Sashe 79
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi alamar zaiyi fighting dinsu, lamarin ya aure masu kai, ganin sun sanya naci akan sai sun duba shi, Angel ta ro e su akan su yale shi zuwa gobe, fargabanta kada su haya a shi azo asamu matsala, tunda harya fara zare masu ido yana aure masu fuska. Ba don sun so ba, su ka yi masu sallama da niyar gobe zasu dawo, kusan atare suka fuce waje, aransu suna Ayyana irin kyawun fuskarshi da surarshi, sai santin shi suke Yi musamman nurses din cikin su. Su Uku Suka rage a akin, Nurse Jessica ta dubi Angel"na lura brother in nan naki, ke ka ai yake jin maganarki, Inaso ki tambayar min shi ko akwai abunda yake bu atar ci"? Kallon shi Angel Tayi, idonshi na akan plasma tv ta akin, sai an kalle kalle yake yi. "My man kana jin Yunwa"? Da budar bakinsa sai cewa yai"Ina haris da su Batul? Inason ganinsu" Kallon Nurse din Tayi"yace yana son ganin an uwanmu" gya a kai tayi"badamuwa Zamu Iya zuwa" Ru o Hannunshi tayi acikin nata"muje in nuna maka su" nurse jessica tana agaba suna abayanta, tun da suka fito daga akin Yake arewa ko'ina kallo, agogo ka ai mutun zai kalla ya gane cewa dare ne amma donta hasken light bulbs na asibitin ba za ka ta6a gane dare bane. Nurses in dake yin zarya da doctors sai satar kallon shi suke yi, hada masu yin tuntu6e. akin Haris suka Shiga, tun bayan fitar Angel bacci ya auke shi. Rabin jikinshi lullu6e da bargo, da sauri Danish ya arasa daga gefen gadonshi Ya zauna Yana kallon shi, nurse da Angel suna a tsaye suna dubanshi. "Bacci ya ke yi Danish, ko zamu bari sai gobe idan Ya farka mu dawo" aga mata kai Yai alamar eh, dama burinshi ya gansu hankalinshi sai yafi kwanciya, aura hannunshi yai saman sumar kan Haris ya shafata a hankali, tsantsar farin Cikine akan face dinsa' mintuna Biyar kafin Ya mi e, suka nufi akin Batul, ko da suka shiga, basu sameta a saman gadonta ba, nan fa hankalin Angel Ya tashi, "ina batul taje" nurse jessica harta bu e baki zata bata amsa, suka ji motsin fitowarta daga toilet, Kamar a mafarki take kallonsu kafin ta tsayar da idonta kan Danish, da arfi ta ambaci sunanshi, da gudun gaske fa arasa ta fa a saman faffa irjinshi, aura Hannayenshi yai saman bayanta sosai ya yi tighting inta, da i kamar zai kasheta, annurin fuskarshi sai ara nunkuwa yake yi, da alama yaji da in canjin rayuwar da suka samu. agowa tayi da kanta daga saman chest dinsa, ido cikin ido suke kallon juna, tuni hawaye sun cika idonta muryarta na rawa ta soma yin magana an uwana rabin raina, kaga canjin rayuwar da muka samu ko? Nasan Angel ta fa a maka komai, Danish ba zamu Iya misalta kewarka da mu ka yi ba, wlh naji da in farkawarka nayi farin cikin ganinka" a tsanake ya furta mata"nima nayi farin ciki Batul, Ina taya mu murna, ina yi mana fatan wannan ya kasance arshen wahalarmu" Angel da nurse jessica sai murmushi suke saki yayin da suke kallonsu. "Danish nasan za ka ji wani iri, nan ba kamar prison ba, inda aka untata rayuwarmu, tun muna Yara wannan ne karo na farko da muka fara tsintar kanmu awajen prison cikin mutanan duniya, Iskar da muke sha a a yanzu ta anci ce bata kurkukun addara ba" kalamai masu da i take fa a mashi "Muna samun kyakkyawar kulawa awurin mutanan nan" tayi maganar tana nuna mashi nurse jessica"sun bincika Lafiyarmu, kuma sun taimaka mana wurin samun sau i, sannan muna samun Cin abinci har sau uku arana, komai muke so sunayi mana, Ina fata kaima zaka saki jikinka da su sannan ka ba su ha in kai donsu duba lafiyarka, idan akwai wani abu dake damunka zasu taimaka maka wurin samun sau i in sha Allah, sannan idan kana Jin yunwa ka yi masu magana zasu baka abinci, ba sai kasha wahalar neman abunda zaka Ci ba..." muryarta na rawa ta arasa maganar, hawaye tuni sun cigaba da wanke face dinta aura tafin hannunsa yai saman face nata, share mata hawayen fuskarta ya soma Yi Calmly ya furta"its ok, stop shedding ur tears, ngde da shawararki, zan basu ha in kai," "Danish babu wasu kalmomi da zan Iya yin amfani da su wurin yi maku godiya kai da Angel, Allah ne ka ai zai Iya biyan ku, ha a kun taimaki Rayuwarmu kun gatanta mu, kun yi mana silar barin mu kurkukun addara, duk wani cigaba da zamu samu a duniyar nan kune sila, ba zamu ta6a mantawa da halaccin ku agare mu ba, kun fiye mana iyayenmu sau dubu, matsayin da suka rasa awurinmu kune kuke ru e da shi...." sosai ta fashe masu da kuka, Janyota yai zuwa saman chest dinsa ya ara yin hugging dinta yana lallashinta. Da yar ya samu Batul ta dakata da yin kukan, bayan ya raba ta da jikinsa, ta rungume Angel sosai suka ame juna, tsawon mintuna kafin suka raba