Sashe 40
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ayoyi suka Sargaho afafuwansu kusan atare suka rubza asa kansu ya daku. A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya aya, Halittun nan sai binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu idanuwansu, ba zato ba tsammani afafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali ya cika shi, gaba aya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa. Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka araso bakin wata bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama ibarshi a cikin kwando, Gabriel na yun urin zura afarshi Ya sauko asa kwatsam idanuwanshi suka sauka akan kurar dake asan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu ya ha iya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba, Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu Muryarshi Na kakarwa yace Angel mun shiga uku, wlh kura ce a asa take cin nama, Sai lokacin ta wurga Idanuwanta asan bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun muryar Naufal Ta kara e kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci babu lafiya a wurin an uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yun urin sauka yasa gabriel dam o hannunta, muryarshi a hargitse yace Kada ki sauka angel kashe ki za ta yi Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun riki a jawur dasu tace wara ta cinye ni, wlh sai naje wurin an uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah ka ai yasan meke faruwa dasu kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan Gaba ayansu suka undumo asa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin ta ago da ido ta kallesu, Da iya arfinsu na arshe suka yun ura suka mi e a guje suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin shi ba, lokacin da suka fa o wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba aramin tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi. Kafin Angel tayi yun urin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta fa o masu, Da arfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana mi a hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su kawai ta ke hari, kur awa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar masu masifa ta hanasu sakat *Boss Bature Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom inshi ya nufi Palour, A zazzaune ya samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle in nashi, Ya auki wankan tsadaddiyar shadda mai aukar ido, amshin turaren shi Ya cika palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama ha iyar agogon diamond ce wadda a alla price inta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a mu ami bai kai shi matsayi ba, Alhaji musa anine ga Alhaji ubaid uwa aya uba aya, kuma shine former president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi ba i wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya aukar wanka ga aji ga kuma ji da kai. Daga asan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid ne ka ai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arzi in kallo bai samu ba, har sai da hajiya layla tace mashi baka ji shureim yana gashe ka ba ? Ba tare daya bu e idon shi ba yace Naji, sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya 6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi, Har yau mamakin Halin anin nashi Yake yi. Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka matsa kusa dashi yaji umin anshi a jikin shi acewar Alhaji ubaid, Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta sha e wuyan Alhaji musa, jin kanshi na matu ona mata rai, mi ewa shureim yai tare da nufar sofa in da musa ya ke a hakimce, ya zauna daga asa, Uncle sannu da zuwa, Ya gajiyar tafiya sai lokacin ya an ware idanuwanshi tare da kallon shureim na tsawon mintuna, sai da ya mula ya sha iska tukunna ya soma magana Babu gajiya atare da ni, kai zanyiwa sannu, ni banzo da niyar in ganka ba, banma yi tunanin kana a asar ba, sai da Ya ya ya ke fa amin, shureim kafi arfin ka tako kazo gidana ne? Laifin hada ni ya shafa kenan ? Tun da ya soma magana, hajiya layla