Sashe 3
Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eyyah Hakane ashe, " jinjina kai Angel tayi"dama ni tun ina agida idan na ci abincin da aka ha a da ganye zaucewa nake yi, Bana son Cin ganye yana affecting ina" Fuskarta amarairace ta yi maganar. Shiru tsohuwa zafreen ta yi a yayin da ta ke are masu kallo kamar tana son gano wani abu da ke 6oye akan fuskokin su sai dai Allah bai bata ikon fahimtar komai ba, Abun da ya aure mata kai yadda su ke yi mata magana ba tare da jin shakkarta ba. "Da za ki bamu dama Yau na rana aya kawai, Ki zauna muyi fira da ke, A matsayin ki na kakarmu....." gaba aya sun ru ar da ita, sai kallonsu take yi tana faman jinjina kai kamar adangaruwa Sun kashe mata bakin magana, A hanzarce ta juya ta nufi bene Giants dake take mata baya suka juyawa tare da bin bayanta, Suna jiyo sautin rufe ofar akinsu, Gaba aya suka daka uban tsalle tare da rungume junansu fuskokinsu auke da farin Cikin nasarar da su ka yi akanta, yau sun kashe tsohuwa zafreen da mamaki "Alhamdulillah Ya Allah, Mun gode da taimakon ka agare mu, " Angel ce ta furta hakan. "Mun ji jiki yau Allah, ba kiji yadda gaba na ke fa uwa ba, tun da ta shigo hankalina ya i kwanciya" acewar Yasmin, Hibba tace"Ae ba ke ka ai ba, ni kaina iris ya rage in saki fitsari a wando, matar can bala'e ce' Kowa yana tofa albarkacin bakin shi "Amma wai ya akai da ta shiga toilet din bata ga komai ba? Kuma har ta ga Tukunyar fulawar"? Naufal nai yai tambayar mamaki ya ishe shi "Ae Allah muka ro o shine ya makantar da ita, shiyasa bata ga komai ba" Deeja ce tai maganar, "Pls kudaina maganar nan kada Suji mu tunda suna ganin mu, Inaso mu yi magana amma dole mu jira zuwa anjima idan marece Ya nutsa, sai mu shiga sashen toilet dinmu saboda idan su ka ga zaryar Tayi yawa zasu fahimci wani abu" Atare suka hada baki wurin furta mata "Toh" "Yanzu kowa yaje ya kwanta, Inaso ku huta, kafin zuwa anjima " aya bayan aya suka nufi gadajen su tare da haye saman suka kwakkwanta, Mutun uku ya rage a tsaye, Zuciyoyin A cunkushe suke da tunanin taya zasu Iya 6alle murfin ofar nan? Taya zasu iya Gano Danish? Fatansu Allah yasa adawo masu da shi ba tare da sun sha wahala ba, A tunanin su Haris kenan su da basu san komai game da zamanshi giant ba. Mutun uku da suka rage atsaye Gabriel ne sai Batul tare da Angel, Sun i tafiya ga dukkan alamu suna bu atar jin wani bayani ne daga gare ta. Kallon su ta anyi kafin ta soma magana "Gabriel nasan me ka ke son ji, Ka ara ha uri zan yi maka bayanin komai" amsa mata yai da toh tare da juyawa ya nufi gadon shi. "bugun zuciyata me kike tunani ne"? Lumshe ido batul ta yi tare da ware su kan fuskar Angel"har yanzu ban fahimci komai ba, dangane da abunda ya faru da an uwana Danish, hankalina bai kwanta da abunda kika fa a mini ya faru dashi," Matsawa Angel tayi kusa da ita sosai har numfashinsu na kokawa dana juna "Kin damu dashi"? Jinjina mata kai tayi alamar eh, ta ara da cewa"taya bazan damu dashi ba Angel, bakisan yadda nake jin shi acikin zuciyata ba, da ace ina da hanyar da zanbi inje gare shi nothing would stop me from going." Angel ba ta yi mamakin jin abunda batul tace mata ba, saboda sanin irin sha uwar dake a tsakaninsu, Hakan yasa ma ta i sanar da ita cewa Ya zama Giant, gudun kada ta sanya damuwa Ruwan hawayen da ya taru acikin idonta ne yaci gaba da gangarowa "Ki kwantar da hankalin ki bana son kina shedding tears din ki, Ko dan saboda farin Cikin ki zan yi ari wurin ganin Danish ya dawo gare mu," kwantar da kanta tayi saman kafa ar Angel taci gaba da yin shesshe ar kuka tana fa in"Amma ai bashi da lafiya, An cire mashi ido aya, bansan awani hali yake ciki ba, " "Ki daina kuka batul so kike hankalinsu Ya ara tashi? Nace ma ki lafiyar shi alau shi da kanshi Ya fa a mini cewa babu abunda ya samu idonshi" lallashinta Angel taci gaba dayi har saida ta samu ta lafa, Abun da ya aure ma Angel kai, zazza6in da taji a jikin batul lokacin da ta kwantar da kanta saman kafadarta, Jikinta zafi sosai. Hannayenta biyu ta aura saman shoulders in batul, ta ago da kanta, Idanuwansu acikin na juna, "Baki da lafiya ne?naji jikin ki da zafi"? Muryarta adisashe ta ce"Lafiyata qalou, idan ma bani da lafiya damuwar rashin Danish ne" shiru Angel tayi kamar an auke mata sautin muryarta, ta rasa tunanin me za ta yi, Ru o hannun batul tayi acikin nata Calmly tace "You need to take a bath, mu je in raka ki toilet, girgiza kai batul tayi"A'a bana iya wanka, nafi so na kwanta zuwa