Sashe 100
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsaresu da ido "Yaran Fa akwai kyau, Yanzu ummi har kina Iya zama wuri aya dasu ba tare da kin rage zafi ba"? Shiru ummi tayi mata ba tare data tanka mata ba, hankalinta na akan prisoners, ta ura masu ido, hakanan ta dinga jin bugun zuciyarta na aruwa, ba tare da sanin dalilin daya haifar mata da hakan ba, jikinta yai wani irin sanyi, aya bayan aya take bin su da kallo, yayin da suke gaisawa da sojojin cikin raha suke amsa masu. Sai daga bisani Ummin America ta bu e murfin motarsu, atare suka fito ita da Natasha, Hankalin su Angel Ya dawo kansu, Kallo aya tayi mata sai da gabanta ya fa i, kuma nan take ta gane wacece ita, tun da taga uban hips dinta da boobs dinta da suka cika irjinta, ranta ya bata cewar tabbas itace matar da aka dam a ma amanarsu, tun da ta fito hankalin kowa ya dawo kanta, taku aya girgiza goma, wankan suit din jikinta ya tafi da imanin kowa dake awurin. Kallon kallo suka soma bin juna da shi, tsakanin prisoners da ummin america, da kuma dr. Laura, da jami'an isod, da sojojin da suka halarta, sama sama suka soma gaisawa da ita, Dr laura ta ha e rai kamar yadda itama ummin american ta aure mata fuska, bayan sun gama gaisawa da juna, jami'an suka bu e boot na motocin da suka zo da su suka auko suitcases dinsu tare da jakunkunan kayansu, gaba ayansu suka unguma zuwa cikin departure gate din Airport, ta inda suka samu sau i, Jirgin da zai auke su privet jet ne mallakin Jami'an isod, babu bu atar jira ko wasu shaidu, An riga An shirya masu komai su kawai ake jira domin tafiya, duk inda suka bi darewa akeyi abasu hanya saboda sojojin dake atare da su, prisoners sai an kalle kalle suke Yi, sunga wuri mai kyan gaske ga mutane launi daban daban suna ta yin zarya acikin wurin, Yankin da jirginsu zai tashi fili ne na musamman aka ware shi domin tashi da safkar jirage masu zaman kansu. amemen Privet jet ne Aka tanadar masu, Mallakin Chief of isod, Aljannar duniyace ar ubansu a wurin ha uwa, tun daga wajen jirgin zaka fara cin karo da sunan ISOD da aka rubuta da manyan haruffa ajikinsa. Idan ka shiga cikin jirgin kamar ka shiga ha en villa ne saboda ha uwar kayan alatun dake acikin sa, akwai Falour wanda yaji hadaddun leather seats masu numfashi, tare da ayatattun tables, ga fine carpet shimfi e saman floor na jirgin, bayan shi akwai large flat-screen TV, ga Conference table domin yin meeting, a kewaye yake da kujeru, ga kitchen da bathroom, and privet bedroom da kuma dining area, Komai fa akwai shi acikin jirgin babu ce ka ai ke babu, ta ko'ina sanyin A.c ka ratsa cikinsa. Bayan sun sauka abakin jirgin, Hankalin su Batul Ya i kwanciya tun da su ka yi arba da jibgegen jirgin dake agabansu, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da abu kamar wannan ba, duk sun bi sun rude, sai faman zazzare idanuwa suke yi, badan Angel na atare da su ba, da tuni wasu daga cikinsu sun zauce saboda tsabar ki ima, bankwana suka somayi da sojojin da suka rako su, Dr laura hada hawayenta na rabuwa da su, aya bayan aya saida ta rungume su, tana yi masu fatan alkhairi, Jemimah da Azeeza sunji acin rabuwa da ita, sun sha kuka hawaye duk Ya 6ata fuskokinsu, lallashinsu ta dinga yi tana kwantar masu da hankali, tace kada su damu zata iya zuwa har Nigeria tagan su, babu wanda bai ji kewar rabuwa da su ba, Dr mark da brown suma sun matse wallarsu, hatta nurse jessica da Rebecce sai da su kayi kukan rabuwa da su, musamman masoyiya Angel kowa ya saba da ita, suna sonta sosai, ummin america tuni tayi sallama da awarta Natasha, bayan sun gama an rungume rungume, sojojin da ke atare dasu sunyi masu fatan sauka lafiya, lokacin da zasu hau matakalar jirgin da yar suke taka staircases din, har dai suka samu damar shiga ciki, al'ajabi ya kama su ganin ha uwar jirgin, kowan nan su Ya samu wuri saman tausasan leather seats din suka zazzauna, tun da suka shiga jirgin ummin america bata tanka masu ba, sai dai kallon kallon da suke Yi a tsakanin su, ita dai Angel damuwarta Danish inta, Ya ameta, babu alamun lafiya atattare da shi, jikin shi yai zafi rau. Lokacin da jirgin Ya soma tafiya Yana bin hanya kafin Ya aga sama, Hankalinsu