← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 106

Sashe 43

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka sanyasu yin al ajabi, tayaya har an ta addan ya iya guduwa dasu bayan asarsu tana da mugun tsaron da babu wani shege da ya isa Ya etare ta cikin Salama, Abu na biyu Ta ya ya an ta addan Ya iya aukar mutun mai mugun Nauyi irin matashin saurayin da suka gaza agawa? Abu na uku da ya aure masu kai Uniform in Jikin yaran masu auke da numbobi sunyi mamakin hakan. Suna Cikin yin tafiya, Zuciyar Gabriel na dakan uku uku tamkar zata faso kirjinshi ga kishirwa da ya ke ji, babban tashin hankalin shi Ina Su Batul suka kutsane a cikin Dajin? Ga dare yana shirin yi masu adajin, fargabansa kada sojojin su ce zasu tafi. Kana tunanin an uwanka zamu same su? Lokaci Yana ure mana Sojan ne yai mashi maganar, gabriel bai samu damar amsa mashi ba saboda tashin hankalin da ya ke aciki, Sai faman wurwurga wayar idanuwansa ya ke yi akan bishiyoyin dake a kewaye dasu, Suna Cikin yin tafiya suka araso gaban wannan ramin mai auke da ta6o, har zasu gifta shi Kwatsam Sojan Yaji ya taka wani abu, Da sauri Ya age afarshi yana kallon Warin Slipper in dake asaman ciyayin, Gabriel na ganin takalmin Ya zu unna tare da kai hannu ya auke shi, Gabansa ne ya fa i A gigice ya kalli sojan tare da furta Takalman ar uwata ne! Ya gane slippers insu ne Da tsohuwa Tamira tai masu kyautarsu, dama tunda suka shigo Dajin da takalmansu suke yawo a afafuwansu, shiyasa ko aya ba ta ta6a shigarsu ba. Dan Allah ka taimaka mun, wlh takalmansu Batul ne an uwana Muryarshi na rawa yake maganar, cikin agara. Waige-waige Sojan ya ke yi yana bin ko ina Na dajin da kallo, Kafin ya sauke idonshi akan Ramin ta6on, kasancewar Sojoji suna da warewa wurin sanin takan Daji, Nan take ranshi ya bashi cewar Ta6on da ke a wurin Ramine, mutun zai Iya rubzawa cikinsa, musamman wanda ke gudu cikin fitar hayyaci. Matsawa yai gaban ramin, Bayan ya soke bingidar hannun shi a ugun shi, Ya an zu unna saman afarshi, a tsanake Ya tura hannun shi Cikin ramin ta6o, Cikin sa a Ya dam o gashin aya daga Cikin su, matsar da hannun shi yai ya ru o Hannunta, Ya ago da ita gaba aya jikinta ya 6aci kaca kaca da ta6on baka Iya ganin komai na fuskarta, hatta Gabriel bai gane wacece a cikin su ba, A asa sojan ya kwantar da ita tare da ara zura hannun shi Ya ara cafko hannun wata ya curo ta, bayan ya kammala zaraso duka ukun Gabriel Yace mashi suke nan babu saura, Jin haka yasa Sojan Zaro wayarshi Ya sanar ma sojojin dake a bakin helicopter din cewa sun ara samu Yara Uku azo da stretcher a auke su, Cikin anin Lokaci sai ga sojoji sunzo da abun aukar, duka ukun suka aurasu saman shi kamar tsummokarai haka suka nanna Sojoji biyu ne suka tafi dasu zuwa Inda jirgin ya ke, Hankalin Gabriel Ya an kwanta sam ya manta da Haris saida suka kamo Hanya zasu Nufi jirgin ba zato ba tsammani su ka ci karo da haris a sume, Ba tare da 6ata lokaci ba, Sojan da suke atare Ya sa6e shi saman kafa a, suka nufi Jirgin Bayan sun Shiga su dukansu. Matu ar jirgin suka Tada shi, Da wata irin jijjiga tayoyin jirgin su ka soma motsawa suna yin tafiya sannu a hankali, Gabriel da ya kasance shi ka ai idon shi biyu, farin Ciki duk ya cika shi, sam baiyi tunanin wace asa za a kaisu ba, hankalin shi bai kai nan ba, fatan shi su bar dajin Cikin oshin lafiya. Bayan tashin jirgin sama aya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ofar helicopter in ne Ya kanga Tactical phone in hannunsa jikin kunnansa Yana magana Cikin Harshen turancin muryarshi na fita da amon murya saboda arfin iskar Dajin We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest. (Munyi nasarar cafke mai laifin, yanzu muna akan hanyar mu ta dawowa U.s, tare da yara goma sha aya da mu ka samu a dajin) Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya mi i hanyar komawa asar da ya fito. *Alhamdulillah Finally Ex-prisoners sun Bar Evil forest Fatan Nasara_~*BossLadiesWriters*~_ _*KURKUKUN ADDARA*_ _The Prisoners E12_ *Daga al alamin Boss Bature* ~Middle step~ _A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._ *GIDAN AN IYA* Gaba ayan su sun Hallara a bakin Entry hall na shiga palourn gidan, Mommy da Mami sun yi matu ar yin kyau cikin shigar Lace, Zahra da Aneelerh sai Abie da Uncle an Iya sun yi shiga ta alfarma, Bakomai ne yasa su fitowa ba fa ce tarbar Su Hajiya adama, A agare su ke da ganin ba in nasu, badajimawa ba su ka kira Aneelerh awaya su ka sanar da ita cewa sun shigo garin abuja, har ta tura masu da addrress in gidan. arar