Sashe 66
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
farar fata ne acikin su? a iya sanina ba ar fatane mutanan Nigeria, Sannan matansu kuma basu da dogon gashi, kuma Launin idonki Kalar na mutanan asarmu ne" Dr. Mark jockson ne Yai maganar da alamun mamaki akan face insa Dr. Laura na murmushi ta dube sa"kada ka bani kunya mana, ko mu a asarmu ai akwai black americans, zai Iya yiwuwa suma suna da ala a da fararen fata ne ina nufin half cast" "Dagaske Ku an Nigeria ne? Jinjina masa kai tayi"Eh, ai yaren da muke yin magana dashi hausa ne na nigeria, zaku Iya bincikawa" Ba aramin mamaki suka yi ba, Hatta turancin da yaran suke magana da shi sak Na america ne bana Nigeria ba. "Yanzu dai bazaki fa a mana gaskiyar abunda ya faru da ku ba ko! To Shi an uwan naki da kika ce yasan komai tayaya zamu Iya farkar da shi daga bacci"! Anzo dai dai wurin da tafi so, marairaice masu fuska ta yi"maganinshi Yana a nigeria, dan Allah ku taimaka ku maida mu asarmu, idan ba haka ba an uwanmu zai Iya mutuwa" hada wallarta "Meke damun shi ne" Dr Brown ne yai mata tambayar, batare da ta yanke shawara da zuciyarta ba tace"nima bansani ba, Idan yafara bacci yana aukar tsawon lokaci bai farka ba, to akwai maganin shi kuma yana acan asar" Murmushi kowannansu ya saki, hakan yasa tasha jinin jikinta, Commender yace"Kin Iya acting, da farko kince bazaki Iya tuna komai daya faru a rayuwarku ba, amma ayanzu kin fa i inda za'a samu maganin an uwanki hakan na nufin tunaninki yana nan baki manta komai ba ko"? aure mata fuska yai "Zaki fa a mana gaskiya ne? Ko kuwa kunfi so mu je dake can headquater Ki amsa mana tambayoyinmu ta tsiya" tashin hankalin da ba'a sanya mashi date Maganar commender tayi matu ar tsoratar da ita Jikinta Ya hau yin kakarwa duk tabi ta rikice, A arshe data ga dagaske zasu titsayeta saita amsa masu tambayoyi ko su tafi da ita headquater, aiko da arfi tasa wata irin gigitacciyar ara data firgitar dasu, Hannayenta Biyu ta sanya ta daddafe kanta tana fa in"Nace maku ni bansan komai ba! Dan Allah ku maidamu asarmu Nigeria, an uwana zai Iya rasa ranshi, Na ro e ku idan har dagaske zaku taimaki rayuwarmu to ku maidamu Nigeria wurin danginmu," kamar mahaukaciya haka tadinga nanata masu akan su maidasu Nigeria. Hankalinsu Ba aramin tashi yai ba, ganin yadda wayar idanuwanta suka burkice Launin Ciki Ya 6ace sai zallar farin idon, Jijiyoyin wuyanta dana Gaban goshinta shatunsu ya fito ru u ru u, Jefar da robar fanta hannunta asa ta yi, a zafafe Ta mi e saman gadon kamar ar daba, ta dun ule hannayenta, taci gaba da ambaton Ku rabu dani ku yaleni, Ku maida mu asar mu Nigeria nace ku kaimu asar mu, can muke son zuwa" Har suna ha a baki wurin lallashinta"sorry ki kwantar da hankalin ki, zamu tafi yanzu, Ki daina kuka ki kwantar da hankali, Ki koma ki kwanta, babu wanda zai ara tambayarki wani abu" sun firgita da ganin haukan Angel. Dr laura duk tabi ta ru e Sun rasa gane kanta. Kallon Sojojin ta yi"Pls, Ku yale yarinyar nan, Muje office muyi magana, idan ba haka ba za'a Iya samun matsala" gy a kai sukayi ba don sunso ba suka Juya tare da fucewa daga akin tare da Likitocin, Ya rage da ita sai Dr laura. "Pls My daughter kukan Ya isa haka, Ki koma ki zauna muyi magana kinji"? Lallashinta tashiga yi, Da yar Angel ke iya kallonta sumar kanta duk ta rufe mata fuska, dagangan ta irarma kanta Ciwon hauka. Marairaice mata fuska Angel tayi"dan Allah ki taimaka mana, su maida mu asarmu, banaso mu rasa an uwanmu zai Iya mutuwa, maganinsa yana can, Nayi maki al awarin idan ya farfa o zan fada maku duk wani abu da ku ke son ji dangane da mu" saukowa Angel tayi daga saman gadon, A sukwane ta zube saman gwiwowinta agaban Dr laura, Idanuwanta sun cicciko tab da hawaye take fa in"Na ro e ki Ki taimaka mana, kamar yarda Allah Ya taimake ki, Kice ma sojojin can sumaida mu Nigeria, Idan ba haka ba an uwana danish zai mutune, ba zaku Iya sarrafa shi ba, maganinsa yana acan, Ni na yarda ku sanya jami'an ku, su bimu can kasar don su shaida abunda na fa a masu su sanya mana ido' Muryarta asha e ta arasa maganar. Tsananin tausayintane Ya kama dr. Laura har cikin ranta ta aminta da yarinyar, Mi a mata hannu tayi"mi e tsaye" da sauri Angel ta aura hannayenta asaman na dr laura, ta yun ura ta mi e, ba zato ba tsammani taji ta rungumeta a kirjinta, amshin turarenta Ya daki hancin Angel sosai ta ankameta tana faman sauke ajiyar zuciya. Shafa sumar kanta dr laura tayi a hankali take yi mata magana "Ni tun farko banso suka tsareki da tambayoyinsu ba, sunyi gaggawar yin hakan, But Inaso ki kwantar da hankalin ki, Zanyi iyakar bakin arina wurin ganin sun maida ku asar ku, idan har kikayi min al awarin zaku fa a mana abunda ya faru da ku bayan an uwan naki ya farfa o kamar yadda kika ce" Cikin sanyin murya Angel tace"Nayi maki al awari shiyasa ma nace su sanya jami'an da zasu bibiyi rayuwarmu" ta are maganar tare da raba Jikinta daga na Dr laura Shafa fuskarta tayi"is ok, Zanje muyi magana da su yanzu ki koma ki kwanta ki huta" Amsa mata Angel tayi da toh, Bayan fitar dr laura, Da i kamar zai kasheta, don tana ji aranta zasu amince masu su koma Nigeria, juyawa tayi tana neman robar fantar data jefar a asan tiles can ta hangota gefen nightstand zuwa tai ta auko lemun ta koma gefen gadon Hankali kwance taci gaba da shan lemun fatanta Allah yasa su amince masu. Gaba ayansu sun Hallara a katafaren ofishin dr laura, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna saman ha un kujeru, table ne Ya ratsa tsakaninta da su,. "Shawarar da zan bada shine bai kamata mu takura masu da tambayoyi ba, duba da Yanayin yaran akwai ciwon damuwa atattare da su, tursasa masu zai Iya haddasa masu wata matsalar da bama fata" Dr laura ce ta kora jawabin idonta akan faces din sojojin Commender yace"Ya zamuyi kenan? Menene Mafita don muna bu atar son Jin ainihin abunda ya faru da su a dajin nan" Numfasawa dr laura tayi"Munyi magana da yarinyar, tabbas bata manta komai ba, tasan abunda ya faru da rayuwarsu sai dai rashin yarda da tsoron fargabar abunda zai biyu baya idan ta fa a mana sun Hana ta sanar damu, abun duba anan shine Babu yarda za'ae su saki jiki damu don ta yanzu, saboda basu sanmu ba bugu da ari kuma ba an kasar mu bane, donni na yarda da maganarta, Idan har munaso muci nasara akansu dole sai mun yi masu abunda su ke so, ta hakanne zasu saki jiki damu har su fa a mana gaskiyar abunda mu ke son ji daga gare su, sannan suna bu atar wadda zata Kula da rayuwarsu tamkar mahaifiyarsu, Ta hakanne zasu saki jiki da ita har su Iya fa a mata damuwarsu, abu na biyu shine Muyi masu abunda suke so! Musamman ita Angel din ta roke ni akan mu maida su asarsu, Akan idonku kunga haukan da tayi mana tabbas akwai amshin gaskiya a maganarta, tace maganin an uwansu yana acan, kuma tace zamu Iya sanya jami'ae su bi su har can kasar sannan tayi al awarin idan harya farfa o zata fa a mana duk abunda muke son ji. Shiru suka anyi na wani lokaci kowan nan su Yana nazarin maganar dr laura. Numfasawa Major yai kafin ya soma magana"Me zai hana mu dam a Case insu ya koma hannun Hukumar Isod? (Intelligence Special Operations Division) Tun da shugabansu asar Nigeria, su ka aine zasu Iya bincikar Ainihin abunda Ke faruwa da yaran, saboda suna da warewa a 6angaren. Jinjina kai Commender yai da alama ya gamsu da jawabin Major "Hakane ka kawo shawara mai kyau, case in yafi dacewa dasu, Tunda Aikinsu ne Yin binciken sirri Harma da fafatawa idan ta kama kuma duk muna atare dasu banbancin ka an ne mu ba jami'an sirri bane su kuma duka sun Ha a sunayin aiki a matsayin sojoji sannan kuma jami'an sirri" Captain Yace"Nima na goyi bayan hakan, amma fa zaiyi wuya mu iya samun chief in nasu a waya, So the best way to contact him is through email, We need to start making our request for the case through their email, If they show interest in the case, we will turn everything over to them." Commender yace"shugaban nasu ai Yana a Washington (babban birnin america) kuma naji ra e ra en kamar cikin weekend da zamu shiga zai bar asar ya koma Nigeria, duk da bani da tabbaci kunsan aikin nasu na sirri ne babu mai sanin shiga da fucen su, Idan har muka samu ya nuna interest akan case insu komai zai zo mana da sau i, In yaso sai mu dam a mashi Yaran ya tafi da su can, mu kuma zamu dinga bibiyarsu don jin ya ake ciki" Murmushi Dr laura tasaki, Har cikin ranta ba aramin da i taji ba, Fatanta Allah yasa Chief in Isod Ya amince da case in Yaran, ko dan saboda Yarinyar da ta ro e ta akan amaida su asarsu" "Doctor, how long do you think it will take for the children to be discharged"? captain ne yai mata tambayar, Dr. Laura ta bashi amsa da cewa "After the three-day injection course is completed, we will be able to discharge them, Shima ayan Yaron mai fama da ciwon zuciya Zamu Iya sallamar shi idan har aka Kiyaye sharu an da zamu rubuta na bashi kulawa ta musamman, " ta ara da cewa"zasu Iya zama a asibitin namu har zuwa lokacin da shi chief in zai Amsa mana bu atar mu" Commender yace"dole ne mu sama masu wadda zata Iya kula da su tamkar anta kamar yarda kika bada shawara, wadda zata Iya tarairayarsu ta basu kulawar da zasu Saki Jiki sosai," Yai