Azeeza ba aramin tashi yai ba, jami'an Sunyi arin kwantar masu da hankali, ganin yadda su ka ru e jikin su ya hau yin kerma, sun fahimci mugun tsoro ne da su, Angel ce ta tunasar dasu akan suyi addu'a, aiko atare suka hada baki suna karanta addu'o'in data koya masu. Cikin anin lokacin jirgin Ya aga sama Ya keta hazo can cikin sararin samaniya, Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke kamar an yaye masu tsoron da suke Ji, hankalin kowan nan su ya kwanta tun da aka kunna masu kallo a tv, ban da na Angel, Yanayin fuskarta ya canza, sakamakon maganganun da taji Danish yana furta mata acikin kunnanta, muryarshi arauna ce yake fadin baya son mutane, haushin su yake ji, yana ji kamar ya kashe su, jinin su yake sha" an hanjin cikin ta ba aramin ka awa su ka yi ba, sai faman zazzare ido take yi, babu wanda ya lura da halin da take a ciki, sau in ma acikin kunne yake yi mata ra a, sautin muryar baya fita, kuma akwai tazara tsakanin seats dinsu dana sauran an uwansu, aya daga cikin jami'an isod ne Ya auko mashi eye mask ya mi a ma Angel don ta sanya mashi a tunanin shi hasken jirgin ke bayaso shiyasa ya cusa kanshi saman kafadar Angel may be ko yana son ya runtsa ne. Tun da ta sanya mashi eye mask taji yayi shiru ya daina magana alamar bacci ya dauke shi, a alla ta sauke ajiyar zuciya yafi a irga, addu'o'i taci gaba da karanto mashi tana tottofa mashi saman sumar kanshi, fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane zai faru da shi, gashi ta manta bata nemi takardar dake auke da address din gidansu salsabeel, duk da bata tunanin ma ko sunje zasu samu abunda suke so. A Kishingi e yake saman shimfi an full-sized bed dinsa dake acikin privet room na jirgin, ya aura kansa saman tattausan pillow, Shin wanene wannan kyakkyawan matashin saurayin? A jin farko afagen kyau da asaita, Namijin duniya, A halitta madai-dai ci ne, mai wani irin faffa irji a bu e yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen irjinsa, Ko an wrestling bazai nuna mashi irar arfi ba, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da arfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa farare tass ga su so sexy, masu auke da launin wayar ido reddish brown, har shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows insa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su ha e da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala'en yi mashi kyau, abun da yafi komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi, kuma burin kowace a mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an fa a maka ba, su kan su ku in raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida girman girka, mutum ne shi da bai auki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko'ina Allah ya hore mashi, yana matu ar jin an talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da abi'unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita daban ko acikin jikokin family insu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba'a sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi, babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin mutane Yana zalunci, In kuwa ya dam i irin su, mai watar su sai Allah, shiyasa mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta asaitaccen Namijin nan ba, Ka an ne na Iya fa a maku sauran ku biyo ni acikin labarin, Yanzu ne wasan Ya fara. Tun da ya aura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi irar Apple macbook pro bai yafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist watch irar Rolex submariner ha ar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta cikin laptop dinsa, ayataccen table din dake agaban gadon shi auke ya ke da Mug na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali a kwance bai da wata damuwa. Awanni da suka auka acikin jirgin ba aramin da i suka ji ba, saboda an gatanta su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake yi, Danish ne ka ai baici komai ba, tun da bacci ya auke shi bai farka ba. * ABBAN SOJOJI KURKUKUN ADDARA *Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun addara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita