Sashe 102
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_THE PRISONERS E26 *Daga al alamin Boss Bature* Confusion of the heart Tun da Aneelerh ta turawa numbar sa o har yau ba'a tuntu6eta ba, abun ya dame ta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji da i, kullum ne sai ta ara jaraba kiran layin ko za'aci sa'a mamallakin wayar ya aga amma wani iko na Allah a kashe take samun layin duk ta damu da son jin wanene. Fitowa ta yi daga cikin akinta hannunta ru e da wayarta, akin zahra ta nufa da niyar ta fa a mata halin da take ciki wata'kil ta bata shawara akan abun da ke damunta. A bakin ofar akin ta fara yin sallama, shiru ba'a amsa mata ba, kusan sau uku tana kwa a sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata' il kuma wanka ta shiga. Haura afa ta yi ta shiga akin zahra, tun abakin ofar room din ta fara cin karo da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba aya ta watso su saman floor, nan take hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta ago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta da pillow dinta duk ta watso su asa, Komai na akin ta tarwatsa shi. Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai tsafta dagangan dai bazata ta6a barin akinta a hargitse ba. Cikin tashin hankali ta soma wala mata kira"Zahra! zahra!!" shiru babu amsa, ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga akin ummi, da sauri Aneelerh ta fuce daga akin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami da ummi zaune suna fira, juyawa tayi da sauri ta nufe su, babu wanda Ya lura da ita acikinsu har saida ta furta"ummi mami Ina zahra" kusan atare suka ago suna kallonta, gaba daya sun fahimci babu kwanciyar hankali atattare da ita. Ummi tace"kin duba akinta baki ganta ba"? Kafin ta bata amsa mami tace"Aneelerh wai lafiya? Ya akai naga kamar bakya acikin natsuwarki" Muryarta na an rawa ta furta"bakomai, na duba akin zahra ne ban ganta ba" Mami tace"shine duk kika aga hankalin ki? Sai kace yau ta fara fita daga gidan, kema kinsan zahra idan har ba wurin aiki taje ba toh tana acikin gida" Ummi tace"tun azu fa ta dawo, ki kwantar da hankalin ki, bata wuce cikin akinta, Ki koma ki sake dubawa" Juyawa tayi da sauri ta nufi akin donta ara dubawa. Bayan tafiyarta ummi ta dubi mami" awancen Aneelerh da zahra ba aramin burgeni ya ke yi ba, har mamaki nake yi idan naga yadda Aneelerh take jan zahra a jiki, duk da ta girme ta" Mami na murmushi tace"ai shi awance ba a shekaru yake ba, indai mutum Ya mallaki hankalin shi ko da ya girme ka zaka Iya awance da shi, Ni kaina ba aramin burgeni suke Yi ba, Allah dai Ya bar zumunci" Ummi tace Ameen ameen. Daga haka su ka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu. Afujajen Aneelerh ta fa akin zahra tana faman Yin haki, ta kware murya tana ambaton sunanta"Zahra! zahra! Nasan kina jina, Dan Allah kiyi mini magana" Still babu alamar za'a tanka mata, ranta ne ya bata cewar wata' il ta fita ne ba tare da sanin kowa ba, Har ta juya zata fuce daga akin ba zato ba tsammani ta soma jin shesshe ar kukan zahra, da sauri Aneelerh taci burki, a sukwane Ta juya tana bin ko'ina na akin da kallo, a arinta nata gano inda zahra ta 6uya, hankalinta yafi karkata akan toilet din akin, da sauri ta arasa bakin kofar ta kara kunnanta, sosai take jin kukan zahra mai matu ar tsuma zuciya. Muryarta na rawa ta furta"Zahra meya faru dake? Wanene ya ta6a min ke? Dan Allah ki fa amin zahra, ashe kina jina shine kika i tanka mun ko?" cikin shesshe ar kuka zahra tace"...Aunty Aneelerh babu abun da ke damuna, kawai bana son kowa ne a kusa dani" "Ki fito daga cikin toilet din muyi magana zahra, ni bana so inganki acikin damuwa, kema kin sani har farin cikina zan Iya sadaukarwa saboda ke, don haka ki fito muyi magana" cikin kwantar da murya Aneelerh take yi mata magana. "Zahra ke nake jira ki fito muyi magana, wlh idan kika bari na haura afa ta daga cikin akin nan to kada ki yi tsammanin zan waiwaye ki, haba dan Allah, ina amfanin irin hakan? Ashe dama baki auke ni kamar yadda na auke ki ba? Har zaki Iya ke6e kanki cikin damuwa ba tare da kin neme ni ba"? A fa ace Aneelerh ta ambaci hakan, duk don ta samu zahra ta bu ofar toilet din. Bugun ofar tayi da hannunta"kada Allah yasa ki bu ar rainin wayau" ta fa a tare da juyawa ta nufi ofar fucewa daga dakin, Bu ofar toilet din zahra tayi, Fuskarta sharkaf da hawaye idanuwanta har sun kumbura, kumatunta sunyi jawur dasu, Short ne a jikinta tare da farar vest, Sumar kanta kamar ta mahaukaci sabon kamu. Da gudun gaske ta nufi Aneelerh dake arin fita daga akin, Gaba aya ta fa a saman bayanta ta rungume tana cigaba da yin shesshe ar kuka. Ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, tare da kai hannu ta ru o damtsen zahra ta zagayo da ita, har saida gabanta ya fa i ganin yadda hawaye suka wanke mata fuskarta tamkar ba zahra ba, damuwace arara akan fuskarta, kwantar da kanta Aneelerh tayi saman kirjinta, a hankali take shafa sumar kan zahra da yatsun hannayenta. "Ya isa zahra, ki daina kuka bana son ganin hawayenki,' cikin murya kuka tace"Aunty Aneelerh ba zaki gane ba, Ni ka ai nasan halin da nake aciki, Allah ji nake kamar in ha iyi zuciya in mutu kowa ya huta" Kalaman zahra sun ara aga mata hankali, tabbas akwai gagarumar matsala, Yarinyar da koda yaushe fuskarta dauke da murmushi komai zaka yiwa zahra a duniyar nan baka isa ka 6ata mata ranta ba, sai gashi a yau itace take Yin kuka har tana fa in kamar ta ha iyi zuciya ta mutu. "Kiyi ha uri zahra, bai kamata kina yin wannan furucin ba, Idan ma wani abune ke damunki meyasa ba zaki kai kukan ki ga Allah ba? sai kawai ki kulle kanki a toilet kina kuka? Hakan ya dace? Kina tunanin shine mafita a gare ki? Ga ummi ga mami, ga mahboob, ga abie da uncle uwa uba ga kuma ni meyasa ba zaki tuntu6i aya daga cikin mu ki fa a masa damuwarki ba? Kin tsaya kina yin zurfi ciki a arshe ki yi wa kanki illa amma fa amana da zakiyi shi zaisa ki samu maslaha na abunda ke damunki, ko da ace bamu da abun da zamu taimaka maki wurin yaye damuwarki zahra zamu Iya baki shawara ko mutayaki da addu'a akan Allah ya yaye maki" Fa a Aneelerh tayi mata, sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, ru o hannunta Aneeleeh tayi"wuce ki shiga toilet ki wanke fuskarki Ina jiranki" ta fa a tare da sakin hannun zahra, baiwarAllah jikinta duk ba wari tana tafiya tana waiwayon Aneelerh, yayin da hawaye ke cigaba da fita a idonta. Kafin fitowarta Aneelerh ta bar akin ta nufi falo, fridge ta bu e ta dauko mata ruwa me sanyi. Cikin tafiyar sauri ta nufi akin. "Aneelerh kinga zahran ne"? Muryar mami ce ta katse mata hanzarinta, ba tare da ta juya ta kallesu ba ta bata amsa da cewa"Eh mami, ashe toilet ta shiga" Bayan ta shiga akin, ta daura ruwan a gaban mirror, ta koma bakin door din akin ta soma tattara kayan da zahra ta watsar ta maida su a ma'ajiyarsu. Ba ta jima da zama a gefen gadon ba, Zahra ta fito daga toilet, ta wanke fuskarta kamar mara gaskiya ko ha a ido da Aneelerh bata son yi, saman mirror chair ta zauna tana fuskanta Aneelerh, sai dai ta ta agowa su ha a ido da ita. "Ga ruwan nan ki sha" ta fa a tana nuna mata robar ruwan, data ajiye mata, Yatsun hannunta na kerma ta auki bottle water din ta cire murfin ta soma akar ruwan kamar zata ha a da robar duka ta shanye, bayan ta gama sha ta maida murfin robar ta daurata gaban mirror. "Zahra ina sauraronki, Ki natsu ki fadamin meya faru dake? Da har yaja kika kulle kanki a toilet, bana so ki furta mun kalmar babu komai! Ranki zai Iya 6aci" fuskarta a aure tamau tayi mata maganar. Zahra na faman sunnar dakai, idanuwanta akan yatsun hannunta muryarta adabarbarce ta soma magana. "Aunty aneelerh zan fa a maki amma kada ki fa a ma kowa dan Allah," jinjina kai Aneelerh tayi"in sha Allah" Cigaba da yin magana tayi"dama akan decorating company dinmu ne, ban ta6a fa a maki cewa banawa bane, mallakin mamansu awata ne, Ni a lokacin dana kammala karatu ina neman aiki bansamu ba, Nayi ma daddy magana akan ya taimaka mini in bu e Beauty saloon nawa nakaina, amma sai yace min shi baida halin da zai Iya taimaka mani, bayan ni nasan yana da arzi in shi kawai baison bani ne kusan halin shi aya da mahboob in dai wurin ma one ko mami fama take yi dashi, dawowar ku gidan nan ne ma ya fara sakin hannunshi gudun kada ku gane halin shi,' Aneelerh ta natsu tana sauraranta. Numfasawa zahra tayi kafin taci gaba da cewa"akwai wata rana da naje gidansu awartawa, muna zaune a falo muna fira akan yadda zamu bu e beauty saloon da zamu gudanar da kasuwancin su, har take ce min mommynta tana da ku i sai dai itama ma one da ita ba ta Iya fidda ku i ta bata hakanan idan ba abun da ya shafi karatunta bane, amma da zata amince mana ko da bashine ta bamu idan muka samu ku i tun da kusuwancin ana samu sosai indai mutun ya samu kar6uwa awurin mutane, sai na zaro ido nace mata a'a ni bana so muci bashi muzo mu kasa biya, na fa i hakanne saboda sanin halin mahaifiyarta masifaffiyace bata da mutunci in dai akan ku in