← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 106

Sashe 64

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

gyara fuskarki, akwai sojoji da suka zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast inki ko kina da za6i na abunda kike son ci"? Girgiza kai Angel tayi"a'a" Okey daga haka Nurse in ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin ofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din ta shige ciki. A hankali take tafiya tana bin ko'ina na toilet in da kallo A tsaftace yake fari yal Kamar ba'a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba. Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples inta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba aramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha'awar son Yin alwala, nan take ta canza ra'ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet in tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? Bu ofar da akayine yasa ta ago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ru e da tray na kayan breakfast in Angel asaman table ta aura mata shi.
Chapter 64 · 0% Book details