← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 106

Sashe 38

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

inshi, Ta kar6i wayar tana duba hotunan, Ta yi mamakin ganinsu kamar hauka, hada wanda ya ke a rungume da ita saman irjinshi, ta6e baki layla tayi, hankalin shureim ba aramin tashi yai ba ganin zata danna delete all, jikin shi har tsume ya ke yi. Assalamu alaikum ! Muryar zainab ce ta katse mata hanzarin ta, a sukwane ta juya tana binta da kallo, a bakin ofa ta tsaya Alhaji ne ya shigo tare da kawun shureim, Shine yace nayi maki magana yatsina fuska layla tayi Naji, ga ni nan zuwa a wa shureim wayar tayi ka tabbatar ga goge su, sannan ka fito ku gaisa da kawunka, Amsa mata yai da toh, Bayan ya kar6i wayar, fitar ta keda wuya Ya cire memory in wayar, Ya 6oye shi a cikin rigar pillow, Ajiyar zuciya ya sauke Ba aramin da i yaji ba, don ji ya ke kamar za a raba shi da ranshi idan akace ya goge hotunanta. Toilet ya shiga ya wanko fuskarshi, Ya futo Ya nufi dressing mirror, cikin jerin turarurrukansa ya auki aya ya feshe shi a jikin shi, bayan ya ajiye ya fito daga akin Ya nufi babban palourn. *GIDAN AN IYA* Tun da ta fito daga cikin toilet ta ke a tsaye bakin wardrobe, daga ita sai Towel aure a irjinta, Ya sauko har saitin gwiwarta, a alla Tafi arfin mintuna goma, ba tare da ta motsa ba, idanuwanta na akan Jerin suturarta da ke a ninke sun sha guga, ba komai ne ya tsaida ta ba fa ce neman kayan da zasu dace da tarban Manyan ba in su da zasu Yau, Ruwan ido take yi, duk kayan da ta auko sai taga kamar ba zasu dace da ita ba, Wayarta dake a jiye saman drawer ce ta soma ringing, nan ta ke taji gabanta ya fa i fatanta Allah yasa basu bane suka araso, Da an saurinta ta nufi wayar tare da kai hannu ta auketa, ko da ta duba screen in wayar, babu sunan wanda ya kira, Ba uwar number ce, kokwanto ta shiga yi akan ta aga ko karta aga? Don ita a tsarinta bata aga ba uwar number in dai ba wadda ta yi saving akan wayarta ba ce, kusan sau uku kiran nashigowa Yana yin rejecting ba tare da ta aga shi ba, tayi kasa e kamar an dasa mata Aya, Shigowa Cikin akin Zahra ta yi, bakinta auke da sallama, turkish gown ce a jikinta launin pink ba aramin kyau tayi mata ba, tayi rolling veil saman kanta. Ganin Aneelerh a tsaye yasa tace lafiya? Ya akai naga baki shirya ba? Ko kin manta cewa suna a hanya? Sun fa kusa isowa, Na rasa meke damunki, Ko har yanzu kewar baby junaid in ce bata sake ki ba ? Harara Aneelerh ta an jefa mata, Ba tare da tace koma ba, ta aura wayarta saman mattress, kafin ta juya ta nufi wardrobe din Kayan da ta bari a bu Zahra zo Ki tayani zabar kayan da zan sanya, Ruwan ido Ya hana ni auka tun murmushi zahra ta saki yayin da take tunkarar wardrobe Aunty aneelerh, shiga za ki yi ta mutunci, ta kece raini, Lace ko shadda su zasu fi dacewa, Ta yi maganar tare da Kai hannu cikin wardrobe in kayan ta janyo mata wani ha an lace launin golden colour, ta mi a ma Aneelerh, Fuskarta auke da murmushi ta kar6i Kayan da zahra ta mi a mata na yadda ke wararriyace a6angaren iya zabar kayan da zasu dace da mutun, nafi karfin 15 mins ina neman wanda zasu dace dani na kasa, sai da ki ka zo Zahra tace kada ki manta aikina ne, burina kiyi kyau auntyna, surukanki su ganki a mutuncenki, bari naje na auko maki sar ar da zata dace da kayan, amsa mata Aneelerh tayi da toh, Wuce wa zahra tayi agaban drawer chest Ta zu unna ta dauko mata jewelry box dinta, Ta bu e ta lalubo mata necklace da earrings launin Lace inta, maida box dinta tayi kafin ta mi e ta daura mata su gaban mirror. Aunty aneelerh, Ga su nan saman mirror, Pls Ki shirya da wuri, Ni zan je na taya su mami shirya masu abincin Amsa mata ta yi da toh ta ara da yi mata godiya, Bayan fitar zahra, Aneelerh ta shirya tsaf cikin Lace inta, riga da skirt, sun yi bala in yi mata kyau, sun an kama jikinta, shape inta ya fito sosai, Kamar a jikinta aka inka kayan, a gaban mirror ta zauna tana yin make up, lip gloss ta shafa ma la66anta, Ta an shafa hoda, ta auki brush tana gyara jagirarta, Sumar kanta Ta sauko har saman