Sashe 41
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
irin speed jirgin ya karya kwana ya mi i hanyar komawa asar da ya fito , Nima kuma na ajiye al alamina. *Boss Bature Mu ha u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura ku in*_~*BossLadiesWriters*~_ _*KURKUKUN ADDARA*_ _The Prisoners E11_ *Daga al alamin Boss Bature* ~Middle step~ _A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._ Gaba aya Haris ya fidda rai da rayuwa, tun da halittar nan ta zura afafuwansa cikin wawakeken bakinta, tsabar tsoro da firgici sun hana shi motsawa jini duk ya wanke bakinsa har saman rigar sa, jikinsa yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyaci, Bawan Allah sai sambatu ya ke yi yana ambaton Sunan Danish dana sauran an uwan su don su kawo mashi agaji. Ba zato ba tsammani ya ji Sautin dirar wani abu daram! tamkar zai fasa kunnansa, tsabar firgitar da yai ne yasa nan take ya sume saman koraren ciyayin. Wani Gabjejen Bature ne A tsaye cika shigar Kaya na tatattun an ta adda babu igon Imani akan fuskarsa, Hannunsa aya ya ru e da Bindigar da yai amfani da ita wurin harbin Halittar da ta nanna e Jikin Haris, yayin da ayan hannun ya ke ru e da cigarette. Hankalin shi a kwance ya ke zu ar Tabar Cikin warewa Har ta hanci Haya in Ya ke fita, kwarkwararrun idanuwanshi na akan Haris dake kwance Ya sume, Tuntsirewa Baturen Ya yi da dariya hada an girgiza kanshi, da arfan muryar sa ta Mashaya giya cikin harshen turanci ya ke fa wani irin ganganci ne ya kawo ka urmin daji da ananun shekarun ka, ba ka da hankali ne? Matashi da kai kake son are rayuwarka abanza? Ina iyayen ka su ke kamar zautacce Shi ka ai ya ke yin maganar shi, sam bai fahimci Yaron Ya sume ba, Sai da Ya gama Magana kafin ya matsa inda Haris yake a kwance, Ya zu unna Bayan Ya soke pistol in a qugunsa, Ya sanya hannayensa Biyu Da arfi Yake jan jikin halittar, Har sai da yai nasarar zaro afafuwan Haris daga bakinta, Allah yaso ba ta kai ga Gatsa ha oranta akan legs insa ba, da ko ta yi mashi babbar illa, Bayan Ya zame jikin Halittar da karfi Ya jefar da ita gefe aya, yun urawa yai ya mi e tsaye yana kakka6e tafin Hannayensa, Zu ar Tabar sa Ya ara Yi Bani da zuciyar Imanin da zan Iya taimakon ka, ka gode wa Allah da na raba ka da dabbar nan, da ko yau Ka rasa afar zuwa gidan Iyayen ka Yana magana yana sakin dariya idanuwansa akan fuskar Haris. Sautin kururuwar neman a gajin da ya Ji ce Tasa shi Kan ga kunnansa ga iska Don Ya ji da kyau, Muryar Naufal ce Ya ke faman Fasa Ihu, Da gudu Baturen Ya kutsa Cikin Dajin Yana Tunkarar inda sautin arar ke fitowa, ta wutsiyar idon shi ya hango gifcin mutune sanye da Jajayen kaya, Ta tsakantsakin jibga jibgan Bishiyoyin dake a kewaye da wurin da yake, Cikin Zafin Nama Ya daka uban tsalle ta tsakiyar wasu bishiyoyi, Kamar an jeho shi Ya fa o Tsakar wurin da Su Naufal su ke, Gaba aya sun fita hayyacin su, Halittun sun kewaye su sai gurnani su ke yi, Naufal da javed sun ame Juna, Kuka hada majina fuskokin su jaga jaga da hawaye, wandunansu a ji e sharkaf da ruwan fitsarin da suka saki, an iskan murmushi dangerous terrorist Ya saki kafin Ya zaro bingidar da ke soke a qugunshi, Ya saita Jikin Halittun aya bayan aya yake sakar masu alburushi, duk wadda ya harba nan take Tsakiyar Cikinta yake tarwatsewa an hanji su fito waje, Sautin harbin bindigar da basu ta6a ji bane Yasa su rikicewa Kusan atare suke yanke jiki saman koraren Ciyayin suka fa a a sume, Tuntsirewa Baturen yai da dariyar sha iyanci Yana fa Yaran nan kuna da ban dariya, Sai ka ce ba maza ba? Kun iya shiga daji amma ba ku Iya fa a ba? Zaman gida da sanya buje zaifi da cewa da ku, In yaso kun cigaba da taya iyayen ku shiga kitchen yin girki acikin harshen turanci ya ke yin maganar. Gabanshi Ne yai mugun fa uwa Jin arar Jirgi A cikin kunnuwansa, Da sauri Ya kai idanuwansa saitin rassan bishiyoyin da suka lullu6e sararin samaniya, nan ta ke yanayin fuskar shi Ya canza daga annuri zuwa tsantsar ba in ciki, fargaba da tashin hankali, Juyawa yai da gudun gaske tamkar zai tashi sama Haka ya dinga buga uban tsalle Yana gudun Ceton, ga dukkan alamu bai da gaskiya shiyasa ya arin gujewa wa anda suka kawo mashi Hari, tuni Ya jima da jefar da tabar hannun sa, kwata kwata Baya a cikin Hayyacinsa, shi kansa baisan in da ya ke wurga afafuwanshi ba, saboda tabar firgicin da ya shiga, ko ma su wanene su ka biyo shi sun shammace shi bai yi tsammanin