← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 106

Sashe 44

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman sakin murmushi tana no e kai Jin Muryarshi tasa ta ago da ido tana kallon shi uwa ya sakar mata Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan naki? yarinya sai ka ce jinin fulani Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba ayansu, Yadda yai magana yai matu ar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta mi e daga saman sofa ta nufi Hajiya adama daga asa saman carpet ta zauna gefen afar Hajiya adama, muryarta asa asa ta furta Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can aura hannu hajiya adama tayi saman kafa ar Aneelerh Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da shi, da fara a ya amsa mata Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata Kafin daga bisani, Mami tace bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da surutu, ta fa i hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi bu atar hutu, Mi ewa su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu, wuce abie yai da uncle abdallah zuwa akinsa, Itama mami ta wuce nata akin tare da hajiya adama bayan tafiyar su. Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle an Iya ya fita waje domin amsa kiran da akayi mashi a waya Wlh ummi takalman afarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko ku insu yakai dubu talatin an zaro ido Ummi ta yi Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu ku i ne, ai naga sar ar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki sa a, Yarinya mai ashin arzi kwa6a fuska Zahra ta yi ni kuma mai ashin tsiya ko ? ummi na dariya tace Ni dai bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari yatsina fuska ta yi asa asa da murya ta furta Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamsha an masu ku i irin hajiya sarauta Aneelerh dake zaune saman carpet ta mi e ta koma saman sofa ta zauna Ummi ta kalleta nasan zasu bu aci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na marece za a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu, zahra tace Zan kira mahboob A waya ya je ya auko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada islamiyyar ba, ace kullum sai arfe shidda zai dawo gida, in banda weekend, Harara ummi ta an watsa mata Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai dai na bokon Girgiza kai zahra tayi Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi aranta brain insa ma arama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya auke duk abunda aka koya masa Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan asan zuciyarta kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba da i ita kanta ba ta son Yana kaiwa har arfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so yaronta ya saba da karatun boko dana addini. Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da uncle an Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya auro alwala kafin ya dawo suka unguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu Acan Cikin Gidan kowa ya koma aki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh Ya i kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu i tasha dogon hijabinta. Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya ameta Yana ti ar dariya babyn mommy is back Gabanta harya fa i sai da taji muryarshi tukunna ta sauke ajiyar zuciya, ha i da an sakin murmushi jin ya kirata da sunan da malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu ar, ta zagayo da hannunta ta ru o damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps inta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform in jikin shi riga ce fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai ar coat launin Ja, kafin ya ta fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi A hargitse ta ke. Idanuwanshi luhu luhu ya furta Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in daina smiling softly tace jirwayen menene akan fuskarka tai maganar tana nuna hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai mommy ai ni bake nayi ma kuka ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate ina da kika saka min a basket idanuwanshi cike tab da walla yai mata maganar, ranshi ya 6aci. aure fuska aneelerh tayi Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya Mommy don t worry, Ni ma ai na rama Dame ka rama da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun wandonsa, ya zaro aramin box mai kyan gaske Ya nuna mata Menene wannan ? Shu umin murmushi babyn mommy ya saki pls mommy kada ki yi min fa a, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu wannan, bu e ki gani abun da ke a ciki yai maganar yana mi a mata box din, bayan ta kar6a ta bu e akwatin, ha en zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone in jikin shi har yali Ya ke yi, Jinjina kai aneelerh tayi Lallai Mahboob Ya iya kashe na an mata ku i amma bai Iya kashe ma an uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace mai sa ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne Mommy daga ni sai ke, kada ki fa a mashi ni na auka, Mubar shi yai ta wahalar nema shima Ya ji idan akwai da Cikin 6acin rai ya ke yin maganar. Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box in nan ka 6oye mana shi cikin rigar pillow, kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya haye tare da ru o pillow ya zuge zip inshi Ya tura box in, abun mugunta ya samu sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga ewa ta yi daga saman sallayar, bayan ta cire hijab din jikinta ta tura a wardrobe, Baby junaid ta auka ta nufi toilet dashi, Wanka tayi mashi bayan sun fito ta auko mashi riga da wando na shadda, ta zura mashi kayan ajikin shi, ta feshe ko ina na jikin shi da turare bayan ta kammala gyara mashi sumar kansa ta auke sa suka nufi Palour, kafin su arasa sai da ta yi mashi hu uba akan ya natsu ya gaishe da kakanninsa kada ya bata kunya, ya amsa mata da toh, Lokacin da suka arasa palourn babu kowa duk suna a dining area sun hallara domin Cin abincin da aka shirya masu, dukkansu Ne a zazzaune saman dining chairs, zahra da Ana ke yin aikin zuba masu abinci. Farin Ciki a wurin Hajiya adama baya misaltuwa, shima Uncle abdallah sai murmushi yake saki ganin jikan nashi, Yayi matu ar tafiya da hankulansu, tun daga kan yadda ya zu unna kamar wani babban mutun ya gaishe da su, Hajiya adama ta auke shi Tana shafa sumar kanshi tace Masha Allah, Yaro kamar rainon turai, Jawur dashi atare suka ci abinci, tana ci tana bashi abaki, Junaid an samu jikin Granny, Ya ameta yana zuba mata shagwa6a shi ala dole ga jikallen Hajiya adama da uncle abdallah. Bayan sun kammala Cin abincin, aka fara kirayen kirayen sallar isha i, Mazan suka tashi domin zuwa masallaci. Shigowa cikin kitchen Mahboob yai fuskarshi a aure babu annuri, Ana dake a tsaye bakin sink tana wanke kwanukan da aka 6ata, Jin motsin mutun yasa ta waiwayo don ganin wanene, ganin mahboob ne atsaye sai ta saki fuska tana fa mahboob sannu da dawowa ashe kaine banji motsin shigowarka ba Yamutsa fuska yai muryarsa agajiye ya furta kin ban mamaki Ana, Yanzu hada ke aka ha a baki wurin yin almubazzaranci? Sai ka ce gidan Obinna abinci har kala Biyar? Ina laifin ko shinkafa da wake ne adafa masu In yaso sai a yayyanka masu kayan lambu asama ranshi a matu ar 6ace yake yin maganar, Fuskar Ana da alamun ru u take kallon shi Mahboob me kake nufi ? Hura mata hanci yai magana nake akan almubazzarancin girka abinci da ku ka yi saboda surukan Aneelerh dafe kai tai da hannu Pls mahboob ka daina magana kada wani daga Cikin su Ya fa o kitchen in ba tare da sanin mu ba, bansan meke damunka ba, menene damuwarka idan an girka masu abinci kala Biyar? Ko sisin ka babu acikin ku in girkin harara ya wurga mata tamkar wayar idon zata fa o kasa, rai a6ace ya ce Abar zancen, Zuba min abinci yunwa nake ji girgiza kai Ana ta yi kafin ta nufi dish rack ta auko plate ta zubo mashi dambun shimkafa, Ta mi a mashi, Matsiyacan kallo yabita da shi Shi ka ai aka girka? da mamaki akan fuskarta tace yanzu ka gama zazzaga min masifar almubazzaranci na girka abinci Kala Biyar, yanzu kuma ka ke tambayata shi ka ai aka girka? Dalla ni kar6i plate if not shima zaka rasa ne fuskarta a aure ta yi mashi maganar, hakan ba aramin kayar mashi da gaba yayi ba, sassauta muryarshi yai nifa wasa nake yi maki, dan Allah ki zuba min komai da aka girka yunwa nake ji, idan na gama cin abincin akwai wata kyauta da zanyi
Chapter 44 · 0% Book details