Sashe 67
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
maganar yana kallon fuskar dr laura Major yace"why not bazamu dam a amanar kula da yaran a hannun UMMIN AMERICA ba? Tun da itama ar Asalin asar Nigeria ce, hatta yaren da naji Yaran suna magana da shi itama tana jin shi sosai" Jin Major Ya ambaci sunan Ummin america yasa Dr Mark da dr brown Kallon Juna ga dukkan alamu sun girgiza da jin an ambaci sunanta, Dr laura ta zaro ido tana fa in" The Baddest mistress? There's no way we can leave the children in her care, She's a dangerous woman. How could she possibly know how to take care of them?" hankalinta bai kwanta da zancen mi a yaran ga Ummin america ba saboda sanin wacece Ita. Bayan ta are magana Major yace"Ai ba yau tafara Yi mana aiki ba, tana taimaka mana sosai akan irin case in nan, Ina da tabbacin zata Iya! Fiye da yadda baki tsammani"Kwa6e fuska Dr laura Tayi don ita har aranta Fargabar Ummin americe take ji, Kowa yasanta sananna ce a 6angare Iya karuwanci tantiriyar ar bariki ce, tayi aurin suna america shiyasa su ke yi mata la abi da Ummin america, tsabar Iya shai ancinta har award ake bata akan Iya Karuwanci. "Mu zatayi ma aiki, bai shafi sana'arta ba, Kawai munaso Yaran su kace a hannunta amatsayin guardian insu, Kafin Mu dam a mata su zamu yi yarjejeniya da ita idan har ta amince to lafiyalou ba zamu samu matsala da ita ba" ta6e baki dr Laura tayi"amma dai ba'a asibitin mu za'a gayyato mana ita ba, Don ina jin fargabar ta rikitar mana da ma'aikatan mu da surar jikinta" Gaba aya suka sanya dariya jin abunda tace, ta fa i hakanne don tasan Ummin America kamar magana isu take awurin Iya jan hankalin mutun da surar Jikinta, Dirine da ita na bala'e' Sunjima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani Commender yace "Dr mun gode sosai da shawarar ki, Zamu koma bakin aiki Yanzu, Idan har Chief din isod Ya amince da bu atar mu zamu tuntube ku" Daga haka Sojojin sukayi Ma Dr laura sallama, Har bakin parking space na asibitin ta rakosu, Bayan tafiyar sojojin suka dawo Cikin asibitin. _~*BossLadiesWriters*~_ _*KURKUKUN ADDARA*_ ~Middle step~