Sashe 51
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sojojin sun bar asibitin da niyar idan sauran Yaran suka farfa o daga bacci Ayi hanzarin kiransu da gaggawa don suna bu atar ganawa da su. Nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel ya sauke tun bayan fitarsu yake ta sakin murmushi ba in shi ya i rufuwa, tuni hawayen farin ciki sun wanke fuskarshi bakomai yake tunawa ba fa ce twin sister insa da sauran an uwansu da suka rasa rayukan su a kurkuku, Ya ji ra in Rasa su da su ka yi da yanzu duk atare zasu ji da in rayuwarsu, don yana ji aranshi arshen wahalar su ce tazo, babban burin shi a yanzu sauran an uwansu su farfa o, Yasan zasuyi farin ciki Mara misaltuwa, fatan shi Allah yasa Idan Angel ta farfa o Ta yi ari wurin yin magana da sojojin cikin hikma yadda zata yi masu hanyar komawa gidan daddynta ko dan saboda azeezarshi da ta wallafa rai da son zuwa can. Yayin da ya ke yin tunanin, hawaye basu daina yin sintiri akan fuskarsa ba, a saman pillow ya aura kansa, ga sanyin A.c dake ratsa jikinsa. Motsin bu ofa ya ji da sauri ya an yun ura ya mi e zaune yana kallon mai shigowa ciki, Matashiyar Nurse in da ta kawo masa abinci ce azu, Fuskarta auke da murmushi agaban gadon ta tsaya tare da goya hannayenta saman irjinta Fuskarta da murmushi ta soma magana "Hello, I'm Sister Rebecca, May I know your name?" Da yar ya iya bu e baki ya furta suna shi "Gabriel" jinjina kai nurse rebecca tayi a wayance tace "It's wonderful to meet you, Gabriel. How is your body? I hope you're feeling better now," Rashin sabo ya hana ya saki jiki da ita, cikin rashin natsuwa yake amsa mata. Ganin yadda take sakar masa fuska yasa shima sakin tashi fuskar "Is there any part of your body that's hurting?" cikin kulawa ta yi mashi tambayar. Girgiza mata kai yai"A'a lafiyata alau" "Okay, is there anything you need?" again ta ara tambayar shi. asa asa da murya ya furta "No, thank you." "Okey, ko akwai wani abu da kake bu ata"? Shiru ya anyi yana faman wurwurga eye balls dinsa akin Ya ke bi da kallo Ganin kamar tv yake kallo yasa tace" "Would you like to watch some TV?" Numfasawa yai tare da mayar da idon shi akanta "I wanna see my brothers, I want to know how they're doing." "Please, don't worry, Your relatives are in good health and we expect them to wake up soon." da sauri ya tari numfashin ta "Can you help me go to their room to see them?" A agare yai mata maganar "Don't worry I'll take you to see them but first you need to rest. You've traveled for hours, and you must be tired. I'll turn on the TV so you can relax, and if you need anything, you can use the phone to call me." ta yi maganar tana nuna mashi wayar dake ajiye saman table na gefen gadonshi "Ga kuma ofar shiga toilet idan kana bu ata" duk abunda ta yi mashi bayani saita nuna mashi da hannu Bayan ta kammala, Taje gaban plasma tv dake manne jikin bango ta kunna mashi tashar da ake wasan wallon, don tasan mafi akasin maza sunfi sha'awar kallon wasan wallo, irji ya rungume pillow yana kallon tv in, fuskar nan auke da annuri banza ta samu an samu anci, Yadda nurse in ke tarairayarshi kamar wani aramin yaro da bai wuci shekara goma ba. Kafin barinta akin saida ta auki Kayan abincin da ta kawo mashi ta fuce da su robar lemun da bai sha ba ka ai ta bar mashi, Hannu ya mi a ya auke ta, Yana sha Yana kallo Hankalin shi kwance gwanin ban sha'awa *The prisoners Middle step Wuraren arfe goma sha Biyu agogon birnin san antonio ta buga, adai dai wannan lokacin sambatun muryar Angel ya cika akin da aka kwantar da ita, tana akwance saman ha en gadon, patient's gown ce a jikinta launin ligh blue, drip in da aka sanya mata tuni ya jima da arewa, zazza6in jikinta ya sauka temperature inta ya dai dai ta. Muryarta na kakarwa take ambaton sunan danish, Shi ya tsaya mata arai shiyasa take sambatun ambaton sunansa, duk da sanyin A.c na akin hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, zucyarta na harbawa da arfi da arfi "Danish ina kura ta cinye min shi, wayyo Allah Danish ina na shigo uku munbar Danish Gabriel kura Zata kashe min shi....." tuntana sambtun a hankali har takaiga ware murya da wata irin firgita Ta ware Gray eyes dinta ta zazzare su akan ha en