Sashe 93
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin harshen turanci. _Idan ka karanta sa ona, dan Allah ka kira ni, Inason Yin magana da kai, sa o daga Aneelerh muhammad falgore_ Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kammala rubuta mashi sakon, Ta aura wayar saman side drawer, A gogon akin ta kalla arfe Uku na rana, kwanciya tayi saman gadon tana jiran tsammanin Kiran me wayar. ZEENATU A 6angaren zeenatu kuwa tun da ta fito da gudu daga akin Dr. Shureim ta koma akinta, ta fada saman gado taci gaba dayin kuka tamkar ranta zai fita, cikin muryar kuka take fadin"yaya shureim ba sona yake yi ba, wata yake so daban, dama nasani babu namijin da zai yarda yaso ni saboda rashin natsuwata," Idanuwanta sun ka a jawur, mi ewa tayi zaune ta soma cire lace jikinta a saman floor, ta watsar da kayan hada ribbon din da aka daure mata gashin kanta, iya undy ta bari a jikinta, ta jashi saman irjinta, tana huci yayin hawaye ke cigaba da wanke mata fuskarta, saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gaban dressing mirror dinta, cikin 6acin rai ta sanya hannu ta watsar da jerin turarurrukanta komai sai da ta wurgo shi asa, bayan ta gama ta koma gaban wardrobe dinta, aya bayan aya sai da ta wurga da suturar saman floor, hankalinta bai kwanta ba har saida ta maida akin kamar na mahaukata, tukunna ta koma saman gadon ta haye tare da jan bargo ta lullu6e zuciyarta na ta farfasa. Bayan Dr. Shureim ya fito daga wankan, kimtsa kanshi yai ciki shiga ta larabawa Ya feshe jikinsa da turare, Ya ru o wayar shi a hannun shi, tare da car key dinsa, walking quickly ya fito daga bedroom dinsa, Ya nufi akin zeenatu, duk inda Ya gifta a paloun masu aiki ne suke Yin aikace aikacen su cikin girmamawa suke gaishe da shi. "Yalla6ai barka da fitowa" muryar Tani ce ta katse mashi hanzarinsa, dakatawa yai da yin tafiyar ya juya ya dubeta "Yawwa barkanki, Ya aiki" fuskarta da fara'a ta amsa mashi"Lafiyalou Alhamdulillah," Har zai wuce ta Ya kuma tsayawa ya kalle ta" akin zeenatu nake nema" Da rawar Jiki ta ce"Yana a second floor, muje in nuna maka akin" ta fa a tare da yin gaba Yabi bayanta, Yayi matu agara da son ganinta, duk don Ya lallasheta akan laifin da yayi mata. Bayan sun hau elevator ta sauke su a second floor, Tani ta nuna mashi ofar akinta. "ki shiga ki fa a mata inason magana da ita" Tani ta amsa da toh, tana zura afarta akin zeenatu, gabanta Ya fa i ganin irin 6arnar da tayi, hankalin ta ba aramin tashi yai ba, jiki na rawa ta nufi gefen gadonta. "Zeenatu! Lafiya meke damunki ne? Meyasa kika hargitsa suturar ki"? Shiru zeenatu bata tanka mata ba, saima ara udundune kanta da take yi cikin bargo. "Dan Allah zeenatu kiyi mini magana, nasan 6ata maki rai akayi ki fada mini wanene" Jin tayi shiru ba ta yi mata magana ba yasa tace"ba zan takura maki ba, Yanzu ki tashi Yayan ki shureim Yana a ofar akin ki, shine yace in yi maki magana yana son ganinki" Kamar jira ta ke yi Tani ta ambaci sunan shureim, Cikin shesshe ar kuka tace"Tani, I don't want to see him. Please tell him I won't come. Yaya Shureim doesn't love me wata yake so daban, tun jiya yayi min al awarin zamu fita yawo atare, yau kuma da kanshi yace min inje in shirya kafin in dawo zai yi wanka ya shirya, Tani da naje akin shi babu abunda yayi, yana akwance saman gado yana kallon hoton girl friend dinsa a laptop...." da yar ta are maganar. Jikin Tani yai sanyi, duk sai taji ba da i, sai yanzu ta gane dalilin dayasa ta shiga halin da take aciki. "Kiyi ha uri zeenatu, ki tashi ki gyara jikinki, Yace yana son magana dake nasan yazo ne don ya baki ha uri, kuma naga ya shirya hada key din mota a hannunshi...." Katse ta Zeenatu tayi"Na fasa zuwa ki fa a mishi bazan je ba, tun da bayaso na" Cikin muryar ra a Tani tace"yana fa jin ki, bai kamata kina aga murya ba, sannan ke in banda abunki waya fada maki budurwashi ce yake kallo awayar? "Ai naga hoton da yake kallo, Yana a kwance saman gado ya rungumeta a kirjinsa" ta fada tana jan numfashi ta i fitowa daga bargon. "Zeenatu, kiyi mashi kyakkyawan zato, yaya shureim yana sonki fiye da yadda kike son shi, Ni shawarar da zan baki shine kada ki bari ya gane kina son shi, idan kika kwantar da hankalin ki da kan shi zai furta maki kalmar so" Sassauta muryarta tayi"Tani, zan iya jure wannan amma bazan Iya jure kallon hoton budurwarshi da Yake Yi ba," Dafe kai Tani tayi da hannu aya"zeenatu baki da tabbacin budurwashi ce, pls kibi komai a sannu zamu gano ainihin wacece Yake kallo awayarshi, Yanzu Ki tashi muje Yana awaje yana jiranki' "Tani ki