Sashe 88
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wara Yarinyar daka wuce akan wannan, taci ka sanyi daga gani babu kuzari a jikinta" yadda take fayyace abi'unsu kamar ta ta6a ganinsu. Ko da akazo kan Hoton Parveen Ya cika screen din laptop din. Da bu ar bakin Ummi sai cewa tayi"yarinyar nan daga ganin kumatuntu mayyar abinci ce, zai yi wuya idan ba asame ta da shegen ci ba, Ni bana so mutun mai ciye ciye" murmushin fuskar Major da commender sai ara fa ada yake yi, don ba aramin nisha i take basu ba. Hoton Jamimah Ya nuno mata, waro ido waje tayi hada sanya Hannu ta dafe saman irjinta. "Major, ru on wannan Yarinyar ai sai likitan mahauka, shi ka ai ne zai Iya sarrafa ta, ba dai ni ba, Ni ina zan Iya kula da ita, daga ganin bakinta zatayi tsiwa" Major yayi dariya tare da nuno hoton Azeeza, shiru tayi tana are mata kallo, kafin ta ago da ido ta kalli Major"sai naga kamar an biyu ne ita da Yarinyar da ka nuna min kafin ita, sunyi kama" Major yace"haka muke tsammani, sai dai muna hasashen azeeza tafi Jemimah shekaru kamar yadda an uwansu ya fa a mana" Yamutsa fuska Ummin america tayi"tana da kyau sai dai daga ganinta matsoraciya ce, wannan ko tsawa na daka mata zata Iya sakin fitsari a wando, gani da tsiwa bansan ya zamu are da ita ba" ta fada tana ta6a baki tace"wai Iya matane Yaran"? Ta yi tambayar tana kallon Fuskar Major "akwai maza" ya bata amsa, a dai dai kan hoton Haris Ya bu e mata shi. "Sunan shi Haris, shine yaron da commender Ya fa a maki cewa Yana fama da ciwon zuciya" Ta6e baki tayi"nifa banason namiji mai raunin zuciya, daga gani baya da hayaniya ba laifi yana da kyan fata" ta fa i hakanne saboda kasancewarta ba ar fata, tana son mutun me duhun fata. Wuce hoton Haris yai adai dai kan hoton Javed ya dakata Yana dubanta "Amma dai wannan Yaron an south korea ne ko? Major yace"bamu da tabbacin an Ina ne, duka yaran bamu san wani jinsi bane, sai dai sun fa a mana cewa an Nigeria ne" da sauri ummin america ta girga kai tana fadin"Impossible, babu kalan wa annan a nigeria, may be sun yi loosing memory in su ne shiyasa su ka fa i hakan" Hoton Naufal Ya budo mata, lumshe ido ta anyi tare da waresu akan kyakkyawan fuskarshi "Wow, kaga Namiji, sumar kanshi ta burge ni, Yayi min kyau" ta yi maganar tana hura mashi kiss. "Yaro ne" Commender ne yace haka, Ummi tace"Ai shi namiji baya ka an, especially idan abunsa ya ru a, a wurina wannan ba yaro bane Namiji ne" murmushi suka saki, basu damu da abun da tace ba saboda sun san halinta, bata mu'amala da matasan samari, Sai mazan da su ke da aure wa anda tasan idan ta bibiyesu za'ayi bala'i idan matansu suka kamata. Bayan Ya wuce hoton Naufal Ya bu e mata hoton Gabriel, tunda ta kafe shi da ido bata yaftaba sai faman jinjina kanta take Yi alamar mamaki Can dai ta numfasa tare da cewa"Allah Ya yayi halitta, gaskiya idan aka bani rainon yaran nan tamkar kun ba kura ajiyar nama ne, major idan akwai wani hoton nuna mini na osa na arasa ganinsu" Lokacin da Major Ya hasko mata hoton Danish daga zaune ta zabura ta mi e tsaye tana duban fuskarsa data cika screen na laptop din, duk suna akwance akayi masu hotunan idanuwansu arufe. Muryarta tamkar tame Yin ra a ta furta "Speechless! Major Ina kuka samun Kyakkyawar matashin nan mai kama da an sarkin aljanu? Anya Cikakken mutunne? Ko dai A cikin Dajin da kuka tsintosu Aljana ta haife shi Ta yada" dariya kowan nan su ya saki jin sambatun ummi dama sai da ransu ya basu zata ru e idan taga hoton shi. Major yace"sai ma kin ganshi a zahiri, ba aramin kyaune da shi ba" Ko da ta koma ta zauna, sam takasa auke idonta daga kan fuskar Danish, Yayi matu ar tafiya da imaninta, aranta har ta fara Ayyana koya surar shi zata kasance a zarihi? Muryar Commender ce ta fargar da ita ga dubanshi"dukansu ne muka nuna maki, shin kin canza ra'ayinka akan kula da su ko kuwa har yanzu kina akan bakanki" Shiru ta anyi tana yanke shawara da zuciyarta, duk sun agara da son jin amsarta. "Yanzu haka case din Yaran mun mi a shi hannun shugaban isod, shine zai cigaba da jan ragamar bincike akansu, jiya muka samu amincewarshi na kar6ar case din nasu, sai dai ya nuna baya bu atar 6ata lokaci yanason ya tafi tare da yaran can nigeria a jet dinsa, a satin da zamu shiga" Lokaci aya ummin america ta canza fuskarta zuwa 6acin rai, da farko tayi murnar jin cewa Case din Yana a hannun chief na Isod, daga bisani daya furta komawa Nigeria ne taji komai ya fita aranta. "Naji kin yi shiru, baki ce komai ba" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta soma magana ranta a6ace"Idan har kuna so in ru e Yaran a hannuna, they should stay in America. I will