jikinsu. "Allah yabar Mana ke, Our Super star, Allah ya cika maki burikanki dake da Danishi inmu" murmushi kowan nan su ya saki, sun an jima a akin Batul kafin suka Yi mata sallama, Sauran aku nan su Azeeza suka shiga kowan nan su bacci ya ke yi, Ya ha ura sai zuwa gobe zai gaisa da su. Komawa akinshi su ka Yi, nurse jessica tace da Angel, zata kawo mashi Abinci, kafin ta dawo ta taimaka mashi Ya shiga toilet ya gyara jikin shi, amsa mata tayi da toh, Bayan fitar nurse in, Taja hannun Danish suka shiga toilet, tun da suka shiga yake bin ko'ina da kallo, Karaf Ya aura Idonshi Kan madubin toilet din A firgice taga Ya Juya mashi Baya. "Danish meya faru"? Hankali atashe tayi mashi Tambayar "Bana son ganin shi," ba ta yi mamakin jin abunda yace mata ba, tunawa da ranar da tsohuwa tamira ta basu kyautar madubi, kowa ya duba fuskarshi, amma shi Ya i Yarda ya kalle shi. Dubara tayi wurin Cire Hijabin jikinta, taje gaban mirror in ta lullu6e shi. "Nayi maganin matsalar Juyo ka gani" a hankali Ya juya yana kallon mirror din nan take ya sauke ajiyar zuciya, ganin ta rufe madubin. "My Man, Ka fara Yin wankan, almost one week jikin ka bai ga ruwa ba, I'll wait for you outside." Akan idon shi ta fuce, a bakin ofar toilet din ta jingina Bayanta tana jiran fitowarshi, ta kasa kunne tana sauraron motsinshi, da i take ji kamar wadda akayiwa albishiri da gidan Aljanna, a alla ta sauke ajiyar zuciya yafi a irga fatanta Allah yasa subar america batare da sun samu wata matsala ba. Gaba aya hankalinta baya atare da ita, gangar jikin ce ka ai, ruhin Yana atare da Danish dake acikin toilet, har Nurse jessica ta shigo akin hannunta ru e da food trolley, ta gunguro shi zuwa gaban table, murmushi tasaki tana kallon Angel dake ma ale jikin toilet door, aranta ta ayyana ko dai soyayya ce a tsakaninsu, don wannan sha uwar tasu tafi arfin a kirata da abokantaka. Bayan ta araso gaban table din, ta soma jera kayan abincin saman shi, har ta gama jera su, ta juya da food trolley din duk Angel bata lura da ita ba, Har ta fuce daga akin. Jin motsin bu ofarshi, Yasa tayi saurin komawa gefen gado ta zauna tana faman sakin murmushi kamar wata zautacciya. Zuro afarshi yai saman carpet dake gaban ofar shiga toilet in, Kafin ya arasa fitowa, jikinsa da danshin ruwan wanka da yai, Ya maida uniform dinsa da aka sanya mashi. Tun ya fito idonshi na akanta, ya lura da tsantsar farin cikin dake akan fuskarta, Hakan ba aramin da i yayi masa ba. Gefenta Ya zauna yana are mata kallo "Na fito" sai da ya ambaci hakan tukunna ta ago suka ha a ido wani irin asirtaccen kallo suke jefa ma junansu kamar zasu ha iye kawunansu tsabar auna. Lokaci aya ta samu kanta da jin kunyar shi, Muryarta adabarbarce ta furta"am..um.. Ga abincinka da nurse ta kawo nasan kana jin yunwa" ta yi maganar ha i da nuna mashi table din, aura idonshi yai akan kayan abincin kafin ya dawo da dubanshi gareta"baki jin bacci? Naga sauran an uwanmu suna yin bacci, ta hakan na fahimci dare ya nutsa" Ma e mashi kafa a tayi"bana jin bacci, inaso na zauna a kusa dakai, don na taimaka maka da wasu abubuwan, tun da yau ka farka ba ka san komai dangane da wurin nan ba, bana so in tafi in barka kai ka ai a room" natsuwa yai yana kallonta, har ta are maganar tukunna ya furta mata"nagode da kulawarki agareni, kuma nagode da nuna damurki akaina" still murmushin fuskarta bai washe ba "Zamu ci abincin atare? Ko kin ci naki"? Yai tambayar yana duban fuskarta, Yafi son tana kallon Cikin idonshi idan suna magana. "Bana jin yunwa, amma Zan Iya taimaka maka ka ci naka" amsa mata yai da"okey, " mi a hannu tayi tana bu e plates din, lafiyayyan abinci aka ha a mashi Grilled chicken with roasted vegetables, and black bean burger with sweet potatoes fries, hada Green tea a mug. "My Man, komi da ka gani a saman table in nan duka sai ka cinye shi, yadda kasha baccin nan na tsawon kwanaki nasan cikin ka babu komai ko ruwa ma babu, yanzu fa amin me ka ke son fara ci? Cikin kulawa take yi mashi magana. "Ki za6a min" murmushi ta sakar mashi, Mug din ta mi a mashi, Yasa hannu biyu ya kar6a, a tsanake yake kur6anshi da zafi zafinshi, idonshi na akan face dinta, ta urawa adam's apple dinsa ido. Batasan Ya janye cup din ba sai dai taji muryarshi acikin kunnanta"me kike kallo"? Yamutsa fuska ta anyi"bakomai, tun da ka gama shan tea din, zaka Sha ruwa? Ko lemu"? Girgiza mata kai yai"a'a, tea din ya ishe ni, sai dai wani abun" Kamar wani aramin yaro haka take tarairayarshi, da hannu ta dinga bashi grilled chicken din yana ci, Idan ka kallesu a yadda suke zaune sai ka sha mamaki saboda girman da yai ma