← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 106

Sashe 69

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuskura ki bari in sake nanata maki! Nace ki gaishe da ita tunkafin na 6ata maki rai" sanin halinshi yasa ta wurga ma turai harara kafin tace"Ina wuni matar yaya" Cikin sanyin murya ta amsa mata Lafiyalou. Fitowa Dattijon arzi i yai daga toilet, jikinsa sanye da jallabiya, dogon gemunsa kamar ana ara mashi tsawo fari fat, fuskarshi auke da murmushi yake binsu da kallo "Gayu mutanan Allah, wa nake gani kamar turai? Rufe fuska turai tayi da mayafin jikinta, Sir mubarak na murmushi yace"yau surukar taka tazo gaidaka, tun azu da safe tasa naci akan saita shigo, nace tabari mu zo atare" "Amma nayi farin ciki, ni nasan iyata tana son zuwa duba babanta, kaine dai ka hanata zuwa mubarak, Allah ya kamaka, dama Ana kawo min tseguminka, akan untata mata da ka ke yi kana yi mata kulle agida" ar dariya Sir mubarak yai yana fa in"gaskiya kowaye ya fa a maka haka baba to ka bincike shi, Ni nasan ma baya wuce Jazz ne, Aiko inda shine yau a headquater zai kwana" Dariya suka sanya banda hajiya saratu data aure fuska, muryarta a ula ta soma magana "Baba dama na shigo ne don in gaishe ka, inaso zan wuce" Ganin tana yun urin mi ewa sir mubarak yai saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Koma ki zauna sarkin fushi, indai saboda mune kike ta 6ata fuska yanzu zamu koma gidanmu," ya arasa maganar tare da kallon Baban nasu, hankalin shi na akan fuskar saratu "Zamu wuce baba" "Ban gaji da ganinku ba, ku zauna muyi fira mana" acewar Obinna "Auta Ya meeting in naku? Yamutsa fuska tayi"lafiyalou, ba in har sun tafi, shiyasa na dawo gida" "Masha Allah," ya ambaci hakan tare da shafa gemunshi "Ya shirye shiryen tarbar ba inmu na gida da zasu zo? Ko kun manta da shagalin da zamuyi ne"? Sai lokacin Saratu ta sassauta fushin fuskarta jin anzo inda tafi so"A'a baba taya zamu manta da rana mafi mahimmanci agaremu ranar da mahaifinmu abun al'faharinmu yazo duniya," Kalaman saratu sun faranta mashi ranshi. Sir mubarak yace"Ai nafi kowa zumu in ranar tazo baba, naso ace ni aka ba damar aukar awainiyar duk wani abu da za'ayi a ranar, sai dai kash Hateem yai min kutse, gaskiya ban ji da i ba, Haka last time Sharafuddeen ne ya auki nauyin gudanar da shagalin" Da murmushi akan fuskar obinna yace"ai ba wani abu, dakai da su din duk abu ayane awurina, ina matu ar alfahari da ku, kuma Inajin da in yadda kuke nuna mini auna" Ya are maganar tare da kallo Turai, da zolaya yace"Surukar wannan karon wani kalar wanka zaki auka"? Du ar da kai asa tayi fuskarta auke da murmushi. Hajiya saratu tace"anko ne zamu fidda ae, zanyi magana da zahra aya daga cikin matasan Yaran da suka yi mana decoration lokacin birthday din twins, ta ware wurin iya tsara anko in yaso ma sai su yi mana decoration Jinjina kai Obie yai'naji da in jin haka, nima na yaba da aikinsu, yarinyar da kike magana akanta ai na ganeta ar gidan an Iya ce, suna da mutunci mutanan kuma mahaifinta yana yi mana hidima sosai, Yakamata ayi masu magana da wuri, tun da mun shiga watan" "Insha Allah idan na koma aki zan Kira zahran awaya in sanar da ita, amma baba kowa da kowa zai hallara ko? Dan banason inga babu wani adanginmu" Sir mubarak yace"dolensu ma su zo ai, wan su da kwarkwatarsu, babu wanda zamu yi ma uziri acikinsu, da na gida nigeria da na asar wajen kowa zai zo, Inyaso mutun zai Iya komawa aranar da yazo don wlh bamu raga ma kowa, just rana aya kacal zamu taya mahaifinmu birthday, banga dalilin da zai hana mutun zuwa ba" a tsanake obinna ke kallonshi, yana matu ar jin da in girmama shi da su ke Yi. "Ku kwantar da hankalinku, in sha Allah kowan nan su zai zo, munyi waya da lateef da abdul razak duk sun tabbatarmin da zuwansu, dama ni banida matsala dasu, Mutun ukun nanne suka fi shiga busy, sharafuddeen da Hateem inayi masu uziri sosai saboda yanayin aikinsu, to su dinma dai Alhamdulillah sun tabbatarmin da zasu samu damar halatta, hada sauran jikokina owais dai ne bani da tabbacin zai zo ko kuwa, har yau dai bansamu wayarshi ba," muryarshi da rauni ya arasa maganar. ta6e la66a hajiya saratu ta yi aranta tace"sai kace wani an gwal duk yabi