take jifar shi da harara a fakaice batare da ta bari Alhaji ubaid ya gani ba, ita sam baya burgeta, haushin nuna isar da yake yi take ji, Ay min afwa Uncle, bani da kwanciyar hankali ne shiyasa bana samun damar zuwa, amma kuna araina, Ta6e baki Alhaji musa yai ba tare da ya furta kalma ba Hajiya layla tace To ai kaima in baka damu dashi ba, Ba ka neman shi taya zai yi tunanin kana bu atar ganin shi a gidan ka bata arasa maganar ba, da sauri ta dakata ganin irin kallon da Alhaji ubaid ya ke jefa mata, sam baya son tana shiga tsakanin shureim da anin shi, saboda mugun son shi ya ke yi baya son 6acin ranshi. Kare shi za ki yi ? Alhaji musa ne yai maganar sautin muryar shi a kausashe, Shiru tayi bata tanka mashi ba, Kada ki shiga tsakanin Uba da ansa, Kija baki kiyi shiru Alhaji ubaid ne yai maganar, Ta6e baki tayi tana faman hura hanci. Ae da kabarta yaya ta arasa maganarta, yai maganar fuskarshi auke da murmushi. Kafin ya kawar da idonshi daga kallonta. Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai zamu tafi, bazan barka a gidan nan ba, don Na fahimci akwai masu takura maka, Shiyasa duk ka rame kayi duhu, Cikin kulawa yake yi mashi maganar, hannun shi aya asaman kafa ar dr shureim in, Layla ta yi mamakin jin abunda yace, mutumin da ko an shi bai sakar masu fuska shine ya ke zancen zai tafi da shureim, kwa6e fuska ta yi don ta fahimci so ya ke ya untata mata. Alhaji ubaid yana murmushi yace naji dadin jin hakan, wata il idan kuka je can yafi sakewa, don na fahimci shureim baya son zama gida kafin ya arasa maganar, layla ta katse shi da cewa ae sai ku tsaya kuji ra ayin shi ko? Idan ya ce yana son zuwa can Tana rufe baki Alhaji musa yace ai ba shawara nake nema dashi ba, Umarni ne Cikin isa Ya furta hakan, Kafin ya kalli dr shureim, ka shirya komai naka idan muka tashi tafiya atare zamu tafi Lamarin ya aure mata kai, shi dai Dr shureim yai shiru bai tanka masu ba, Girgiza kai Hajiya layla tayi bazai yiwuwa ba, haba dan Allah duka yaushe muka samu shureim in ya dawo wurin mu, Sannan kuma yanzu kace zaka tafi dashi? A an bari ya huta mana, Shi ka ai fa nake gani inji da rai a6ace take magana, Sun natsu suna sauraronta, sai da takai arshen Aya tukunna Alhaji ubaid yace da ita meye na tada jijiyoyin wuya? Guduwa zai yi dashi ne? Bafa raba ki zaiyi dashi ba, Yana so ya zauna gidan shi na an wani lokaci, fuskar Alhaji musa a aure yace idan na ga dama zaici gaba da zama awurina ne kuma ke baki isa ki hana shi ba murmushin fuskar Alhaji ubaid bai washe ba yace ba girmanku bane ku tsaya kuna sa insa akan Shureim sai kace wani aramin yaro, ko da ya ke laifin ka ne shureim tuntuni nake baka shawarar kayi aure ka i yi, da ace kana da Iyali babu wanda ya isa yai iko da kai da zolaya yayi maganar, Shureim dai ya natsu yana jinsu, Ya jima yana jin takaici yadda rayuwa ta canza mashi, Ya koma tamkar aramin yaro a idon kowa, saboda raunin zuciyarshi. yar Alhaji ubaid ya samu Ya maida sa in sar tasu Wasa, dama can basu jituwa tsakanin Layla da anin shi tunfil azal. Yakamata mu tashi muje muci abinci, zainab ta shirya mana a dining layla ce tayi maganar, aya bayan aya suka mi e tare da nufar Dining room. an daga Cikin Na sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya* *Evil forest* Sautin arar Dan araren Helicopter mai saukar angulu irar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin asar america ne Ya kara e ko ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza suke yi saboda arfin iskar fankar Jirgin, Shawagi jirgin yake yi a saman Iska Yana kewaye ko ina na tsawon mintuna talatin, Yayin da Hot soldiers din dake a tsaye saman jirgin cikin shigarsu Ta ka ki sun aura amarar Yaki, Sai dai ga dukkan alamu Sun kammala gudanar da abunda Ya kawo su Cikin Dajin, aya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ofar helicopter in Hannun shi ru e da tactic phone Wayar da sojoji suke yin amfani da ita wurin yin sadarwa ga Manyansu dake acan Headquater, Cikin Harshen turancin Yake Yin magana muryarshi na fita da amon murya saboda arfin iskar Dajin We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest. Da wani