Sashe 90
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha aya za'a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su" ranta amu ar 6ace take Yin maganar. Cikin kwantar da murya Dr mark yace"ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba" Dr brown ya aura da cewa"sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma'aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a dam a mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba" Gya a kai Dr Laura Tayi"Shikenan na ha ura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai" "Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da aunarsu, Har na fara jin kewarsu" acewar dr. Mark Dr brown yace"aini har asarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su" Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa. *DAULAR ALHAJI MUSA* *Dr Shureim an kwanakin da yayi a gidan Uncle in nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman aki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matu ar jin da in kulawar da take bashi, sun sha u da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta fa akin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba aramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba. A Kishingi e yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko'ina ba, ko ofar bedroom dinsa bai le a ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba aya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya aura saman pillow, Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a jikinta aka inka kayan, duk da bata iba kayan sunyi bala'en Yi mata Kyau, Tani da Lami ne sukayi mata Make up, hatta aurin an kwalin kanta sune suka aura mata shi, ziririyar sar ar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai yalli Yake Yi, ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ru e da handbag, fragrance din turaren jikinta mai da in sha a ahanci. Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo akin tayi mashi sallama bai amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta ga ko bacci yake yi ne Tun kafin ta araso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen din Laptop nasa Ras taji gabanta yai mugun fa uwa, zuciyarta tamkar zata faso irjinta saboda zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce yake kallo. Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim inta rungume da mace a kirjinsa. Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar ara wadda tayi silar firgitar da shi, da sauri Ya mi e tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar hannunta asa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta. Hankalinshi ba aramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya nufeta fuskarshi da alamun ru u ya furta"zeenatu! Lafiya? Meya faru? Girgiza mashi kai tadinga yi tana fa in"kada ka matso kusa dani yaya shureim, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" gaba aya ta gama rikitar dashi"zeenatu ki natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke? Cikin shesshe ar kuka tace"yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya bugawa, tun azu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne? Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta arasa maganar, tare da juyawa da gudu ta fuce daga akin nashi. Hankalin shi ba aramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin shi. Dafe kanshi yai da hannu aya, har cikin ranshi baiji da in kalamanta ba, baiso yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba, lumshe idanuwanshi ya anyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta walla fa rai akan son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata al awarin yau zai auke ta a sabuwar motarshi su fita yawo. Cikin sanyin murya ya furta"am sorry my zeenat, " da sauri Ya nufi toilet don yai wanka. _~*BossLadiesWriters*~_ _* KURKUKUN ADDARA ~Middle step~