ceilling akin, Sam bata acikin Hayyacinta, bakomai take gani acikin idanuwanta ba face Fuskar Kurar da ta biyo su A daji tana gurnani, gizo take yi mata, A gigice ta zabura har batasan ta fisge iv line in dake hannunta ba, durowa daga saman gadon tayi Hannayenta bibbiyu daddafe da kanta, Tsantsar tashin hankali ne akan fuskarta, duk tabi ta furgice, doguwar sumar kanta har saitin gwiwarta gaba aya ta hautsine gashin kan tamkar na mahaukaciya, Sam bata acikin hayyacinta batasan A ina take ba? Daji kawai take gani a idonta Sosai ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, idanuwanta sun makance,, Da gudun gaske Likitoci suka fa akin da take a ciki, Dama jiran farkawarta suke yi, wasu daga cikin an uwanta sun farka acan inda aka kwantar dasu, Sun rasa gane kan Yaran tsabar tsoro da firgici Jikin su sai kerma ya ke yi sunga mutanan da basu saba gani ba, duk wanda yai yun urin tunkararsu ara suke fasawa tamkar ana zare ran su, Kalma aya su ke iya ambato abakunansu Sunan Angel wannan yasa Likitocin su ka ara da ta farka, don sun fahimci ita ka aice zata Iya sarrafa su. Sam bata ji motsin shigowarsu ba, Sai dai ta ji muryoyinsu akanta, Nan fa hankalin Ta ya ara tashi, A firgice ta waiwayo tana binsu da kallo tun daga asa har sama, Waro idanuwanta waje tayi tamkar wayar zata fa o kasa, jijiyoyin wuyanta sun fito ru u ru u, tsantsar tashin hankaline akan fuskarta da ru ani, sai lokacin ta soma tunanin wai ma A ina take ne? Ya akai ta tsinci kanta a wurin nan? Wanene Ya kawota? ina an uwanta suke? Su wanene wa annan masu fararen Kayan kamar likitoci ne"? Wahalallan Yawu ta ha iya, zufa duk ta wanke fuskarta da jikinta, yadda kasan wadda ta yi tozali da aljanu, ganin komai take yi tamkar a mafarki Cikin kwantar da murya su ke yi mata magana don sun fahimci arikice take babu natsuwa atattare da ita "Ki kwantar da hankalin ki, Dukanmu nan da kike gani likitoci ne, mune masu kula da lafiyarki, Sannan anan inda kike Asibitine....." Ras taji gabanta ya fa i Cikin sar ewar murya ta soma motsa small lips inta "Ban...ban..gane ba wanene ya kawo ni nan? Su wanene ku kuma Ina an uwana su ke"? Kallon tuhuma take binsu da shi gani take yi kamar mugaye ne. an uwanki suna nan Cikin oshin Lafiya, idan kika natsu zamu Nuna maki su, wata' il hankalinki ya kwanta" ma e mashi kafa a tayi"wlh bazan yarda daku ba, so kuke ku cutar dani, Ni ku fa amun Ina danish ina yake da sauran an uwana....." cikin disasshiyar murya tayi maganar hawayen nabin fuskarta, ganin suna matsowa kusa da ita aiko da sauri ta dinga ja da baya tana girgiza masu kai, ha i da zazzare masu ido don karsu ta6ata Hakan yasa suka dakata da yin tafiyar, turo ofar da akayi ne yasa gaba ayansu suka juya don ganin wanene Nurse rebecca ce Ta shigo akin hannunta ru e dana Gabriel, Wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi ganin Angel, Ita ko ta runtse ido, Masifa kawai take Ji, da arfi Ya ambaci sunanta"ANGEL!!" Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnanta, Kamar an tsunkuleta Ta bu e ido Tana faman zazzaresu Akan fuskokinsu, da gudu gabriel Ya arasa gabanta, Gaba aya ya rungumeta Yana dariya, A alla ta sauke ajiyar zuciya yafi a irgita, ame shi tayi tamkar zasu koma mutun aya. Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirkon suna kallonsu, murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, tamkar sun samu tv. Raba Jikinta Tayi daga na Gabriel Muryarta na rawa take fa in"Gabriel wanene ya kawo mu nan? Pls ka fa amin Aru e nake bangane komai ba, Ina danish dina da sauran an uwana? Ru o Hannayenta yai acikin nashi"Angel mun tsira! Mun ku6uta daga kurkukun addara da Evil forest......." a tsanake Gabriel Ya kwashe komai Ya sanar da ita, Cikin harshen hausa, hakan yasa Doctors din basuji me yake fa a mata ba. Maimakon tayi dariya Sai gani suka yi ta rushe da matsanancin kuka, abunda da ya aure masu kai, tana kuka tana dariya a lokaci aya, slowly ta zube saman gwiwowinta, tare da aura goshinta saman tiles, Sujjada tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan ranar da suka da e suna Jiranta! *Boss Bature Mu ha u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details_~*BossLadiesWriters*~_ _*KURKUKUN ADDARA*_