Sashe 104
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shu'umin murmushi tace min bataso inyi danasani, don tasan banda arzi in da zan Iya biyanta, tasan wanene mahaifina karen an siyasane sai yayi masu wahala suke watsa mashi hatsin da zai samu ya tsastsaga harma ya an mana, raina ya 6acin sosai jin irin wula ancin da take yi mini nasan nina ja ma kaina, dama ance kwa ayi mabu in wahala, sannan idan har kace zaka dogara da wani kana tare da wahala, sai dai ba yadda zanyi ne tun farko da nasan wacece ita wlh daban amince ta bu e mana company ba, da yar na samu ta yale ni abisa sharadin gobe da safe arfe 7 tana jiran alert na ku inta, wlh idan daddy yaji maganar nan sai ya kusa kasheni, ni bansan ya zanyi ba" Zuciyar Aneelerh tayi matu ar karaya, tayi mamakin Hajiyarsu zahra me halin bunsuranci. "har nawa ne kudin"? Zahra na matsar walla tace"kusan fa miliyan shidda muka raba ni da fatima" Zaro ido waje Aneelerh tayi tana mai jinjina kai tace"tab ijancan, ashe da rabon zahra ki kwana a cell, don kuwa babu abunda zai hanaki zuwa gidan Yari, Ni har na hangoki cikin uniform dinsu" fashewa zahra tayi da kuka jin abunda aneeelerh take fa Cikin shesshe ar kuka tace"Aunty aneelerh kidaina banso, bakisan halin da nake aciki bane shiyasa kike zolayata, wlh saboda tashin hankalin da nake aciki tun safe ko ruwa ban sha ba" Tsananin tausayinta ne Ya kama Aneelerh, idanuwanta sunyi jawur dasu kamar an watsa mata barkono, muryarta na rawa tace"Aunty aneelerh ko zaki taimaka mini mu je mu nemo wanda zai sayi motata da wayata kafin lokacin Ya cika" Jikinta na kerma tayi magana. "Lokacin da ku ka yi yarjejeniyar bu e companyn kinyi shawara da wani? Ina nufin Uncle ko Ummi akwai wanda kika fa a mawa"?! Girgiza kai zahra tayi"Ni ban fa a ma kowa ba, babu wanda ya sani, kawai dai na fa a masu na samu aiki a company, sun tayani murna kuma sun yi min fatan akhairi, ummi ma ta ta6a tambayana ya akai companyn yaci sunana? Kamar nawa, sai nace mata banawa bane, Yarinyar me companyn ce takwarata shiyasa aka sanya mashi Sunan Zahra world of beauty" Jinjina kai Aneelerh tayi"Kinyi babban kuskure Zahra, Matar nan Tayi maki wayau, Nafi ganin laifin ki, ke fa da kanki kikace kinsan halinta masifaffiyace amma ahaka kika biyewa fatima ku ka kashe ku i har miliyan shidda bayan kinsan ba gadon an iya bane, Idan ita yarinyar bata da wayau ai ke da hankalin ki, kuma ita dukiyar mahaifiyarta ce, ke kuma fa? Baki ha a komai da ita ba,Yanzu ai gashinan taja maki bala'e, ko dai ki biyata ku inta ko ta maka ki kotu, Ni dai shawarar da zan baki shine kije ki yi mata abun da take so!" hankali akwance aneeelerh tayi mata magana, tayi tsammanin zata taimaka mata ne donsu nemi mafita amma sai taji tana fadin hakan, zuciyarta ta karaya sosai, har batasan sa'adda ta fashe da kuka ba, ta sauko daga saman kujerar ta zube saman gwiwowinta Cikin shesshe ar kuka take fadin"Na shiga uku aunty aneelerh, amma dai wasa kikeyi mini ko? Ni nasan bazaki ta6a bani shawarar in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, wallahi ina tsoron Allah, Ina tsoron ranar da zan koma gare shi" aure mata fuska Aneelerh tayi"Idan har baki amince mata ba zahra tayaya kike tunanin zaki Iya biyanta? Kinsan halin mahaifinki bazai ta6a biya maki kudin nan ba, Ummi kuma bata da ku i, zahra wara ki bata ha in kai, nayi maki al awarin babu wanda zai ji abunda ya faru, daga ni sai ke, kinga tace zata ara maku wasu kudin harma tasa ayi maku order na kayan da zaku yi amfani da su daga dubai, wallahi zahra ki amince mata idan ma don baki saba bane zaki saba a Hankali, Allah kuma gafurirrahim ne, zaki iya tuba ko daga baya ne in ta gama amfani dake" Zazzare ido waje zahra tayi yayin da take kallon Aneelerh, cikin matsanancin tashin hankali da ru ani, Muryarta na rawa ta furta"Aunty Aneelerh dagaske kike? In bata hadin kai"? Murmushi Aneelerh ta sakar mata hadi da aga mata gira alamar eh, girgiza kai zahra tayi idanuwanta cike tab da walla tace"wallahi aunty Aneelerh bazan Iyaba, koda kuwa duniya zata mallaka mini don in biya mata bu atarta bazan ta6a amincewa ba, da in sa6ama Allah na wammace in rasa komai dana mallaka don In biyata ku in ta, ina tsoron Allah kuma ina jin tsoron ranar da zan koma gare shi, yanzu idan na mutu kafin in tuba fa"? ta fa a yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta, kallon da take bin Aneelerh da shi, kallone na mamaki da al'ajabin shawarar da ta bata, har ta fara kokwanton Anya kuwa Aneelerh ce wannan? Ko dai Aljanu sun shige ta ne? a kai Zahra tayi cikin rauni na murya ta furta "Aunty Aneelerh ki daina wannan maganar kina rikita mini tunanina, idan har ba zaki taimaka mini mu nemi