Sashe 28
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta an kalli fuskarshi"Na gaji Danish afata ciwo ta ke yi min" ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya mi auke da ita, ba aramin da i taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta ameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman sha ar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko'ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari al dashi. "Mun araso," Jin abunda yace ne yasa ta ago da kanta, tana arewa wurin kallo, nan ta ke ta ji tana sha'awar shan ruwan, Zu unnawa yai ta sauko daga saman bayan nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu . "Danish ishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu ebi wani mu kai ma su Parveen ko"? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana"Wanka nake so nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti" Har saida gabanta ya fa i jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare da kashe mata ido "za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne"? gabanta ne ya dinga fa uwa sai ta ga kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar. Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu, ko ta ku aya bata kai ga yi ba taji Ya dam ugunta, arfi ba aya ba, Duk yadda taso ta kubce mashi ta kasa, matseta yai a irjin shi, A hankali Yai amfani da hannun shi aya wurin zame rigar Jikin shi, tare da wandon kakinsa na Giant, ya rage daga shi sai short fari, saman gungurumeman dutsen dake agefen ruwan, ya jefar da uniform inshi. kamar jinjira haka ya auke ta, kaitsaye Ya nufi Cikin ruwan da ke gangarowa, ba yadda ta iya dashi, Tana kuka tana fadin bataso ya yale ya rabu da ita, ahaka yayi mata wanka tass ya wanketa Kamar yayi amfani da sabulu ita kanta tayi mamikin yadda Jinin jikinta ke fita, Farar fatarta sol ta dawo har wani sal i takeyi da aukar ido, hatta uniform in da ke ajikinta sun wanku sosai sun manne ma fatarta, kwantar da kanta yai saman broad chest inshi, Ya cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanta yana cuccu ata da ruwa, Jinin da ya dan are mata a cikin kan ya dinga fita, gashin kanta ya dawo ainihin launin shi dark brown mai kyan gaske, ba aramin taimakonta yai ba da yayi mata wanka, Ita kanta tasan bazata iya wanke najasar dake a jikinta ba, ame jikinshi tayi sosai la66anta na kerma take fa in"sanyi Danish san yi ni ke ji, tamkar ana ara gudun ruwan sun ji e sharkaf acikinsa, sai da ya kammala tsaftace mata jikinta tukunna ya aukota saman kafa arshi ya dawo da ita Gefen dutsen da ya aura uniform inshi. Tun da ya sauke ta ta fa a ma faffa irjinshi, ta zagayo da hannayenta saman bayanshi, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, idanuwanta a lumshe, ita ka ai tasan da in da ta ke ji, da farko taji haushi da ya yi mata wanka, amma yanzu ta fahimci Dalilin dayasa ya tursasa mata yin wanka, jikinta yayi mata da i wata irin ni'ima ke sauka, tamkar an yaye mata damuwar dake acikin zuciyarta, sun natsu suna sauraron bugun zuciyar junansu, irin yanayin da yafi son kasancewa tare da ita, yana son Angel dinsa fiye da yadda yake son kanshi, a shirye yake daya sadaukar da ranshi indai akanta ne" Fatar wuyanta ya urawa ido fara sol sai an tabannin da ba arasa ba, na gurjewar da tayi, aura tafin hannayensa yai asaman bayan nata, "My Angel!" a kasalance ya furta sunanta shiru bata amsa mashi ba "Are you feeling sleepy?" kamar yayi magana da bango shiru ta i bu e ba ki ta yi magana, arin rabata yayi daga irjinsa, sai dai ta i bari ya ago da ita, ta yi tighting in shi tamkar zata koma cikin shi, baiwar Allah, Dama abu ace take da ta samu inda zata sassauta ra in da ke acikin zuciyarta, abubuwan da suka faruwa a rayuwarta ta soma tariyowa tun daga lokacin da ta mallaki hankalin ta, har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji da kuma fa owarta gidan kurkukun addara, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta, jin shesshe ar kukanta ne yasa shi rikicewa ya shiga ambaton sunanta adabarbarce, da yar ya iya 6an6arota daga irjinshi, eyes dinshi akan fuskarta ta runtse idonta "My Angel I don't want you to dwell on what happened before, I know it hurts you, but please forget about the past. I don't like to see you cry. tun da ya soma lallashinta bata bu e idanuwanta ba, tsawon mintuna kafin a hankali ta ago da kanta tare da jingina