← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 106

Sashe 45

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maki magiya ya dinga yi mata da yar ya samu Ana ta zuba mashi abinci kala Biyar ta aura masa saman dinner table na kitchen Yana ci yana santi, Musamman da ya zo kan Farfesun ganda, duk ya bi ya susuce hada si ar hannu kamar an maro Bayan kammala sallar isha i tun akan hanyar dawowa daga masallaci Uncle abdallah yace da abie Yana so zasu wuce idan sun koma, abie yace ba zai yiwu ba, dama ba kwana zasuyi ba? uncle an Iya da ke atare da su Yace Yaya ka yale shi, sai mu ga ta ofar da zai fita, Dama Hajiyar shi na cikin gidan dole shima Ya shiga, Haba Abdallah yanzu ku kwaso uwargajiya sannan ka ce zaku tafi? A wani masauki zaku sauka ne da yafi namu? Uncle abdallah yace A hotel ne zamu sauka ya 6oye masu cewa sunyi gida a abuja, Uncle an Iya na jin haka yace ai da ku in hotel in da zaka bayar wara ka dun ule su ka bani sai ku kwana a gidanmu dan na fahimci ku in ne su ka yi maka yawa dariya suka saki gaba ayansu suna tafiya suna Yin fira gwanin ban sha awa, Bayan komawarsu gidan uncle adallah da abie suka nufi aki atare. Hajiya adama na akwance saman gadonta, Har ta canza kayan jikinta daga Lace zuwa Rigar bacci, da har ta yi shirin tafiya tana jiran uncle abdallah ya dawo su tafi, sai ga mami ta shigo akin, ganin tana shirye shiryen tafiya yasa ta ce da ita ina zuwa tace ae zasu sauka a hotel ne, girgiza kai mami ta yi ki ma daina fa in hakan don ba zai yiwu ba, ga gida kuma sai ku ce zaku kwana a hotel? Hajiya adama tace bamu son mu aura maku nauyi ne, mami tace babu wani nauyi wlh, idan ma kina tunanin ko dan saboda gidan aninsa ne, to ki kwantar da hankalin ki, gidansu ne su biyu, kusan ma rabi da kwata na abunda aka kashe a ginin da ku in abie ne, Allah ne bai nufa zamu dawo nan in ba, sai daga Baya da ya samu arin matsayi awurin aiki kin ji yadda akai muke zaune agidan, na fa a maki ne don ki kwantar da hankalin ki, idan da kara ae gidan surukai gidan an uwana ne tun da anzama aya, Ga an jikanmu junaid ya ara mana dan on zumunci maganar Mami ce tasa hajiya adama fasa shirin tafiyar, mami bata jima da fita daga akin ba Kiran uncle abdallah Ya shigo wayarta, ko da ta aga kiran sanar da ita yai game da fasa tafiyar su sai zuwa gobe, hankalin ta ya ara kwanciya, ba tare da 6ata lokaci ba ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, tana shirin kwanciya, muryar Aneelerh daga waje ta katse ta, sallama tayi mata, hajiya adama ta amsa mata da wa alaikum salam, Suruka ta gari shigo ciki mana cikin Jin kunya Aneelerh ta turo ofar akin hannunta auke da baby junaid, saukowa yai daga jikinta da gudu ya nufi hajiya adama tana dariya ta auke shi kafin ta zauna gefen gadon tana shafa sumar kanshi, ganin Aneelerh na arin zama daga asa yasa ta katse ta da cewa ki Zaune gefe na, Muyi fira komawa gefen gadon aneelerh tayi Mommy barka da dare, Ya gajiyar tafiya Hajiya adama tace ai Gajiya tabi jiki tun da na ga jikana shiru suka anyi kafin Hajiya adama ta ce Ya ha urin rashin da mu ka yi ? Du ar da kai Aneelerh ta anyi, a duk lokacin da aka yi mata maganar 6acewar su tajudden tamkar an fama mata mikin dake acikin zuciyarta ne, nan take hawaye suka cika idonta, Muryarta na an uwa ta furta uri an gode Allah, muna ta binsu da addu Ko akwai wani abu da ku ke shiryawa ne game da 6acewarsu ? Jinjina kai Aneelerh tayi Eh mommy, dama na jira ne sai kun huta mu yi magana gaba aya Aneelerh ta kwashe komai dangane da tada zancen 6acewar su Uzair ta labarta mata, annurin da ta gani akan fuskar Hajiya adama ne Ya tabbatar mata da zata samu goyon bayanta, Kunyi tunani mai kyau surukata, Naji da in shawarar da zahra ta baki, Yarinyar tana da hankali, duk cikinmu babu wanda yai tunanin tada zancen, idan har akaci nasara silar shawarar da ta bada, Na yi mata al awarin kyauta ta musamman Ba aramin da i Aneelerh ta ji ba, Mommy adama ta aura da cewa In sha Allah zamuyi magana dashi abdallahn dangane da tada zancen, sannan zamu bada tamu gudummuwar, fatana Allah ya dafa mana, Ya dube mu da idon Rahma, Ya bayyanar mana da su idan suna a raye, ko da basa a raye da bu atar muji meya faru da su ! Cikin girmamawa aneeleeh tace In sha Allah zamuyi nasara mommy, saboda bana son in rasa surukai na gari irin ku Sam batasan Ta furta hakan ba, Dariya Hajiya adama ta yi Nima ai bana so na rasa suruka ta gari irin ki Aneelerh, domin kuwa zai yi wuya asamu tamkar ki, cikin jin