aiki, idan yaso zamu dinga raba riba da ita, a lokacin munyi mamakin jin zata bu e mana company mu da muke maganar bu aramin beauty saloon, ni bansan da wata manufa a asa ba, Ni da fatima munyi murna muka dinga yi mata godiya da addu'o'i, tun da ta bu e mana companyn bata ta6a kar6ar ribar da muke rabawa ba, duk in muka kai mata kasonta sai tace mana mu ru e a hannun mu zata nema yanzu bata bu atar ku i, Aunty Aneelerh tun muna tara mata ku in har dai fatima tace min mu kashe kudin ai mommynta bata bu atarsu shiyasa bata kar6a ba, in yaso daga baya in muka tara wasu ku in sai mu biyata, zuciya ta ebeni muka ha u ni da fatima mu ka kashe ku in, acikin su na cika da nawa ku in na sayi mota, Na canza wayata na sayi iphone 15, wayar da kika ga ina ru ewa a hannuna, Na ciri dubu ari uku naba ummin mu nace gashi nan tasa mun albarka kasuwanci yayi kyau, ummi taji da in ku in nan, dama tana bu atarsu daddy baya bata ku in da zatayi hidindimu dasu, duk nice fa nake taimaka masu idan na samu kudi, shi kawai ta 6angaren abinci ne yake yi mana ari, sai kuma kayan sallah idan tazo amma inba sallaba babu abunda daddy yake yi mana, kudin shi sai dai muga wasu suna ci, acikin ku in naba mahboob dubu hamsin shima yai ta yi mini godiya hada wallar shi saboda da in da yaji....' dakatawa ta anyi da yin maganar hawaye nabin fuskarta, tun kafin ta arasa jikin Aneelerh yai sanyi don tasan arshen zancen bamai da i bane. Jinjina kai zahra ta anyi kafin ta daura da cewa"Aunty aneelerh saida na tabbatar ku in sun are tukunna hankalina Ya kwanta, sai kwanan nan da Hajiya saratu ta kira awaya suna bu atar ayi masu decoration da kitso da unshi, lokacin dana duba asusun mu, ba mu da isassun ku in da zamuyi order na kayan da za'ayi masu amfani, dama dai ita hajiya falmata itace take yi mana hanyar da ake shigo mana kayan adon daga dubai, muka zauna nida fatima mukayi shawara sai tace min zatayi ma mom dinta magana, bayan sunyi magana da ita, sai ga fatima tazo wurin aikin mu idanuwanta jawur dasu, hankalina atashe na tambayeta lafiya meya faru da ita, cikin shesshe ar kuka tace min mominta tace idan har muna so tayi mana order din kaya mu fara tura mata ribar da muka tara mata a hannun mu, tana bu atar ku in da gaggawa, tun anan fatima tace mata ai babu kudin nan mun kashe su, tsabar 6acin rai ta zazzaga mata masifa tamkar ba ar ta ba, hada mari ta kwasa mata a fuska, ko lokacin da tayi mini magana fuskarta da sahun yatsun hannun mahaifiyarta, Hankalina ba aramin tashi yai ba, saboda ni bansan inda zan samu ku i na biyata ba, daga ni har fatiman bamu da ku in a hannun mu, Aunty Aneelerh nasan bamu kyauta ba tunda ba kyauta ta bamu ba, amma muka ta6a mata kudinta bayan yarjejeniyace muka ulla da ita akan duk in aka samu riba zamu raba kaso uku, matsalar da aka samu ku in data bar mana a hannun mu ta i kar6arsu har saida tsautsayi yasa muka ta6a su...." fashewa tayi da kuka Aneelerh ta natsu tana dubanta. "Nayi arin Na saida motata don na samu na biyata ku inta sai dai bansamu wanda zai siya ba, Jiya ina kwance saman gado na gama shan kuka na sai ga kiran fatima awaya, na aga muka gaisa da ita, tace min mominta tana son Yin magana dani inzo in same ta agida, hankalina ya dan tashi don tunda mu e nu u nu u akan yadda zamu biyata kudin bata ta6a yin maganar dani ba, tsakaninta ne da fatiman, nace mata zuwa gobe zanzo gidan nasu, jiya ko bacci banyi ba, da sassafe na shirya babu wanda ya san na fita daga gidan nan naja mota naje gidansu fatima babu kowa afalon gidan saida mai aikin gidan ta fito daga kitchen muka gaisa take ce min ai hajiya ta fa a mata game da zuwana in shiga aki tana jirana, da sauri na juya na nufi akinta gabana na fa uwa abakin kofar akin nayi mata sallama, muryarta asa asa tace min wanene? nace mata zahra c awar fatima mai dimple, tace in shigo ciki....." dakatawa ta anyi da yin maganar tana faman yafta wayar idanuwanta. Cikin agara