bayanta jikin dutse. Matsawa yayi jikin aton dutsen ya mi a hannu ya ru o uniform in shi, A tsanake Ya sanyasu a jikin shi "Zaki Iya jirana anan"? girgiza mashi kai tayi"tsoro nake ji, ka maida ni cikin an uwana" yaso ta amince ko dan ya samu ya shiga cikin Dajin Ya nemo masu abunda zasu ci, kwantar mata da hankalinta yai"Yanzu zan dawo, bana so an uwanmu su tashi da yunwa pls ki jirani anan, ba abunda zai same ki, kada kije ko'ina" bai jira amsarta ba, ya 6ace ma ganinta. Tunawa da cewa ita fa yanzu mai anci ce yasa ta an saki murmushi, har ta fara tunanin irin mugun kisan da za ta yi ma wa anda su ka sadaukar da su, badajimawa ba ta soma Jin motsin tafiyar mutun a firgice ta bu e idanuwanta lokaci aya ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ganin Danish ne ya dawo hannun shi a ru e da Zomayen Daji da ya yo masu farautarsu, ya ru afafuwansu da hannu aya, yayin da ayan hannun ke aru e da gorar ruwan, mamaki ne ya kamata ganin zomaye, mi a mata gorar ruwan yai da sauri tasa hannu ta kar6a, Acike take da ruwa, jera kafa a su ka yi suna tafiya suna satar kallon juna, abunda ya aure mata kai yadda Danish yasan komai dangane da Daji mutumin da bai ta6a fita daga cikin kurkuku ba, Yanzu tadaina yi mashi kallon solo6iyo, A Namijinsa ta ke kallon shi. Lokacin da su ka araso Gaban Kogon dutsen, Atare su ka shiga Ciki, Ya ajiye zomayen saman korayen ciyayin da ke shimfi asa, ya ago da ido ya kalle ta, zanje na ha o itace yanzu zan dawo, Ta amsa mashi da toh,' Bayan tafiyarshi ta ajiye gorar ruwan asa, kafin ta nufi shimfi ar su, ba ta yi mamakin ganin ba su farka ba saboda ta riga ta gane aikin Danishi, gaban akwatin kayansu ta zu unna ta bu e ta curo tsoffin uniform inta, Cikin anin lokaci ta canza na jikinta da suka ji e ta shanya su daga wajen dutsen, dawowa tayi cikin kogon Agaban shimfi ar ta zu unna tana are masu kallo, idanuwanta akan Jemimah da Azeeza, da i kamar zai kasheta, a agare ta ke da su farka su ga wurin da Allah ya kawosu tasan zasu sha mamaki da al'ajabi kuma zasu ji da in cika masu al awarin da ta yi. Sam ba ta ji motsin shigowarshi ba, har sai da yai mata gyaran murya tukunna ta waiwayo su ka ha a ido da shi In zo in tayaka"? girgiza mata kai yai" a'a bana so ki wahala" mi ewa tayi tare da zuwa gabanshi ta zu unna tana are mashi kallo, hankalin shi ya koma akan itacen da ya ke jerawa bayan ya kammala ya auki duwatsun jiya da yai amfani wurin rura wuta, duk wani motsin shi akan idonta har ce mata yai "kije ki huta mana, ba kince kina jin sanyi ba? Ki auko bargo" ma e mashi kafa a tai alamar ba za ta je ba. Bawan Allah shiya zauna zaman gasa masu naman, sai mai o yake yi kamar an soya shi da mai, Kitsan jikin zomayen ne ke narkewa, bayan ya kammala ya aura gasasshen naman da ya tsira Jikin icce saman faffa an ganyan da ya shimfi a a asa. "Danish" agowa yai tare da kallonta, bakomai ya gani acikin idanuwanta ba face Tsantsar tausayin shi "Kada ki damu kanki am ok, idan zan shekara inayi maku bauta ba zan gaji ba" kalamanshi sun ara sanya mata aunarshi acikin zuciyarta. "A ina ka samu wannan gorar ruwa"? Tai maganar tana nuna ta da yatsa "A cikin Daji ba abunda ba zaki Iya samu ba, Hada kan mutun" murmushin gefen fuska ta saki, ga dukkan alamu zasu fara kafa nasu tarihin soyayyar tun acikin Daji. agowa yai da lumsassun idanuwanshi ya aura su kan fuskarta "Can you eat by yourself? Or do I need to feed you?" Girgiza mashi kai tai" ka wahala sosai, ni ya kamata in baka da hannuna" ya ji da in maganarta har ya bu e baki da niyar mayar mata da martanin maganarta, kwatsam! muryar Jemimah ta katsesu da wani irin sautin mai amo take kwa awa Angel kira amatu ar gigice take fadin"Genie wayyo Allah Genie Zafi Jikina ayi nake ji" Ahanzarce Danish da Angel suka mi e da sauri suka nufi shimfi arsu atare suka zu unna agabansu, Hannu biyu Angel ta sanya ta auko ta zuwa saman jikinta, ta ameta, Duk tabi ta furgice sai kuka takeyi masu tana harba afafuwanta, Sautin kukanta ne ya farfa o da sauran an uwan nasu, Batul ce ta fara mi ewa kamar fatalwa idanuwanta luhu luhu sun ka a jawur, baiwar Allah har fa awa tayi sai uban haske, gashin kanta kuwa a hargitse yake, Bu e idonta keda wuya ta sauke su akan na Danish dake kallonta, Muryarshi na an rawa ya furta sunanta"Ba..tul" auke idonta tayi daga kan fuskarshi ta mayar dasu Kan kogon dutsen da suke aciki sa o da lungu tabi