mafita ba bai kamata kina tunzurani akan in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, har kin sa nafara kokwanto akanki duk da nasan wacece Auntyna" Ta6e baki aneelerh tayi ha i da watsa hannayenta tace" Zahra, we don't have any other solution besides this, ina ara jaddada maki, ki hanzarta zuwa ki biya mata bu atarta, idan ba haka ba zata kai arar ki kotune sannan ta rufe maku companyn ku, amma idan kika bata hadin kai, kinga zaki ci riba biyu da farko zata yafe maki bashin da take bin ki, na biyu kuma zata yi maku order na kayan amfani daga dubai, wannan fa babbar dama ce agare ki!!!" da sauti mai arfi ta arasa maganar, fuskarta babu annuri, ta yun ura ta mi e tsaye, Zahra ta saki baki tana kallon ta da rinannun idanuwanta. "Ni kinga tafiyata, Idan kin canza ra'ayin ki kina iya zuwa aki ki same Ni, zan taimaka maki da mayukan da zaki gyara mata jikin ki" ta hanka e kafa a ta juya ta nufi kofar fucewa daga akin. Kamar sakarya haka zahra tabi bayan Aneelerh da kallo har ta 6ace ma ganinta, hannu biyu ta aura saman kanta, tana faman ambaton kalmar Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un" Tsantsar tashin hankaline akan fuskarta, wani irin azababben zazza6ine ya lullu6eta, saman floor ta kwanta, idanuwanta na fuskarta ceilling, yau Aunty aneelerh ta bata mamaki, ta karya mata zuciya, duk da har yanzu ta kasa yarda da abunda zuciyarta ke fa a mata dangane da ita, batasan ya zatayi ba? Don ita har ga Allah bata jin zata amince da shawarar Aneelerh ta wammace ta tattara duk wani abu data mallaka taje ta biyata ku inta zaifi mata kwanciyar hankali akan ta sa6a ma Allah, tazo tana danasani mara amfani, babban abunda take jima takaici asarar da zatayi na zuwa gidan Obinna, On friday na satin da suke ciki Za'ayi shagalin birthday na babansu, already sun fidda masu anko, decoration ne da kitso suke bu atar ayi masu jibi, tasan tarasa wannan damar, Hajiya falmata baza ta bari ta cigaba da yin aiki a companynsu ba muddin bata amince da bu atarta ba, gashi ita bata da komai, dole ta ha ura tama riga da ta fidda rai, shawarwari ta shiga yankewa da zuciyarta, a karshe ta yanke shawarar Zata yi magana da mahboob watakil ko cikin abokanan sa asamu wanda zai sayi motarta da wayarta, da wannan tunanin baccin wahala ya auke ta, babu ci babu sha tun safe baiwar Allah. *DAULAR OBIE ESTATE* Zayn ne kwance saman shimfi en gadonsu, daga shi sai short a jikinshi, tun da suka dawo daga office yake ta sharar baccin shi kamar matacce, toilet door din akin aka bu e Zaid ne Ya fito waist dinshi aure da towel, jikin shi da alamun danshin ruwan wankan da yayo, tun kafin ya arasa gaban gadon ya soma ambaton sunan zayn. "Bro, get up, I want to have an important talk with you, please," ya fa a ayayin da yake okarin zama gefen gadon, hannu yakai yana bubbuga afarshi"pls ka tashi zayn, baccin ya isa haka sai kace mai sleeping sickness, tun da muka dawo daga office kake ta sharar bacci ko dai ka sha waya ne"? Ya fa a yana cunkulin kafar zayn da mugunta, dogon tsoki Zayn yaja, yana faman yamutsa fuska ya furta" "Zain, I don't want to be stressed, please, let me rest, I'm tired," Rai a6ace yai maganar ba tare daya bu e idanuwanshi ba. Zain na murmushi yace"Haba babyn mommy, you should wake up, you've had enough sleep. I know it's not just work tiredness that made you sleep, because your secretary told me that you're not doing anything other than gathering girls in your office. Ko nayi arya?" He spoke jokingly, looking at Zayn's face, tamkar bai ji me yace ba, Ya ha e fuska babu annuri. "Dole kayi shiru, tun da baka da abun cewa, adai dinga jin tsoron Allah, ta amarka kana da kyan fasali shiyasa kake ma ure an matasan mata a office kana zare masu ido, don kasan dole suyi maka biyayya tunda suna aiki a ashin ikon ......" bai arasa maganar ba, sakamakon zaburar da zayn yai ya mi e tare da dam ar pillow, ya buga mashi akai, Ya janyo wani pillow ya dinga bugunshi ta ko'ina, Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yake fadin"zaid ka takura ma rayuwata, kai ma ka sani wallahi nafi arfin in ma ure an mutane a office, Ni bana yima mace dole in ba ita ta nuna tana bu atana ba, kai ne dai bunsuru da baka Iya gani ka kauda idonka, Ni da aji na matane suke kawo kansu wurina bani nake kiran su ba" ya fa a yana hararansa"shashasha kawai mai kama da daddy" Ya are maganar Yana haki kamar wanda yasha gudu, idanuwanshi sun ka a jawur saboda baccin da bai ishe shi ba. "Zayn? Ni ne bunsuru? Kuma mai kama da daddy? Kana nufin shima daddyn mu bunsurun ne"? Fuskarshi a aure yayi maganar. aga mashi gira zayn yai" arya nayi ne? Babyn daddy, Nifa ba ina nufin bunzuru na dabba ba, No,