da sonjin arashen zancen Aneelerh tace"naji kinyi shiru? Me tace maki ne"! Yawu zahra ta hadiya muryarta na an rawa ta aura da cewa"Ina shiga akin na same ta kwance saman gado daga ita sai an undy shara shara ajikinta, arude na juya zan fuce da sauri ta kira sunana zahra zonan, cak na tsaya ba tare dana juya na dube ta ba, ta sauko daga saman gadon ta nufo inda nake a tsaye ta tsaya daga bayana ta soma yi min magana . Ya maganar ku ina da zaku bani? Nayi magana da fatima tace min atare kuka kashe kudin meyasa zahra? Ban ta6a tunanin za ku yi mini haka ba, Na yadda daku na dam a maku amana amma kuna nema kuyi mini wasa da dukiyata, ko dan ba ku san zafin nema bane"? fa a sosai tayi mini bansan lokacin dana fashe mata da kuka ba ina ro onta akan tayi hakuri nayi mata al awarin zan biyata ku in ta cikin satin nan, Aunty Aneelerh ba zato ba tsammani naji ta sanya hannu ta ru o hannuna, ta juyo dani ta rungumeni a irjinta, ban auka da wata manufa ba sai da naji tana matse ni a kirjinta gabana yaci gaba da fa uwa, cikin dabara ta mi a hannu ta bayana ta datse ofar akinta da jamlock, ba tare da sanina ba...." ganin yadda Aneelerh ta zaro ido waje yasa zahra ta dakata da yin maganar la66anta na kerma. Aneelerh tace"zahra ke nake sauraro uban me tayi maki" a kausashe Aneeleeh ta furta mata hakan, cikin ru u zahra tace"nayi okarin raba jikina da nata amma saita ara tighting dina, ta zame mayafin dake akaina, ta sanya hannu tana shafa sumar kaina cikin ra a take furta min"meyasa nake yi mata kuka? Ko dan saboda tayi mini fa a akan ku inta ne, muryata na kerma nace mata ta yi ha uri zan biyata kudinta, tace min in kwantar da hankalina ai ba dole saida ku i zan Iya biyanta ba, A jikina ma ina da abun da suka fi ku i daraja, idan na amince na bata ha in kai zata yafe mana bashin harma ta yi mana order na kayan decoration din da muke so, cikin rashin fahimtar maganarta nace mata ni ban gane me kike nufi ba? Menene yafi ku i daraja a jikina? Kuma wani irin hadin kai kikeso in baki"? Har lokacin bata raba ni da jikinta ba, saima nishi da naji tana saki, tace min tana bu atata jikina kawai takeso, zatayi amfani dani. Saboda yarda da nayi da matar saina dauka wasa take yi mini, Cikin sanyin murya nace mata mommy amma dai zolayata kikeyi ko"? Na fada ina kokarin raba jikina daga nata saidai ta i bari inyi hakan, kamar zata maidani cikinta. Babu alamun wasa a kalamanta tace min" Zahra na ta6a yi miki wasa irin wannan? Nace mata a'a, tace min toh dagaske take, dama ta jima tana kwa ayin son kasancewa tare dani bata samu damar yin hakan ba don ta lura kamun kaine dani kuma ni ba ar harka bace, shiyasa ta yi dabarar amincewa da bu atarmu ta bu e mata company kuma ta i kar6ar ku in ribarta dake a hannun mu, Ashe ma ashiya ta shirya mini saboda tasan zamu iya ta6a ku in, Ni ban ta6a tunanin matar zatayi mini haka ba. Aunty Aneelerh data fa amin hakan tsigar jikina ta tashi, na rasa uwar ubana, na soma kiciniyar wace kaina daga ru on da tayi min ina fadin ni ki sake ni in tafi gida, wlh kin ban mamaki na dauke ki tamkar mahaifiyata saboda aunar dake a tsakanina da fatima ashe nayi babban kuskure, Ni bazan ta6a baki ha in kai don mu aikata sa6on Allah ba, kema inayi maki fatan Allah ya shiryeki,' sai da nasha wahalar bangajeta, da gudu na dam ofa zan bu e naji ta a gar ame kafin in zare jamlock din Naji ta dam eni ta wurgar dani saman gado tana fadin"baki isa ki kubcemun ba zahra, dama nasan zakiyi min taurin kai shiyasa na biyo maki ta wannan hanyar, wlh idan har kika bijirema bu atata zan saki dole ki biyani ku ina a yau in nan idan ba haka ba zan dam a ku hannun lawyer dina, sannan zan rufe companynku," Ina kuka nace mata naji ta bani lokacin da take son ku inta In sha Allah zan biyata amma ni kada ta kuskura tace zata ta6a jikina, ta jira taga idan ban biyata ba sai ta yi mini duk abun da ta ga dama, tana faman sakin
Chapter 103 · 0% Book details