daina wahalar da kanki, Nifa ba inda zanje, Ki fada mashi bana Jin da i bacci Nike Yi" Duk yadda Tani taso ta lallashe ta akan ta tashi ta je gare shi ta iya, a dole ta yaleta ta juya ta fuce daga akin. A tsaye ta same shi Ya jingina bayanshi jikin bango. Harya fara Gajiya da tsayuwa "Ka yi ha uri, Zeenatu tayi fushi bansan meya ha a ta dakai ba, nayi arin In lallasheta amma ta i amincewa ta amsa kiran ka, ban ji da i ba shureim, duk da bansan meya ha a ka da ita ba, amma bai kamata tun yanzu afara samun rashin jituwa a tsakaninka da anwarka, zeenatu tana da ha uri sai dai tana da zuciya idan aka 6ata mata rai' Tun da ta fara magana Ya natsu yana sauraronta, sai da ta kai karshen maganar tukunna yace"Inaso zan shiga ciki" bai jira amsar da Tani zata bashi ba yai saurin haura afarshi cikin akin zeenatu. Dafe kai tayi da hannu aya tunawa da 6arnar da zeenatu tayi a akin, gashi kuma Ya shiga hake zai je ya same shi kamar bola, can kuma ta ayyana aranta cewa an uwanta ne, daga haka ta ara gaba. A tsanake Yake bin ko'ina na akin da kallo, yayi mamakin ganin yadda ta hargitse komai, ta rikita mashi tunanin shi, Ya rasa gane fushin menene take yi da shi? Don shi a tunanin duk akan fitar da yace za su yi ne. Sam bai lura da lace din data cire ta jefar saman floor, idanuwanshi na akan gadonta, bargon da ta lullu6e dashi sai kerma yake kamar wadda sanyi ya kama. dadda amshin turarensa ne Ya daki hancinta, Nan take ta fahimci Ya shigo akin nata. Gefen gadonta ya zauna Yana dubanta, calmly ya furta"Zeenat ina son yin magana dake Shiru tayi bata tanka mashi ba, tayi tunanin Tani ta fada mashi cewa bacci take yi kamar yadda tace ta gaya mashi. "Nasan Kina Jina zeenatu, Ki amsa mini, nazo ne don in baki ha uri, nasan ban kyauta maki ba, Yanzu haka da nike yi maki magana na kammala shiryawa ke nake jira mu tafi" Cikin disasshiyar murya tace"yaya shureim bana jin da in jikina, bazan iya fita ba, sai dai zuwa gobe" "am sorry zeenatu, fushi kike yi da yayan naki? Ba za ki yi mini uziri ba? "Yaya shureim ni ba fushi nike yi dakai ba, fitarce na fasa, Bana jin da Ya rasa ya zai yi ya shawo kanta don ta amince su fita. Yanke shawarar Yaye Bargon Jikinta yai don ya samu damar lallashinta dakyau. Tsautsayine Yakai hannun shi saman bargonta, Ya ru o shi tare da jan shi, Ras yaji gabanshi ya fa i da sauri Ya maida mata bargon a jikinta, Yana faman jan numfashi da arfi da arfi, mi ewa yai da wani irin Yanayi ya nufi ofar fita daga akin Yayin da la66ansa ke ambaton sunan Allah, Har ya kusa kaiwa ofar akin Muryar zeenatu ta katse mashi hanzarin shi. "Yaya shureim kai da kanka ka fa a mini cewa baka ta6a yin soyayya ba, amma meyasa kake kallon hoton wata awayarka" Ta gaza ha ura har saida ta amayar masa da abunda ke cikinta, shi kuwa Man din duk ya rasa natsuwarshi, tunda Yaja bargonta Yayi arba da undy din jikinta shara shara Hakan ba aramin tada mashi hankalin shi yai ba, ga dukkan alamu ita batasan ma ya bu e bargon ba saboda ta udundune kanta, idanuwanta suna arufe. "Zeenatu, abun da na fa a maki da gaske ne, banyi maki arya ba, Ni ban ta6a yin soyayya ba" A hankali Ya an Juyo yana dubanta, a lokacin ta fiddo da kanta daga Cikin bargon, Yalwatacciyar sumar kanta, ta rufe mata gefen fuskarta, Jan bakin data shafa ya dame fuskar saboda kukan da tasha, har saman kumatunta jan bakin ne, duk da kwalliyar fuskarta ta 6aci ba aramin kyau tayi mashi ba. Muryarta da shagwa6a tace"ka fa amin wacece ka ke kallo awayarka? Idan ba budurwar ka bace. ayataccen murmushine Ya bayyana akan fuskarshi, sai yanzu ya gane dalilin dayasa take haukan nan, wato kishin shi take Yi saboda yana kallon hoton wata wayarshi, aranshi ya ayyana da ace tasan hoton wacece yake kallo da batayi haukan nan ba. "Zeenatu, dama saboda hoton wayata kike kuka"? aga mashi kai tayi alamar eh. "Okey, Ki kwantar da hankalin ki, ba budurwata ba ce," ma e mashi kafa a tayi"ni ban yadda ba yaya shureim, idan har dagaske kake yi min ba budurwan ka bace to ka nuna min hoton in gani" Lumshe idonshi ya anyi tare da waresu kan fuskarka, duk da tazarar dake a tsakanin su, ba aramin Kyau take yi mashi ba musamman yanzu daya fahimci irin zazzafan son da take yi mashi. Ganin ya tsareta da ido, ba tare daya furta komai ba yasa tace"Yaya shureim magana fa nake yi maka, kayi shiru baka ce komai ba, Ni dama nasani baza ka nuna min hoton in gani ba" Yadda take yin maganar tana jujjuya eyes balls dinta ne suka ara rikitar da shi. Gyaran murya ya anyi kafin yace"Idan har Ki ka amince zaki shirya mu fita, Ni kuma zan nuna maki wacece