bayanta, arar Shigowar text a wayarta ne yasa ta an kalli 6angaren da wayar take ajiye saman gado, sai lokacin ta tuna da ba uwar number da ake ta kiranta azu, sai da ta fara aura dan kwalin leshin Kafin ta mi e ta nufi wayar ta auke ta, Da yatsan hannunta ta janyo sakon A hankali ya bu e, Ta yi mamakin ganin Sunanta da aka rubuta da manyan haruffa, menene ma anar sakon? Just Aneelerh? Wanene wannan? Kiran number ta soma arin Yi sai dai ta i shiga, A arshe ta hakura ta daurata saman pillow, Gaban Mirror ta koma ta auki jerin turarurruka tana feshe jikin ta da su, tunawa da baby junaid inta yasa ta an saki murmushi, tayi missing inshi sosai, yau tun da safe Mahboob Yaje kai shi school, Bayan ta ha a da shi da ku in fetur, kusan sati biyu da fara zuwanshi makarantar, kullum da fara a yake tafiya, yana zumu i, da zarar an kaishi Ya ke saka masu rigima sai sun dawo dashi gida, Har atashi daga school in Yana yin kuka, Fuskarshi jawur ake dawo mata da shi. Malaman makarantar har sun canza mashi suna daga Junaid zuwa babyn mommy, saboda sunanta da yake yawan kira masu. Daga waje tajiyo muryar Zahra tana kwa a mata kira Aunty Aneelerh! girgiza kai tayi aranta tace Ko yaushe ne zahra zata daina Yi min irin wannan kiran talaucin kamar zata ararmin da sunana Zahra na shigowa akin ta Waro ido waje tana fadin Wow!!! Tabarakallahu Ahsanul khaliqin Aunty aneelern kinga yadda ki kai kyau? Kamar wadda zata shiga gasar miss world, harara Aneelerh ta jefa mata fuskarta asake tace Naji na gode Da yabo, ni dai yanzu fa a min Kiran menene kike yi min ? Watsa hannu Zahra Tayi dama ummi ne ta aiko ni zaki ci abinci yanzu ko sai anjima idan sunzo Yunwa nake Ji zahra, ba zan Iya jira sai sun zo ba, ki samu plate ki zuba min dambun shinkafa, Ki ha o min da lemu mai sanyi, Toh, Amma kafin nan mu anyi selfy mana ta yi maganar tare da Kunna camera din iphone nata, ta aga Wayar Tare da aura kanta saman kafa ar Aneelerh, gaba aya suka saki murmushi, kusan hotuna Biyar tayi masu atsaye kafin Ta nufi hanyar fita akin tana fa Idan surukan naki sunzo zamu ara yin wasu hotunan tare, Hakan Yana ara dan on zumunci, fuskar Aneelerh auke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta. *EVIL FOREST* Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin urmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su, Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba akwance Yake ba, Danish Ya i farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne ka ai ke fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana. Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfi ar da Angel ta yi mashi, ya ke a kwance sun udundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata aya baya runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su katse mashi hutun shi ba. Angel Yunwa mu ke Ji Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar ar mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfi ar Danish, fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin ya i farkawa fatanta Allah yasa baccin lafiya ne ya ke yi. Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini Jemimah ce tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma take Yi, tana faman yamutsa fuskarta. Ki jaraba Tada shi mana, wata il Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci Naufal ne yai maganar muryarshi da kasala. Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci Gabriel Ne yai maganar, hannunshi aya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman irjin shi. Girgiza kai Angel ta yi a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne ka ai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba, bubbuga afa jemimah tayi cikin shesshe ar kuka tace wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin iya so kike mu mutu ko Gaba aya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel fa a, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata. Angel ku tada shi mana Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a a, su ka ai ne abunda Yake
Chapter 38 · 0% Book details