Sashe 35
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi ya aura asaman kawunan su a hankali ya ke shafa sumarsu kan su, sai ara ame shi suke Yi, a hankali ya furta masu Ya Jikin naku ? Jemimah da Azeeza suka ha a baki Ai mun warke, Gidan daddyn Genie zamu je yau Ganin sun i sakin shi yasa Angel yi masu magana ku sake shi mana, Ko mun samu muyi sauri muci mu tafi, idan har ba barin Dajin nan mukayi ba Hankalina ba zai kwanta ba Jin maganarta yasa suka sake shi, Ya ru o hannun Azeeza dana Jemimah suka jera atare suna tafiya, Cikin Kogon dutsen su ka koma gaba ayansu, suna shiga suka tarar da Haris zaune shi ka ai, bai jima da farkawa daga bacci ba, A asa kowanansu ya zauna, Angel ta curo kayan marmarin ta rarrabamasu, A tsanake suke sha suna kallon Juna, bayan sun kammala sha, Suka fara shirin tafiya, Ba tare da 6ata lokaci ba, Angel Ta goya jemimah abayanta da mayafi ta aureta, Gabriel Ya goya Azeeza abayanshi, sai da i suke ji an goyasu har gwalo suke Yima Parveen, Batul kuma ta Goya Back pack in Unaiza abayanta, Javed Ya ru e masu akwatin kayansu, basu bar komai acikin kogon ba, Hatta Gorar ruwansu acikin kwandon kayan marmarinsu su ka sanyata, Parveen ce ta ru e kwandon a hannun ta. Matafiya sun shirya tsaf saura tafiya ta rage masu, kafin fitarsu daga kogon dutsen saida Angel ta yi masu addu i tabi kowan nan su ta tofe shi tun daga asa har sama ko da ta zo kan Danish sai ce wa yai me take yi haka? ta daina watsa mashi yawu baiso, dariya tayi batare da tace mashi komai ba, Danish ne ke ru e da Haris saboda rashin warin Jikin shi. Suna tafiya suna fira a dokar dajin, Su parveen sunga abubuwan da suka aure masu kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta walo Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo, Angel sai arin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya kashe masu idanuwan su. Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al ajabi, su fa duk aukarsu Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling akin su na kurkuku Yake, Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta fa a mata tayaya akai har aka aura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba, Dariya Angel tasaki tare da cewa Kai parveen Nafa ta6a fa a maku saboda gudun haka, Rana ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya aurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai da yar ta samu suka fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya tunawa, A alla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko ina acunkushe yake da tsirrai. Gaba aya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance Har bacci ya auke su a goye sai daga bisani suka farka, Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? afafuwana duk sun rurru e, Ga yunwa inaji Parveen ce tayi maganar, Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba zamu are acikin Dajin nan ne, fuskar Angel ayamutse ta yi maganar, Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ru Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada tsokanarta atuwa dake dole sai an maki goya irin namu Harara parveen ta watsa mata. Ba tare da tace komai ba. Zogin da afafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata atuwar bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan tasha ta mi a ma Naufal yasha ya mi a ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu suna faman lumshe idanuwansu, karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido, Angel ce tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace an zamuyi, batul Ta natsu tana kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu, Angel Su wa annan basu gajiya da tsayuwa ne !? Fuskar ta a aure tayi maganar babu alamun wasa Su wa kike nufi Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata Bishiyoyin dake fuskantarsu, an zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a kwance taci gaba da cewa tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne ? Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, da yar ta iya cewa Haka Allah ya Halicce su Batul Gabriel da ya umshe dariya abakin shi yace da ita ke yanzu idan wa annan bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa ? Sai lokacin ta an saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka anyi na wani lokaci, Har bacci ya fara arin aukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take ji, aukarta Angel tayi tare da mi ewa ta kalli Danish Zanje nakaita tayi fitsari, lumshe mata ido yai tare da cewa No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko abayan bishiya ne Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita, bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan, Mi ewa su kayi jiki duk ba wari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya azeezarshi suka dasa da tafiya. Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta fa o wurinsu kamar an jehota, a matu ar figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da su ka yi. Hankalinsu Danish ba aramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse wa anda suka rage Danish ne sai haris shima saboda Ya ru e shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da Haris jikin bishiya da gudun gaske ya fa a Cikin Dajin don Ya tattarosu. Jemimah ta ame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar baki, Ciyawar dake awurin take Ci, Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya kara e kunnuwansu Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, an nonuwanta azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko ? shiru Angel bata tanka mata, Damuwace arara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba adawo dasu Batul ba. Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta fa o wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita, Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma ya aureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah ka ai yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro. Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne Gabriel yai maganar, da sauri tace a, Kada kaje ko ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka shiga Danish zai nemo su Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin an uwansu, suka soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke maza, Batul na aru e da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su araso Angel ta fashe da dariya hada dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba aramin ona ransu yai ba. Ko da su ka araso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne suka sani, Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta aura da nata fa an akan dariyar da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, Ru o haris danish yai tare da taimaka mashi ya mi e tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta daji gwanin ban sha awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu shimfi a, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya ha a masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su ka ai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu aya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya aga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya auke su aya