Sashe 92
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai tana son ta haya a shi ne. Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta. "Mommy ba ki yi missing dina ba, shiyasa kike yi mini fa a, Kin barni ni ka ai agidan su, ni wlh gida zan dawo, ko dai kizo ki auke ni ko kuma in gudu in 6ace kamar Angel" maganarshi tayi matu ar bata dariya, cikin sigar lallashi tace"am sorry my baby boy, wlh nayi kewarka kamar zan zauce, yanzu dai ka yi ha uri kadaina kuka, Mommyn ka bata son zubar hawayen ka" Cikin shesshe ar kuka yace"ni dai kizo ki auke ni mommy, ko in gudu" hankalinta ya dan tashi, zuciya da sa e sa e saita dinga tunanin ko dai wani abu akayi mashi ne wanda ya 6ata mashi rai har yake neman dawowa gida. "Junaid, fa amin meya faru? Basa baka abinci ne? Ko ba ayi maka wanka ne? Ko wani ya buge ka ne"! A jere ta furta hakan. "Ni ba su yi min komai, ina cin abinci kuma mommy adama tana min wanka har sau biyu safe da dare, ni kawai ke nakeso kizo ki dauke ni, ko in gudu" ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta har ya an kwanta. "My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, zasu dawo mun da kai nan bada jimawa ba,' Rigima ya sanya mata"Allah in baki zo ba saina gudu" dariya ce ta kubce mata, jin sautin dariyarta ba aramin 6ata mashi rai ba. "Mommy dariya kike mini ko! Shikenan zan kashe wayar" da sauri tace"sorry nadaina, pls kada ka kashe min waya, Ina jin da in yin magana dakai, Yanzu fa a min a kwance kake ko a tsaye" "Saman gado" ya bata amsa atakaice, har ta bu e baki zatayi magana ya katse ta da cewa"Mommy, na tuna sunan mutumin nan da ya kira ki a waya, ran nan, amma ba zan fada maki ba, In kina son ji kizo nan" "Am sorry my baby boy, yakamata ka fahimce ni, babu yadda za'ai inzo, Zasu yi tsammanin ban yarda azu bane shiyasa na biyo ka, dan Allah ka fa a min sunan shi, ka ji yaron kirki" cikin agara da sonji tayi mashi maganar. "Toh mommy, zan fa a maki amma bana so kowa yaji har zahra" muryarshi da shagwa6a yake magana. "Junaid, Ni ka aice a akin, Zahra bata nan taje wurin aiki, Mahboob ma baya acikin gida, Abie da Uncle basu dawo gida ba, mami da ummi ne kuma basa a akin, suna a can palour suna fira" "To zan fa a maki, amma kada ki fa a ma zahra da mahboob" ta rasa ya za ta yi da shi, Ya i fa a mata sai jan maganar yake yi kamar baya son fadi. Kukan arya ta soma yi mashi tana fadin"dan Allah baby junaid dina ka fa amin, zuciyata zata iya bugawa idan ban ji ba" tuntsirewa yayi da dariya yana fadin"mommy wasa kike ba wani kuka ai na ganoki" gajiya tayi da tsayuwar, ta koma gefen gado ta zauna, tamkar tana agabanshi ta marairaice mashi fuska tana fadin"pls my baby boy, ka fa a min, komi ka ke so zan yi maka" "Zoben Angel, da ki ka ce zaki siya mini in bata tun da na maida ba mahboob nashi" "Kada ka damu, kafin ka dawo gida zan siya maka zoben, Nayi maka al awari, Yanzu fa a min toh" Sai da ya mula ya ishe iska tukunna Ya furta"wai ma...waima daddyn Unaisah, haka yace min fa" shiru tayi jimm tana tunanin sunan daya furta mata daddyn unaisa? Wanene daddyn unaisa? Ita kanta unaisan wacece ita!, sunan ya shige mata, jin tayi shiru yasa Baby junaid ambaton sunanta"mommy kin yi shiru baki ce komai ba" "Junaid, na ru e ne, na kasa gane wanene daddyn unaysa, amma shi mutumin Iya abun da ya fa a maka kenan"? "Eh, bai fa a min komai ba, Mommy ki kira shi ki ji toh wanene shi, ko daddyn Angel dina ne?" lokaci aya taji gabanta Ya fa i Jin Ya ambaci ila daddyn Angel ne, nan take walwarta ta tunano mata sunan wacece Unaisa, a sukwane ta mike tsaye Tana faman zare idanuwanta, zurfi tunani ta shiga duk duniyar nan mutun aya ta sani mai sunan daddyn unaisa, wato Tajuddeen, ta gaza yarda da abinda zuciyarta ke fa a mata. La66anta na kerma ta furta"ka tabbata haka sunan yake? Ko dai abakina ka ta6a jin na ambaci sunan daddyn Unaisa? "Mommy wlh dagaske nike maki haka yace min wai in fa a maki daddyn unaisa ne, mommy zan kashe wayar, ga mommy adama nan zata shigo dakin" kafin ta yi mashi magana yai rejecting kiran. Hakanan tadinga jin bugun zuciyarta na aruwa, jiki asanyaye ta koma gefen gadon ta zauna, tsawon mintuna zuciyarta nayi mata kokwanton maganar da junaid Ya fa a mata, har dai a arshe ta yanke shawarar cire nombar daga black list, don ta kira ta ji wanene mutumin da junaid ya fada mata cewa daddyn Unaisa ne, fatanta Allah yasa Dagaske ne hasashenta. Yatsun hannunta har kerma suke Yi wurin daddana wayar, bayan ta cire number daga black list, ta danna call