Sashe 15
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Daga al alamin Hafsat Bature* ~Middle step~ _A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ru u ru u kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head inta jijiyoyin ne.... A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin aki, tun suna kuka har sun fidda rai da an uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shesshe ar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ofar akin tsohuwa Tamira suka zuzzu una, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun afe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba oshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Da yar ne yai tsawaicin kwana. A firgice su ka ago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin akin su, jiki na kerma suka mi e suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba aramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana. "Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima an uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni a ne ga tsohuwa Tamira"! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi. Cikin shesshe ar kuka Haris yace" an..uwan mu suna a cikin akin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ofar....." tun kan ya kai arshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ofar Nan ta ke ofar Ta bu A fujajen Ya fa a Cikin akin Hankalin shi a matu ar tashe Ya ke binsu da kallo aya bayan aya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume asa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform in su yashe a kasa da ta Cire masu, Da arfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dun ule, Tsabar unar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa irjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya ha iyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji. "Ya Allah ka auki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne" Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa'iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe aya, tangal tangal yai kamar zai kife asa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai umin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da aya daga cikinsu ba in ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel in har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan ba ar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar arfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zu unna cikin rauni na murya ya furta"ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni ka ai a cikin wannan Duniyar mai cike da ru ani"? Da yar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta ago da runannun idanuwanta wa anda suka ka a jawur dasu ta ura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi. "Hada kai Aka kashe min an uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine"! ago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yun urin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dun ule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko'ina tana fa in Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana an uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata arasa maganar ba kuka Yaci arfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka aukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ai, Maganar su ta arshe ya soma tariyo acikin kanshi. "Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ADDARA! Ka yi min al awarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da sa on mu zuwa ga mutanan duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici da ba in Cikin ganin yadda ake tauye wa ananun yara ha insu na rayuwa, basu ji ba basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a lalatasu A antar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a wula ance! Ka fa a min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da ka yi tozali da gawata ka ara Jin warin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka, idan mutuwa ta ris e ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan kurkukun addara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni........." lokacin da tsohuwa Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana fa in zai yi duk abunda take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan bayan shi ga an uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku tarwatsa tarihin kurkukun addara, Azzaluman shuwagabannin da suka ire shi ku tabbatar tun agidan duniya sun ani ku arsu kafin su koma ga mahaliccin su bana so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da arfin ikon da ku ke dashi wurin yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin da i da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin da i, zan yi kuma alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya ro e ta alfarma aya kafin faruwar duk wa annan abubuwan yace mata yana so ta kar6i musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi"Ba zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda umbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi arin fahimtar da ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son bayinsa wa anda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare shi, da yar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta arshe data furta mashi"Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a akin su, Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa akin Madubin sihiri Ka canza ganin su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba......wannan itace magana ta arshe da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa akin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har yaje gare ta. Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffa irjin shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi mata ne yasa ta sassauta kukan nata...... Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin akin, Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke yi. Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfa owar Danish, Ba zato ba tsammani ta ga yatsun afarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta mi e Sai dai kash afarta ta i bata ha in kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling akin na tsawon da a talatin kafin Ya yun ura ya mi e zaune.... Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi kamar bai dawo hayyacin shi ba. Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata' il saboda munin da ta yi ne yasa bai gane