za a gano inda ya 6uya ba. Sautin arar dan areran Helicopter mai saukar angulu irar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin asar amurka ne Ya kara e ko ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza su ke yi saboda arfin iskar fankar Jirgin, har wani jijjiga ya ke yi tamkar zai fasa dodon kunnan mutun, Shawagi ya ke yi a saman Iska Yana kewaye ko ina. Hot soldiers din da ke a tsaye ba ofar jirgin zafafan gaske fusatattun sojoji masu ji da arfi, cikin shigarsu Ta ka ki sun aura amarar Ya ki, aya daga cikin su Hannayen sa biyu Na ru e da Telescope abun hangen nesa, Ya kanga shi saitin idanuwansa, Sojan da ke a gefen shi Yana Ru e da Tactical phone wayar da sojoji ke Yin amfani da ita wurin yin sadarwa da Manyansu dake acan headquater, Cikin Harshen turanci Ya ke Sanar da su cewa Sun araso Dajin ayanzu hake suna kewaye shi domin gano Location in da an Ta addan Ya 6uya a dajin. Me ru e da abun Hangen nesan ne Ya soma magana Yana aga murya ya ke fa in A samu wuri a sauke Jirgin Yana zargin me laifin Yana a yankin da su ke, Jin maganar Shi Yasa sojojin dake sarrafa Jirgin su ka Soma arin Samun wurin Da zasu Sauka, A hankali helicopter in Ya ke yin asa tunkafin ya arasa direwa, Sojojin suka soma diddirowa asa Sautin Army boots in dake a kafarsu Yana bugun asa kamar zasu dare ta, Hannayensu ru e da Jibga jibgan bindigu, Haka zalika qugunansu na soke da pistols ananun bindugu, Sun rufe kawunansu da helmet (hular kwano) Hatta faces in su ba ka Iya gani, Iya idanuwansu ne ka ai a bayyane, Kusan su shidda ne su ka sauko daga jirgin, Da hannu Commender in su ya rarraba su zuwa gida Uku, kafin ya basu Umarnin shiga Dajin, Da gudun gaske Su ka fa a cikin zafin nama su ke kur awa Cikin urmin Dajin, Babu tsoro ko fargaba suna da warin gwiwa akan aikin su da warewar su, kuma suna da tabbacin za su yi nasarar Yin aikin da aka turo su, saboda duhun dajin Da fitilu masu haske su ke yin amfani wurin haska gabansu. Gaba aya sun Yi matu ar galabaita, tun suna ti ar gudu Hancin Angel Ya soma bleeding zufa duk ta wanke fuskokinsu da jikinsu, Ma oshinsu ya bushe amas sai azabar ra i da ayin da ya ke yi masu afafuwan su Zogin azaba su ke yi masu, Sun rasa ina zasu tsoma ransu su ji da i, Suna a tsaka mai wuya tsakanin mutuwa da rayuwa, Kurar dake a biye dasu Tana gab da zata cimmasu, Wani irin uban tsalla ta daka tana Gurnani Ta takaiwa afar Angel Cafka da ha oranta, wata irin gigitacciyar ara ta fasa ita da Gabriel a matu ar razane. Kurar na arin Gutsire afar Ba zato ba tsammani, Sautin dirar bullet Ya ratsa kunnuwan su, Basu san daga Ina aka harbo bullet in ba, Gaba aya ya tarwatse Kan kurar, Nan take ta saki afar Angel Ta fa asa tana birgima, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel Ya sauke Yayin da zufa ke cigaba da wanke fuskarshi, angel kuwa Tsabar firgice ne Yasa ta yanke Jiki Ta fa asa a sume tamkar matatta. Hankalin Gabriel Ba aramin tashi yai ba, Ganin yadda Angel ta zube, Cikin shesshe ar kuka ta wanda ya gama galabaita muryarsa na kakarwa ya furta sunan ta da arfin Angel! no!No! Don t die Angel, Na shiga Uku, Pls Angel ki tashi Ina zansa rai na! Fuskarsa sharkaf da hawaye yake yin maganar, Zuciyar shi a karye Ya zube saman gwiwowinsa agaban Angel, Ya dinga kuka yana jijjiga jikinta Da hannayenshi, Sam baya acikin hayyacin sa, shiyasa ma bai yi tunanin Su wanene suka kashe Kurar ba, duk a tunanin shi Angel ta mutu ne, duk yabi ya zauce ya rasa madafa. Jin Takun Tafiyar Mutanan da ke tunkaro shi ne yasa shi saurin wurga eye balls insa da suka ka a jawur Yana duban su, Sojoji ne Su biyu Hannayen su Ru e da Bindugu, duk da baya acikin hayyacinsa saida Ya zabura yana neman guduwa a zaton shi Gianta ne na gidan kurkukun addara. Kakkausar Muryar Sojan ce ta ratsa kunnuwanshi t Move or else i will shoot ur head wit My gun Wannan maganar da ya yi ce tasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar ba tare da ya juyo ya kalle su ba, ya soma magana cikin rawar murya Just kill me so that I can finally rest, Na rasa an uwana, bani da burin cigaba da yin rayuwa a duniyar nan, ku kashe ni kawai idan ba haka ba ni zan kashe kai na Yana magana zufa na tsastsafowa ta jikin fatar shi. Muryar Sojan ce ta kara ratsa kunnanshi cikin harshen turanci yace ba zamu kashe ka ba, rayuwarka tana da mahimmanci a wurin mu, Aikin mu shi ne mu shiga tsakanin ku da mugun da ya yi garkuwa