cikin sa'a Kiran Ya shiga, wayar ta fara ringing, tsabar zumu i jikinta har kerma yake yi, Har kiran yayi rejecting ba'a aga ba, Mi ewa tayi tsaye ta zame dogon hijabin jikinta ta jefar saman mattress, safa da marwa ta cigaba da yi a tsakar akin, ta ru e wayarta a hannunta, a alla Ta Kira layin kusan sau biyar Yana ringing ba'a aga ba, Hankalinta ya i kwanciya burinta taji wanene mutumin nan daya kira kanshi da sunan daddyn Unaisah. Har ta fidda rai da za'a aga Kiran, Unexpected A kira Na shida data yi mashi sai gashi Anyi picking call din. Cikin rashin natsuwa ta furta"Assalamu alaikuma" maimakon ta ji muryar Namiji sai taji muryar matashiyar mace tana yi mata magana da wani yare. "Baiwar Allah, bana jin harshen da kike yi mini magana dashi, Idan kina jin hausa mu yi magana da shi" Ko da Aneelerh ta ambaci hakan, matashiyar sai ta canza harshenta zuwa Yaren hausa ta an koyo tace"wanene ke magana"? A agare Aneelerh tace"sunana Aneelerh, dalilin dayasa na kira Layin, kwanakin baya ana yawan kirana dashi, Ina tunanin ko wani ne ke nema, pls ina neman me wayar" ta fa i hakan ne don junaid ya fada mata cewa Namiji ne Ya daga kiran lokacin da aka kira. Matashiyar budurwar tace"Ni ce me wayar, wato irin kune ku ke bibiyar mazajen mu don ku wace mana su ko"? Sakin baki Aneelerh tayi jin abun da matar tace. "Kiyi ha uri, Nima matar aure ce kamar ke, kawai inason nasan ainihin wanene me wayar, ki taimaka min a agare nake da son ji" da alama matashiyar Yarinyar Akwai uruciya atattare da ita, tun daga kan kalamanta zaka shaida hakan. "Nace maki ni ce me wayar," atsawace ta furta hakan, Aneelerh tace"ba wayar ki bace, saboda ke da kanki ki ka ce irina ne masu bibiyar mazajan mutane don mu kwace masu miji, hakan na nufin ba wayarki bace wayar mijin ki ce" sautin dariyar matashiyar ne ya cika mata kunnuwanta, lamarin ya aure ma Aneelerh kai, gashi duk ta agara a matse take da son jin wanene. "Ke dai zan fa a maki gaskiya, tun da kin gano ni, ba wayata bace, wayar mijina ce, kuma baya nan Ya fita ni ka ai ce agidan" "Okey, pls Ko zan Iya sanin sunan mijin naki"? "A'a gaskiya, salon ki je ki kai ma boka sunan shi ayi maki asiri ki mallake shi" duk yadda Aneelerh ta kai ga jurewa saida ta fashe da dariya jin abun da Yarinyar tace, da yar ta sassauta da yin dariyar tace"wlh ni bana bin boka, Ko hanyar zuwa wurin shi bansani ba, Yar uwata ba duka aka taru aka zama aya ba, ni bana aya daga cikin matan dake zuwa wurin boka, saboda na dogara da Allah shi kadaine zai Iya biyamun bu atuna" matashiyar tace"Ni ban yarda dake ba, mata dayawa suna son wace mini mijina saboda kyakkyawa ne kuma yana da arfi" Aneelerh tace"baiwar Allah na fa a maki nima matar aurece, da mijina akan me zan nemi mijin ki"! "Oho nima bansani ba, idan kin gama magana zan kashe wayar" amsar data ba aneelerh kenan" Shiru aneelerh ta anyi tana tunanin hanyar da zata 6ullo mata, ta fahimci Yarinyar bata da cikakken Ilmi da wayau sai a hankali. Dabara ce ta fa o mata. Dariya ta fara saki, Matashiyar tace me kike yi ma dariya Aneeleh tace"Ai dole inyi dariya, ke yanzu baki gane muryata ba ne? Aneelerh fa ce matar abokin mijin ki Shu'aibu" Da bu ar bakin budurwar sai cewa tayi" arya kike yi aini mijina basu nan shi shu'aib ba, TAJ ne sunan shi, Kina son ki yi mini wayau ne" Jin ta ambaci sunan Taj Yasa Aneelerh Tsayawa cak ta dakata da yin tafiya, yayin da bugun zuciyarta ya aru, Muryarta na an rawa ta furta" arya kike yi, ba sunan mijin ki tajuddeen ba, so kike in yadda don kada ki fa a min ainihin sunanshi, ai ni nasani Shu'aibu ne sunan shi" Matashiyar budurwar tace"To kada Allah yasa ki yadda ma, kuma wlh ma arya kike yi mini cewa wai ke matar abokinsa ne baki da gaskiya," da alama ranta ya 6aci ta fara harzu Sassauta murya Aneelerh tayi"Ki yi ha uri, ba yadda ki ke tsammani bane, Dan Allah ki fa amin ina mijin naki yake inason yin magana dashi" Dogon tsoki matashiyar Taja, kafin ta furta"ba kin ce ke matar abokinsa bane? To ki ce ma shu'aibun Ya kawo ki gidan mu," kafin Aneelerh ta furta wani abu, Matashiyar ta katse kiran!" Hankalin ta Ya i kwanciya, Jiri ta soma gani acikin idanuwanta, a daddafe ta nufi gado, Ta haye ta kwanta, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta ta shiga ru ani, tun da Matashiyar ta ambaci sunan tajuddeen, natsuwarta tabar jikinta, taso ace tayi waya da shi don ta tabbatar da abun da take hasashe. Har ara jaraba kiran layin tayi amma matar ta agawa. Dubara ce ta fa o mata aranta, da sauri ta rubuta mashi sa o