anjima idan na tashi zanyi," a kai Angel tayi"shikenan muje mu kwanta da anjima nima zanyi wankan" Atare suka nufi gadajen su, tafiya su ke yi kamar wa anda aka zarewa laka, babu kuzari a jikin kowaccensu, Ita dai Angel akwai wani abu dake damunta acan asan zuciyarta, Fatan ta Allah yasa hasashenta karya zama gaskiya don kuwa ba aramar matsala za'a samu ba. Ta yi niyar ta kwanta asaman Gadon Danish ganin Jemimah kwance saman nata gadon, sai dai kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta batul ta riga ta kwanciya saman gadonshi, da ido ta bita da kallo ganin ta rungume pillow dinshi a irjinta tare da lumshe idanuwanta, Jiri Angel ta gani acikin idanuwanta kamar zata fa i kasa adaddafe ta nufi gadonta da yar ta haye gefen jemimah ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya, lokaci aya ta ji yanayin jikinta ya canza zuwa zazza6i, hakan yasa ta soma ambaton sunan Allah, sama sama ta fara jin bacci yana fisgarta har ya ci nasara akanta sosai ta nutsa tana bacci............... akin ya yi tsit babu mai magana a cikin su, kamar masu bacci alhalin kuwa likimo su ka yi, sai da marece ya nutsa Angel ta umarce su akan su je su yi wanka saboda wunin ranar jikin su baiga ruwa ba, ba tare da 6ata lokaci ba kowannansu Yayi wanka, ta auko masu sababbin uniform insu kowa ya zura nashi a jikin shi, tsaffin kuma suka cire su Angel ta kar6esu ta ninke su ta ajiye saman table. Lokacin da dare ya gabato, dubara su ka yi wurin kashe Floor lamps in da ke a asan akin su, Duhu Ya mamaye idanuwansu, saboda sabon da su ka yi da akin yasa su ke iya gane hanya ko a cikin duhu, Kamar yarda Angel ta tsara masu mutun Uku ne zasu Ha a masu kayan su A cikin akwatin da zasu gudu da shi, Rai da burin sufa shirin matafiya su ke yi tun kafin su gano Makullin Bu ofa, Babu wanda yai bacci acikin su Hatta Jemimah idonta biyu tun azu da marece da ta farka Angel tayi mata bayanin komai dangane da gano ofa da kuma shirin su na guduwa, abunda yasa tayi mata bayani don kada ta basu matsala, da ya ke yarinyar tana da wayau ta fahimce ta sosai, yanzu haka suna kwance saman gadon Angel ita da azeeza sun rungume juna sunata sa a wasi ar jaki game da rayuwar da za su yi agidan daddyn Genie inta. Sauran an uwan nasu duk suna a zaune gefen gadajen su, duk wani motsin su Angel akan kunnuwansu. "Bamu san Girman ofar ba Angel Kada mu gaza wuce wa da akwatin kayan mu" Gabriel ne yai maganar, Cikin duhu suke magana, zurfin tunani ta yi acikin kwakwalwarta, A Labarin da Salsabeel ya bata Na mahaifin shi habibullah ya tabbatar mata da cewa ofar sai da rarrafe mutun zai Iya giftawa ta cikinta, mutun zai Iya rarrafawa ko ya zauna, Amma babu zancen mi ewa tsaye, abun zai zo masu da sau i tun da basu da girman jiki, yawancinsu dogaye ne amma babu iba, haris in ma da ke da jiki yanzu ya zabge ya koma kamar su Javed. "Ae akwatin zamu Iya kwantar dashi mu dinga tura shi ta cikin hanyar, Ni abunda nake Jiye mana kada mu kwasa mu tafi zai Iya kasancewa urmin daji ne bamusan ya weather in shi zai kasance ba, Zafi ko Sanyi, Zamu sha wahala akwai sanyin da ma zai Iya kisa Haka zafi ma, Ni nafi so mu tafi da bargunan mu saboda tsaro, shiyasa nake so mu auki akwati aya sai Backpack in Unaiza dole mu tafi da ita saboda gadon mu ce. Duk maganganun da suke tattaunawa cikin duhu akan kunnan an uwansu da ke zaune gefen gado Sun natsu suna sauraron su. "Mu fara aukar uniform in mu jera su ciki, " batul ce tai maganar, Angel tace"Ki je toilet ki auko mana fitila aya amma ki fara kashe ta tun acan dan kada su gan mu, a akin tsohuwa tamira zamu aiwatar da komai" ta amsa mata da toh, kafin ta nufi hanyar sashen toilet insu cikin duhu har ta samu ta cimma ofar makewayin nasu, da hannu ta tura ofar ta kutsa kai ciki ta shiga ta auko fitilar tare da kashe ta, Kafin ta dawo akin tunkan ta araso tace dasu gata nan tafe, Ru o hannunta Angel tayi acikin nata ta kuma ru o hannun Gabriel da ayan hannun atare suka shige akin tsohuwa tamira, "Ki kunna fitilar yanzu, Ni kuma zan shiga aki In auko Akwatin kayan mu da backpack in" ta amsa da toh, Batul na kunna fitilar Haske Ya gauraye ko'ina na akin tsohuwa Tamira, Zazzaro ido su ka yi ita da Gabriel da mamaki akan fuskokinsu suke bin Bedroom in da kallo, basu ta6a sanin haka ya ke ba, Yau ne rana ta farko da batul ta fara shigowa akin tsohuwa tamira. Kallon Juna su ka yi ita da Gabriel Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu ba tare da sun yiwa juna magana