ya dami kanshi akan owais, kamar shi ka ai ne jikanshi" Muryar sir mubarak ce ta fargar da ita daga yin zancen zucin"indai owais ne yana sane da wannan ranar mai muhimmanci, duk mun busy din da zai shiga bazai manta da ranar nan ba, saboda aunar da yake yi maka, don haka ka kwantar da halinka baba, In sha Allah Jikanka zaizo. Nauyayyar ajiyar zuciya obinna ya sauke, zallar farin ciki ne kwance akan fuskarshi har ya osa ranar ta araso ko dan yaga Jikanshi daya da e yana mamarinsa. "Baba Ni zan wuce ciki" hajiya saratu ce tayi maganar a yayin da take mi ewa tsaye tana gyara mayafinta. "Har mun gama magana"? Ya jefa mata tambayar, murmushin ya e ta an saki"inaso ne in shiga ciki, namanta na sanya mai aiki ta kaimin abinci, idan naci na huta zan Kira zahran awaya duk yadda muka tattauna da ita zanzo na sanar maka" Gya a kai obie yai"nima nafi so ki huta autana, ki ci abinci ki oshi idan takama ki kwanta kiyi bacci" dariya ta dan saki tana kallon baban nasu, maganar shi ta tuna mata uruciyarta, shi dai burinshi saratu taci abinci ta kwanta ta huta idan ta dawo daga makaranta, bayason tana aikin wahala. "Nagode da kulawarka akaina baba, Allah yabar mana kai abun alfaharin mu" Amasa mata yai da amin, Juyawa tayi ta kalli Sir mubarak da turai "Ni zan wuce yayana, a huta lafiya" bata jira amsarsu ba, da sauri ta fuce daga akin. Bayan fitarta, tattaunawa suka cigaba da yi game da yadda za'a tsara komai na shagalin da za su yi. Tun da ta shigo akin, komai na ciki agyare ta same shi, Safa ta kawo mata lunch inta yana asaman table ta aura mata shi. Cire lapcoat din jikinta tayi a saman Hanger ta sagala ta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa, rigar shan iska, daga bisani ta koma gefen gadon ta, ta zauna domin cin abinci, farawa da bismilla ta kai hannu ta dam i ha an cup na cofee ta kur6e shi, bayan ta gama ta soma shan farfesun naman kaza da zafi zafinshi, cikin anin lokaci ta shanye shi ta kuma dam ar Chips ta cinye ta cakumi cheese burger ta tura abaki hankalinta kwance take cin abincinta. Ringing in wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye saman pillow. Ba ta yi niyar aga kiran ba, don ita a a'ida bata picking call idan tana cin abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra'ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen in iphone inta *Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumu i ta aga kiran cikin harshen turanci ta soma yi mata kirari "Uwargidan shugaban asar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Ha iyar Daular Larabawa! Sarauniya aya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ari mun kulle ofa" sautin ayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya kara e kunnuwan saratu, da alama taji da in yabon da saratu ke yi mata. bayan ta gama yi mata kirarin ta aura da cewa"Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem in baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke" (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba aramin mutun bane, babban gorone magogin arfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice inta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arzi i wa anda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata. "Ba abun da ki ke tunani bane anwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa" itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa. "Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka asarmu" fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana. "Naji da in kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, ha ika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ashin inuwa aya har Allah ya azurtamu da samun zuri'a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min auna sosai nima Ina sonku" Hajiya saratu baki ya i rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta arasa ha iye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya. "Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu anwata baki daina ciye ciye ba ko"? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata aga kiran nashi. *A GIDAN AN IYA* Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu
Chapter 69 · 0% Book details