kunya aneelerh ta mi e tana fa Bari na kawo maki abun sha bata jira amsarta ba, ta yi saurin Juyawa ta fuce daga akin, Bayan fitarta Hajiya adama ta dubi Baby junaid dake kwance saman irjinta, Ya tsareta da ido, tun da suka fara magana bai tanka masu ba, ya kasa kunne yana sauraronsu, sai yanzu ya samu damar yi mata magana Granny kinsan Angel jinjina mashi kai tayi nasanta mana, Inason Angel sosai marairaice mata fuska yai tamkar zaiyi kuka baiwar Allah Angela ina, Mommy ta fa a min da ita da daddynta da daddyna sun 6ace, ni tsorona ma kada ace 6era ne ya cinye su ba Zaro ido Hajiya adama tayi can kuma sai ta tuntsire da dariya Granny, mommyna kusan kullum sai ta yi kuka saboda su angel, ar baiwar Allah, mami ta hanata Yin kuka amma bata Jin maganarta, sai da nayi mata fa a, na nuna mata raina ya 6aci tukunna ta daina sosai hajiya adama ke yin dariya, Sambatu iri iri junaid ke yi mata ba aramin nisha i ya ke sanyata ba, Gobe akwai school junaid, mu kwanta mu yi bacci e mata kafa a yai Ina tsaraba na Nayi maka amma sai gobe zan baka, nafi so ka huta yanzu muyi bacci amsa mata yai da toh mu jira mommy ta kawo mana abun sha ko? in mun sha sai mu kwanta, Turo ofar akin Aneelerh tayi hannunta auke da cup of coffee asaman table ta ajiye mata shi, Godiya hajiya adama tayi mata, daga nan su ka yi sallama da junansu Aneelerh ta fuce, Atare da junaid suka sha coffee in Bayan sun kammala, Hajiya adama Ta kwantar dashi ta tottofe shi da addu a, sauka tai daga saman gadon ta nufi switch ta kashe hasken akin, kafin ta dawo ta hau gadon ta rungume jikallanta a irji, ahaka bacci ya auke su ****JOS CITY MUN WAYI GARI LAFIYA AGIDAN ALHAJI UBAID******* zazzaune suke a saman dining suna Yin breakfast A tsanake shiru baka jin sautin komai saina cokulansu, kwas kwakwas kamar zasu fasa plates in, sun natsu suna tura abinci a cukunnansu, Alhaji ubaid na sanye da Jallabiya Hajiya Laila dake agefensa arab gown ce a jikinta launin royal blue ansha uban make up, Alhaji musa ya auki wankan tsadaddun suit sun zauna mashi, mutumin fa akwai kyau kamar shi ya tsara kanshi ya iya aukar wanka ga aji, daga gefen shi Dr shureim ne cikin shigarshi ta gado wato Kayan larabawa, dadda amshin turarensu mai da in sha a, musamman turaren Alhaji musa fragrance insa na dabanne. A hankali ya ago yana duban shureim ya lura ba abincin ya ke ci ba, tun da suka zauna yake ta faman jujjuya spoon in hannun shi acikin plate in gabanshi, gyaran muryar da Alhaji musa yai mashi ce tasa shi agowa ya kalle shi Cikin kulawa ya ke yi mashi magana meyasa bakasan cin abinci shureim? Na lura tun shekaran Jiya da nazo gidan nan baka ci wani abun kirki ba Hajiya Laila ta an dakata da cin abincin fuskarta a yamutse take kallon alhaji musa aranta tace ji wani ikon Allah ko ina ruwanshi da cin shi da shan shi? Ni narasa gane shisshigin nan da yake yiwa shureim, mutumin da bai damu da shi ba, sai yanzu ne yasan da zaman shi Cikin sanyin murya shureim ya kalli uncle in nashi ina ci mana, kawai ni nafi sha awar abincin hausawa ne wannan baya min da i abaki Alhajin ubaid yace Meyasa tuntuni baka yiwa zainab magana ta girka maka ba? Kamar ba ka da bakin magana, komai naka ya zama na shiririta shureim so ka ke ka koma yaro ? shiru shureim yai shi kanshi haushin rashin warin gwiwarshi yake ji, ya koma kamar wani sakarai komai sai yadda akayi da shi. Kada ka damu Yayana, da zarar mun koma abuja zai dawo asalin Dr shureim in da ka sani ne, Kasan matata ta iya bada tarbiya zata gyara maka anka ya zama namijin gaske Wannan maganar ta Alhaji musa tayi matu ona ran Hajiya layla, har dai tagaza jurewa Me kake nufi? Ni ban iya bada tarbiya ba kome ? Ko kallo bata ishe shi ba saima Ya auki glass in lemu mai sanyi yakai baki Yana kur6a. Haba layla, meyasa bakya iya 6oye fushin ki ne? Laifine don ya yabi matarshi? Harara ta wurgawa Alhaji ubaid tamkar wayar idon zata fa o kasa bansan meyasa kake goya mashi baya ba, idonka ya rufe kwata kwata baka ganin laifin shi, wannan ba adalci bane rai a6ace ta arasa maganar tare da buga table din, A fusace ta mi e tabar dining ewa shureim yai da niyar yabi bayanta da sauri Alhaji ubaid ya dakatar dashi dawo ka zauna komawa yai ya zauna daddy bana jin da in hakan, kasan halina tunfil azal bana so inga ran wani daga cikin ku ya 6aci Shureim ne yai maganar ka kwantar da hankalinka, In sha Allah zan sasanta tsakaninsu, Yanzu zan shiga wurinta in lallasheta Yai maganar tare da
Chapter 45 · 0% Book details