← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 106

Sashe 10

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi don tasan itama zata dawo kanta ne idon ta gama dasu Deeja gani ta ke kamar an uwan su sun mutu saboda wasu daga Cikinsu babu numfashi atattare dasu Musamman jemimah da Azeza zaiyi wuya su rayu. zafreen ta gama kashe masu rayuwarsu ta wulakanta su kamar dabbobi. A haukace Batul ta nufi table in da ke auke da Tunkunyar shayin nan ta ago shi da hannu biyu, tana haki ta nufi tsohuwa zafreen da ta du ufa asaman su Rubina, ta daddage ta buga mata shi, Ko gizau batayi ba, Komawa ta yi tare da auko kujerar table in ta dawo ta kuma buga mata ita saman kanta, still bata ago ba. A fujajan ta koma cikin akin tana neman abunda zata wala mata, Duk ta bi ta haukace sai waige waige ta ke yi fuskarta sharkaf da hawaye, har zata juya ta wutsiyar idonta ta hango Rigar wu a da ke a so ke a tsakanin littattafan cikin Book shelves akin. Tsohuwar ajiye ce wu ar da tsohuwa Tamira ta ba Danish Kyautarta a lokacin da ya bu aci yana son datse sumar kan shi, ashe ya maida mata ita shiyasa ko lokacin da Angel ta yi mashi magiya akan ya bata wu ar Ya i bata saboda bata atare da shi, da gudu Batul ta nufi book shelves din ta zura hannu ta auko rigar wukar ta zaro ta Jikinta har sal i ya ke yi saboda tsabar kaifinta, wu ar sihiri ce mai ha arin gaske, Cikin zafin nama ta watsa aguje bata nufi ko'ina ba sai kan Tsohuwa Zafreen a lokacin ta gama da su Rubina juyowar da za ta yi ke da wuya Batul ta daddage ta Luma mata wu ar Cikin idonta, kafin ta yi wani yun urin yin amfani da sihirinta Batul ta ja wu ar Tun daga kan idonta har zuwa saman wuyanta ta tsartsarga mata Jikinta, Wani irin arfine yazo mata, Dama jinin ta akan akaifa ya ke, Zuciyar ta bushe, Gaba aya tsohuwa zafreen ta gigice saboda azabar zafin da taji na shigar wu ar, Ta yi arin Buge Batul sai dai Allah bai bata Ikon Yin hakan ba, ba aramin Illah Batul ta yi mata ba, Sai dai duk da haka wani abun mamaki babu igon Jini da ya fito daga idonta, duk inda Batul ta fasa mata da wu ar kamar ana inke fatar wurin haka ta dinga ha ewa tamkar ba'a ta6a tsaga ta ba. So ta ke ta lalubo sandar hannunta saboda arfin sihirinta yana a jikin sandar, Idan har babu ita Sauran sihirin da ke a jikinta ba lallai Ya iya yi mata tasiri ba, Da yar ta samu ta yi wurgi da Batul gefe aya gaba aya ta kife asa kanta ya daku, wu ar hannunta ta kufce mata, yun urawa zafreen ta yi tare da mi ewa tsaye Jikinta na kakarwa ta soma tafiya tana tunkararta, so ta ke kawai ta kashe ta har Lahira, Cikin fitar hayyaci Batul ta mi e zaune daga kwancen da ta ke a asa, Ja da baya ta dinga Yi har sai da ta urewa bango. Tuni tsohuwa zafreen ta cimmata, tafin afarta ta aura saman Yatsun hannun Batul ta murjesu, tsabar ra in da Batul ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin ku ka na fitar hayyaci, wata irin zufa ta soma tsasstafo mata "Kafin ki kashe Ni, Ni zan fara kashe ki, Dabba kawai, Kin yi kuskure da ki ka soka mini wu a A cikin idona, Angaya maki cewa Ni Mutunce da zan mutu farat aya? Tana huci ta yi tambayar, janye tafin afarta tayi daga kan yatsun hannun Batul ta aura afar saman jikinta da arfi ta danna shi tare da murza afar, Jini ne ya soma gangarowa ta cikin bakin batul Nan ta ke Numfashinta ya soma kokawar aukewa..... Ba zato ba tsammani tsohuwa Zafreen Taji an buge mata kanta da arfi gaba aya ta kife asa, ta baya aka shammace ta, A hanzar ce ta ago don ta ga wanene, a matu ar ru e ta ke kallon fuskarta, Ba kowa bace face TSOHUWA TAMIRA. "Ban yi mamakin ganin ki ba Dama na jima da zargin cewa ba ki atare damu Tamira!" zafreen ce tayi maganar muryarta akausashe, saboda tsabar 6acin rai facial musles din tsohuwa tamira har kerma su ke yi, Hankalinta yai matu ar tashi ganin yadda zafreen ta lalata rayuwar Yaran da ta raina gaba aya ta gama da rayuwarsu, ta yi danasanin zuwan da ta yi amakare da duk hakan bata faru ba, idanuwanta sun yi jawur dasu tamkar garwashin wuta, wani irin hu ci ta ke futarwa urawa tsohuwa zafreen ta yi tare da mi ewa tsaye, Ido cikin ido su ke kallon juna babu sassauci akan fuskokin kowannan su. "Ni dama ba ki ta6a burgeni ba, Muguwa azzaluma ba ar kafura, Ban ta6a ganin dabba Jahila da iya irin ki ba, Wai ke baki da hankali ne? Ke fa mutunce wa annan yaran da kika lalata rayuwar su mutanene fa ba dabbo bi ba, Laifin me su ka yi maki da har su ka cancanci wannan