Sashe 30
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
s uniform launin farare, wararru ne a 6angaren girke girke da gyaran gida, basu wasa da aikin su, Suna ba lokacin mahimmancin sa, kuma suna takatsantsan wurin kula da bu atun mutanan gidan. A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen in gidan mai girman gaske, A sha e ya ke da kayan Amfani, ko ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba, aiki su ke yi tu uri babu kama hannun yaro, Matasan an mata da manyan su, wasu suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board, yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka aura, akwai wa anda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki. amshin girkinsu ya kara e ko ina tun daga cikin kitchen in har izuwa Babban falon gidan. Babbar macace ta shigo kitchen in domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke gudana, A alla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance aya daga cikin Masu yi masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma aikatan Cikin gidan, Macace mai yawan fara a ga son mutane, ma abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka pakistan ne a jikinta riga da wando farare al anyi masu adon duwatsu launi daban daban, afarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA* ba indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen in masu aikin suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ara dage damtse suna aiki duk don su ku6uta daga fa anta. A hankali ta ke zagaye Kitchen in, Hannayenta a goye saman irjinta, aya bayan aya take binsu da kallo, na an wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan atare su ka ago suna kallonta, Hannu ta tafa masu Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells delious, i m sure anon girkin zaiyi da i kamar yadda amshinsa ya ke da da in sha a, Ina ara jinjina ma ku, ta arasa yi masu maganar tare da aga masu babban yatsan hannunta na dama alamar Jinjina. Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba aramin da i suke ji ba, Idan hajjati ta yabe su, suna matu ar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da unta. Dame dame aka kammala ne ? ta yi tambayar tana kallon faces insu, Abla ce ta soma Yi mata jawabi Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes, kusan abu goma ta lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta anyi kafin ta aura da cewa Kada na katse maku aikin ku, lokaci Yana urewa, Ku hanzata ku kammala, An aikawa Hajiya saratu Breakfast inta! ? da sauri Safa tace yanzu nake shirin zuwa in kai mata, Nice nike duty part inta Gya a kai Hajjaty ta yi. Okey, shirya min fresh fruit ki ha a min da kakkauran tea, Wadda aka kira da Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari a cikin ayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta mi a mata hannu biyu tasa ta kar6i tray din tare da juyawa ta fuce. Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu Safa ashe ke ce kike duty a part in Aunty jarabatu zaki sha Masifa, Abla ce tai mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na gutsiri afar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata guba acikin abinci donta ci ta mutu, dariya suka saka Tana da wuyar sha ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu sophia ce tai maganar, Safa tace Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati siddan, shiyasa a kullum nake ro on Allah ya bani bugun zuciyar family in, Wlh idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya dawwamar da auran mu don nasan ma iya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata aukar raini batason Mu amala da bare tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau saida takai aya tukunna Abla tace you don t ave sense, Dama najima da zargin kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi arfinki, Ni kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi arfinka ka ha a shi da baka so kwa6e fuska Safa tai kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ar aiki ta auri an masu gida, wani sa in ma mai gidan ta ke aurewa sautin dariyarsu ne Ya hana ta arasa maganar, suna fira suna aiki, Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai ku i sai ar mai ku i, talaka sai an talaka, Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a arshe ki are a emergency room Dariya suka saki gaba ayan su, kwata kwata firar da suke yi bata auke masu hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun fa i abunda ya basu dariya su an murmusa. Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu Abla ce tai maganar. Abla tace Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa basa son haihuwa, daga mai a biyu sai mai a uku, Allah ya hore masu wadatar arzi i sai a ne zasu gagare su? Abun na ona mun rai, komai nasu na rayuwar turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan an watanni zamu dinga sakar masu a tuni zamu cika famiy Maganar Abla ba aramin dariya ta basu ba, Sofiya tace Sannu kaza suma ai suna son an, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, addarar su ce ta zo masu ahaka, naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu da ewa a gidan, Suna haihuwa amma an basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar a Namiji ba, shi da matarshi Gimbiya mujeedat, a biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba aramin gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arzi i a family insu daga shi sai sharafudeen, mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu wa anda basu da e da fara aiki ba Abun da aure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun kaka da kakanni aya, Tun daga asa Nigeria har zuwa asashen waje an bincika lafiyar kowan nan su, Ba su da wata matsala da ta shafi wayoyin haihuwarsu, lafiyar su alau, har manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a zuri arshi, Sakamakon aya ne dana asibiti, basu da wata lalura, Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su. Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya, Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah murya asanyaye Safa Tayi maganar. Abla tace Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu a, akan Allah ya yaye masu lalurar da ke damun su shiru suka anyi Na wani lokaci, daga bisani Safa ta shirya Kayan breakfast in Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su, Bayan fitarta daga Cikin kitchen in su ka aura da wata firar, sam basa gajiya da firar Familyn Obinna. Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za ae shagali na kece raini, za a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan an Obinna da Jikokinshi wa anda basa a asar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta Fuskar Sophia auke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace Anya ko Owais zai zo? Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin jikokinsa yafi aunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba, acewar Abla Murmushi Sopy tayi t wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min wankin ido, don na samu damar are Mashi kallo Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya aga ido ya kalle shi ba, Sannan ba a katse shi, Sau in shi aya Idan har kika karanci halayanshi da unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sau in kai baida girman kai, Yana da tausayi ga taimakon na asa dashi tun da ta fara jera masu Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline in dake a bakin ofar fita kitchen in ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce ta je ta auki landline in Ta aga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama, Jikinta sai 6ari yake yi. Cofee Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren in Tayi Hankalinsu gaba aya ya dawo