Horn in motarsu ne Yasa kowan nan su Sakin fuskarshi, da sauri mai gadi Ya fito daga akin sa, Ya je ya bu e masu gate. A hankali Dan areriyar Motar uncle abdallah irar Kia optima ta kunna kai cikin gidan kai tsaye ya nufi wurin Ajiye motocin su, bayan yai parking in motar, Ya fito daga ciki fuskar nan auke da annuri, ya auki wankan shadda gezna, afafuwanshi na asanye da patent leather shoes launin Shaddar shi, amshi ta ko ina. Zagayawa yai ta other side in motar ya bu e ma Hajiya adama ofa, afar ta ta fara zurowa nan take Zahra ta an zaro ido tare da kallon Aneelerh, murmushi gefen fuska Aneelerh ta sakar mata don ta fahimci abunda ya sa zahra mamaki, wato tsadar High hills in dake afar Hajiya adama. Zahra ta ware wurin sanin farashin Kaya, A kunne ta yi ma Aneelerh whispering Surukar ki Ta ji naira yasin, Takalman afarta kalar na saratu obinna ne girgiza kai Aneelerh ta yi ba tare data tanka mata ba. Lokacin da Hajiya Adama ta ara sa fitowa daga Cikin Motar ba aramin tafiya ta yi da imaninsu ba, saboda tsabar wa nkan kece rainin da ta auka na tsadadaddan Swiss cord lace launin brown mixed wit yellow, Riga da zani ne ta daura, kanta yasha aurin an kwali, sar ar wuyanta da awarwaron hannun ta, da zabbanta duk na zinari ne, ta yarfa mayafin kayan saman kafa arta, babu make up a saman fuskarta zallar kyan da Allah ya yi mata ne, Hajiya adama akwai kyau ga diri. Kallon abdallah ta yi fuskarta auke da murmushi, da hannu yai mata nuni da surukansu da ke a tsaye suna fuskantar su mu je ko? Sai lokacin ta lura da su, tafiya suka soma Yi a jere tunkan su araso Zahra take ta faman ingiza kafa ar aneelerh ki je ki tarbo su, kunya ta hana Aneelerh zuwa, har saida suka araso, Abie Yana dariya Ya ru e hannun Abdalla suka fara yin gaisuwarsu ta manya Marhaban marhaban lale surukai na gari, Sassannun ku, kun sha hanya, ku araso ciki Ya ja hannun abdallah, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su auke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta mi e mata hannu suka gaisa a mutunce Sannu da zuwa Hajiya, mu shiga daga Ciki ta yi maganar, tare da jan hannun hajiya adama wadda idonta ke akan Aneelerh, sai faman no e kai ta ke yi, Kunya kamar bafullatana, Ni kaina da nake bafullatana Bani da kalar kunyarki, da zolaya hajiya adama ta yi maganar, Yayin da su ke shiga cikin babban falourn gidan, dadda amshin turarensu ya gauraya da sanyin A.c. A saman soma mai mazaunin mutum uku Mami da ummi da hajiya adama su ka zauna, Abie da Uncle an iya su ka zazzauna saman 2 sita, Aneelerh tana zaune saman one sita, Yayin da zahra ta an zauna saman hannun sofa in da Aneelerh ke zaune, sai faman sakarwa juna murmushi suke Yi, Gaisuwa ta musamman suka ara yiwa junan su cikin girmama juna da mutuntaka. Uncle an Iya Yana faman washe baki Yace Abdallah Kai ne ka koma haka?gaskiya mun da e bamu ha u ba, tun lokacin da ka fito daga cikin mota, idanuwana su ka yi tozali da kai sai da gabana ya fa i araina nace ina muka samu ba in Bature, Abdallah hutu ya zauna maka daga kai har Hajiyar taka kun yada zumunci ko in ce mun yada zumunci Allah dai ya shiryemu dariya suka saki gaba ayan su. Ummi tace Ya gajiyar tafiya? Nasan Kun jigata sosai, tafiya daga jos zuwa abuja ba abune mai sau i ba, kun ma yi ari dana ganku da kuzarin ku mami ta aura da cewa Alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kare mana ku ya tsare mana ku har ku ka araso Lafiya, wannan abun farin ciki ne agare mu, gamu ga surukanmu, mutane masu ima da daraja, muna ara yi maku barka da zuwa Maganar Mami ta yi matu ar faranta zuciyoyinsu. Musamman Hajiya adama har saida ta an saki murmushin da ya bayyana jerarrun fararen ha oranta. A tsanake tace A gaskiya ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, ni dama tun da muka fito daga cikin mota raina Ya bani munzo gidan mutunci da karamci musamman da naji gidan Uncle an Iya ne Masha Allah, Fatan mun same ku lafiya atare suka ha a baki Lafiya lou Alhamdulillah Uncle abdallah ne ya soma yin magana cikin dattako da halin girma Mun jin da in samun ku cikin oshin Lafiya, Abun farin cikine wannan kuma muna godiya da irin tarbar da muka samu, Ina yi mana fatan kamar yadda muka ha u anan, Ubangiji Allah Ya ha amu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare suka ha u wurin furta kalmar SAW Yakamata mu fara yiwa annabi Salati Abie ne yai maganar, tare suka aga hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu i Suna amsawa da ameen ameen Bayan ya kammala, Uncle an Iya ya
Chapter 43 · 0% Book details