not follow them to Nigeria," Commender yace"amma meyasa? Ke kanki fa asar Nigeria ce why baki son zuwa asar Ki" Girgiza kai Tayi still fuskarta da 6acin rai ta furta"Ni ba ar nigeria ba ce, asalina ne acan, amma Ni black american ce, tun da nace banaso mubar maganar kawai, Ni zan koma gidan idan ka gama maganar ka" Yanayin fuskarta Ya canza sosai, 6acin raine tsantsa, sun fahimci kamar akwai wani abu daya ta6a faruwa da ita wanda har yajawo silar barinta asar, kuma batason Anayi mata maganar komawa can" Ganin yadda ta ha e rai babu annuri ko miskala zarratin akan fuskarta, Yasa Commender cewa"Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ba zamu takura maki ba, Zaki Iya tafiya" ba don yaso ba ya ambaci hakan, duk basu ji da in canzawarta ba, muryarta a disashe ta furta"thank u" ta yun ura ta mi e ta nufi ofar fita daga office din, Har ta kusa ficewa Muryar Commender ta katse mata hanzarinta"duk da bansan abunda ya faru dake a asarki ba da har yasa kika tsani jin an ambaci sunanta, da akwai wani abu da nike so in fa a maki ummi" yayi maganar tare da mi ewa hannun shi ru e da mug na coffee, Ya kur6a kafin ya aure da cewa"wannan dama ce agare ki, da zaki koma asarki a karo na farko ki nuna ma wa anda sukayi silar barinki asar cewa Kina araye kuma kinsamu cigaba a rayuwarki ba kamar yadda sukayi tsammani ba, inaso ki basu mamaki ummi, sannan zuwanki Nigeri bana dundun bane na an lokacine zaki dawo nan da zarar Mun samu nasara akan binciken Yaran, zamu dawo dake nan, saboda mu kanmu ba zamu so mu rasa nagartacciyar mace irinki ba, ke kanki kin sani muna aunarki kuma muna daraja imarki a idanuwan mu, ba zamu so abunda zai 6ata maki rai ba ummi, kina da damar da zaki Iya zuwa gida ki zauna ki yi tunani akan maganata kafin ki yanke shawara. Kalaman shi sun an ta6ata, tuni zuciyarta ta fara sassautowa, ita kanta zataso wannan damar ta zuwa Nigeria ko dan taba wa anda sukayi silar barinta mamaki. Numfasawa ta anyi kafin a hankali ta juya tana kallon commender dake tsaye abayanta, kamar bata son furta maganar tace"babu bu atar yanke shawara, Na amince Zan bi su zuwa Nigeria, Kuma nagode da karramawarku agareni, da zarar na gama aikin, zan dawo asata" Murmushi major da commender suka saki, Jin abunda tace, har yanzu bata yadda ta kira Nigeria da sunan asarta ba. Sun ji da in amincewarta, ba tare da 6ata lokaci ba, Commender ya dauko mata kundun dake auke da bayanansu Angel, duka takardun akwai Signature dinsu a jiki, saura sanya hannunta suke bu ata, cikin anin lokaci su ka ulla Yarjejeniya ta (guardianship agreement)atsakanin su da ita, sai da ta natsu ta karanta sharu ansu dalla dalla akan irin rainon da suke so tayima yaran kafin ta sanya hannu a takardun, bayan ta kammala sun bata wasu takaddun yarjejeniyar da zata ru e a hannunta. Bayan tayi masu sallama, Ta fito daga office din, tana tafiya Sojoji Na binta da kallo, Yayin da ita kuma hankalinta na akan takaddun dake a hannunta, Fatanta Allah yasa Ru on Yaran da za ta yi da kuma zuwan ta Nigeria Ya zama alkhairi agare ta. Tun kafin ta arasa gaban motarta da ta bari a harabar ajiye motocinsu, ta hango sojoji dadda6e sun kewaye motar suna jiranta, murmushin gefe fuska tasaki har dimple dinta Ya lotsa, ta fahimci tunda ta shiga office din commender suke ta jiran fitowarta don su yi mata magana, bata tsaya sauraron su ba, da yar ta samu suka yaleta ta shiga mota, a tsanake ta tada motar, Ta juya sitiyarin da gudu ta fuce daga head quarter din. *EX-PRISONERS Tun azu da safe kowan nan su Ya farka daga bacci, sun wayi gari da jin kyakkyawan labarin farkawar Danish, saboda zumu in zuwa ganin shi babu wanda ya nemi breakfast acikinsu, gaba aya sun Hallara a room dinsa, tun daga kan Haris, Javed, Naufal, Gabriel, Batul, Hannah, Jamimah, Azeeza, wansu da kwarkwatarsu sun yi tsaitsaye cirko cirkon suna kallon shi, fuskokinsu auke da Annurin farin Ciki, aya bayan aya Danish Yabisu ya rungume su a irjinshi, kamar sunyi shekara basu atare da juna, Haris hada kukanshi saboda murnar ganin Danish Ya farka. Sun tasa shi gaba suna kallonshi kamar zasu lashe shi, Musamman Azeeza da Jemimah, da i suke Ji Danish insu Ya farka. Muryar jamimah da shagwa6a tace"munyi fushi ma sai yau zaka farka, kullum sai munyi kukan rashin ka, ko bacci bamu Iya yi abincin ma ba mu ci" Harara Azeeza ta watsa mata"wlh arya take yi Danish kullum sai taci abinci sau uku, kuma tana Yin bacci" Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya ru e hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi an uwanshi. "Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin agarar da muka Yi na son ganin