hukuncin daga gare ki"? Rai amutu ar 6ace ta jefa mata tambayar. aure fuska tsohuwa zafreen Ta yi, idanuwanta sun ka a jawur dasu, Babu ko alamun imani akan fuskarta Tana magana tana huci kamar mayun waciyar zakanya" Ni kike gayawa magana? Ka da ki manta ke bakowa bace a gidan kurkukun nan face antacciya mai rainon Yara, dole Ki yi mini biyayya saboda ni ke agaba da ke, Nafi arfin ki Tamira nesa ba kusa ba, Idan har kina son ki tsira da ranki to ki gaggauta barin wajen nan tunkafin In yi maki mummunar Ill......"Bata kai ga arasa maganar ba, tsohuwa Tamira ta daka mata tsawa har saida ta furgita, karo na farko kenan da taga Rashin tsoro acikin idon Tamira. Nuna ta ta yi da yatsan hannunta"ko da can baya da na ke girmamaki ba dan ina jin tsoron ki bane sai don udirin da na ke dashi na son Rushe Ba in tarihin da kuka kafa, Ajali ne ke kiran ki shiyasa har ki ka yi gigin shigowa cikin akina, A yau inaso in nuna maki arfin ikon da na ke shi wanda na samu awurin rainon yaran da nake yi, Zafreen Yau zaki yaba ma aya za inta, Ko da zan rasa raina ne saina fara ganin bayanki wula antacciya kawai"a fusace ta ambaci hakan idonta akan fuskar zafreen ga dukkan alamu mamaki da al'jabi ne ya hana ta mayarwa Tamira martanin maganarta. bata ta6a tsammanin tsohuwa Tamira zata Iya yada mata magana ba tare da jin shakkarta ba. "Tsautsayi da addara ne suka jefo wa annan Watsastsun afafuwan naki cikin aki na, Kin ga babu mai kallon mu bare aji sautin mu, Yau zan huce haushina akan ki...." Tunkan ta arasa maganarta, tsohuwa Zafreen ta 6ace ma ganinta, Hankalin tsohuwa Tamira Ba aramin tashi yai ba, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada ace ta bar akin, In kuwa haka ta faru zasu fuskanci azabtarwa domin kuwa za ta je ne ta fallasa su. Jin motsin mutun abayanta yasa ta yi saurin Juyawa, Har saida gabanta Ya an fa i ganin tsohuwa Zafreen ta bayyana cikin shigar jajayen kayanta hannunta ru e da sandarta, ashe 6acewar da ta yi don ta auko sandar hannunta ne ta kuma mayar da suturarta. "Na yi tsammanin kin ji tsoro kin gudu ne"; acewar tsohuwa Tamira Mahaukaciyar dariya zafreen Ta saki tare da cewa"Babu tsoro a cikin zuciyar tsohuwa Zafreen! Tamira kin shiga Uku! Kin tsokanowa kanki Bala'e da masifar da ba za ki Iya jurarsu ba, Zan kashe ki har lahira bayan na gama da ke zan arasa kashe wa anda basu mutu ba a cikin Yaran can naki, Zan sha Jinin su In ci tsokar naman su" Tana kai arshen maganar ta, ta yi kukan kura tare da Afkawa tsohuwa Tamira, gaba da gabanta Aljani Ya taka wuta, Domin kuwa Zafreen tafi Tamira arfin sihiri, Fa ane ya kaure a tsakanin su kamar dawakai, ba ka iya jin komai sai sautin buge bugen su da gurnaninsu uwa namun dawa, ura ta kara e cikin a ki, Kusan atare su ka canza suffofin su, Tsohuwa Zafreen ta riki a ta koma Damusa, Tamira ta koma kura, Ko a namun dawa Damusa ba abokiyar karawar Kura bace, Fa an nasu Ya canza salo, kamar a filin daga su ka cigaba da kaima junan su Hari duk suka raunata kawunan su. *ANGEL* Tsawon lokaci tana a sume saman Gadon da aka kwantar da ita, fatar jikinta jawur da Jinin da su ka yi mata wanka dashi duk ya daskare mata, zai yi wuya yabar Jikinta, saukar ruwan sanyin da ta ji ajikinta ne ya farkar da ita a firguce ta farka, sai dai ta kasa bu e idanuwanta saboda nauyin dasu ka yi mata, hatta bakinta Ya i bu uwa la66anta sun kumbura suntum wani irin zogin azaba su ke yi mata. Ba zato ba tsammani kunnuwanta su ka jiyo mata muryar SALSABEEL. "Meyasa ki ka yi gaggawa? Kin manta me na fa a ma ki? Sai da nace ku yi takatsantsan idan ba haka ba za ku ja ma kan ku ne damu kan mu...." Sam ta asa motsa bakinta, Idanuwanta ka ai ta iya samun damar bu e su akan jikin shi, Yana atsaye Cikin shigar Giant ko'ina na jikin shi arufe kamar yarda ta ganshi a shekaran Jiya. Ta yi mamaki sosai saboda a tattaunar da su ka yi da ita ya fa a mata cewa ba zata sa ke ganin shi ba, sai ga shi Ya dawo yau, hakan ya tabbatar mata da cewa suna acikin ha ari gaba ayan su, taja masu bala'e. Rushewa ta yi da matsancin kuka raunin da ke abakinta yaci gaba da fitar da jini Tsananin tausayin ta ne Ya kama shi, ganin yadda suka raunata Jikinta sun gur6ata mata tsaftatacciyar fatarta, tsabar takaici da danasanin gaggawar da ta yi ne yasa ta yin kukan, tana so ta yi ma shi magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta ya i fita ko da tana yin kukan babu sauti. "Ban fa i hakan don
Chapter 10 · 0% Book details