← Book details Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 106

Sashe 91

Kurkukun Kaddar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_THE PRISONERS E23 *Daga al alamin Boss Bature* Confusion of the heart Sir mubarak ne zaune Cikin Motarshi, da su ka yi parking dinta a harabar ajiye motoci na asibitin Obinna,Tan ameman asibiti ne Ya ha u tamkar ba wurin Jinyar marasa lafiya ba, An zuba dukiya wurin gininsa, suna da wararrun ma'aikata na gida Nigeria dana asar waje. Su biyu ne acikin motar, Shi yana a back seat na motar Ya zauna a hakimce, A yayin da Driver-operator dake driving dinsa Yana zaune saman driver's seat kowan nan su na sanye ciki kakinsa na sojoji, sun yi shiru, Sanyin A.c din motar na ratsa fatar jikinsu, ga dukkan alamu wani muhimmin abu ne ya kawo su asibitin, akwai wanda suke Jira Ya araso, tsawon mintuna Biyar, wani kyakkyawan matashin likita Ya nufo motar da saurin shi kamar zai yi tuntu6e. A gaban motar su ya dakata da yin tafiyar, ya kai hannu yai knocking glass din motar, turo ofar da a kayi ne Yasa shi yin saurin gyara natsuwar shi, Sam hankalin shi ba a kwance ya ke ba, tun da sir mubarak ya kira shi awaya ya sanar da shi game da zuwan shi asibitin gaba aya ya rasa natsuwar shi, saboda sanin matsayin shi a asar. "Dr fawan, shigo ciki mana " muryar Sir mubarak ce ta fargar da shi, Jiki na rawa ya shiga motar, ya zauna yana faman zazzare idonshi yace"daddy, ina wuni Ya gida ya Iyali" sir mubarak yace"lafiya lou fawan, Ya aiki ya fama da marasa lafiya" tun da ya fara magana bai ago Ya daura idonshi akan fuskar fawan ba, Hankalin shi na akan Wayar hannun shi da yake daddanawa. Still muryarshi na rawa ya furta"Lafiya lou daddy, sai ga kiranka, Na anyi mamaki" sai da ya ambaci hakan sir mubarak Ya ago da ido ya kalli fuskar fawan, duk da sanyin A c na motar, abun mamaki zufa ce ke tsastsafo mashi, kallon tuhuma sir mubarak yake jefa mashi, saboda zufar daya gani a saman goshin shi. "Ya akai naga kana zubar da gumi? Ko baka da lafiya ne"? Yawu fawan Ya ha iya tare da cewa"babu komai, Lafiya ta alau" Ta6e baki Sir mubara k Yai"Okey, Inaso ka kaini gidan kajin da kuke kiwo kai da Jazz," da alamun ru u akan fuskar dr Fawan yace"Gidan kaji? Daddy ban fahimci abunda kake nufi ba, waye ya bu e gidan kaji" yanayin yadda ya furta maganar, babu alamun yasan da zancen. Fuskar sir mubarak a aure tamau yace"You know who I am. I don't need to explain this to you, Don haka kada ka 6oye min gaskiya, wani gidan kaji ne kuka bu e kai da jazz? Da kanshi ya fa a mini cewa kun zuba jari don kuyi kiwon kaji, kusan kullum ne saina kama shi yana yin waya akan gidan kiwon kajin ku" Hankalin dr fawan ba aramin tashi yai fa, Muyarshi na rawa ya furta"`wallahi thumma tallahi daddy bansan da zancen gidan kaji ba, sai dai ko arya dr jazz yayi maka, ka ji na rantse maka da Allah..." Lamarin ya aurewa Sir mubarak kai, Sojan dake zaune a driver seat Ya natsu Yana sauraron su, ta cikin ear-view mirror din motar Yake kallonsu. "Fawan, Ka fa amin gaskiya, ni nasan Jazz ba zai ta6a yi mini arya ba, na lura gaba aya baka acikin hayyacin ka, idan ma saboda ni ne to ka kwantar da hankalin ka, babu abun da zan yi maka, ni dai buri na shine ka kai ni gidan Kajin ku, inaso in gansu, nayi maka al awarin idan ka rakani na gansu zan ara maku jari" cikin ru u dr fawan ya girgiza kai yana fadin"bazan yi maka arya ba daddy, ina ganin ka tamkar uba agareni saboda aunar dake a tsakanina da Jazz, wlh Daddy ni bamu ta6a yin maganar bu e gidan kaji da dr jazz ba" Da kakkausar murya Sojan dake a gaban motar yace"Sir, this boy isn't telling us the truth. Why don't we take him to the headquarter? Maybe if we do, he'll tell us the truth."(yalla6ai Yaron nan bazai fada mana gaskiya ba, Me zai hana Mu shiga dashi headquarter Wata' il idan mu ka je can Ya fa a mana gaskiya) Zaro ido waje dr fawan yai, jin ance za'aje dashi headquarter, sir mubarak yace"kada ka damu ai basai munje headquarter ba, akwai bindiga a uguna, "yai maganar tare da sanya hannu ya zaro bindigar Ya aurata saman laps dinshi, tsabar tashin hankali ne tsantsa akan fuskar fawan. Sir mubarak yace"idan na kashe ka na kashe banza, sai dai idan munje lahira ayi mana hisabi, don haka ka fa a min gasiya, idan ba haka ba zan tarwatsa kanka da bindigar hannuna" bawan Allah dr fawan duk sun tsoratar dashi da barazanar su, an hanjin cikin shi sun ka Hawaye tuni sun soma wanke fuskarshi, cikin sanyin murya yace"ko da zaka kashe ni daddy, bazan fasa fa a maka gaskiyata ba, wlh rantsuwar an musulmi bani da masaniya akan maganar gidan kaji, daddy banyi niyar fada maka ba, amma don in kare kaina zan sanar dakai wani abu da baka sani ba" Hankalinsu gaba aya yana akan fuskarshi. Numfasawa yayi kafin ya aura da cewa "Daddy, jazz baya zuwa aiki, yau kusan wata aya da sati, bansani ba ko kunsan da hakan, Ni kaina na damu da canzawarshi,". Zuciyar Sir mubarak a hautsine Ya furta"idan kuwa har hakane Dr fawan baka kyauta mini ba! Meyasa tuntuni baka kira awaya ka sanar dani cewa baya zuwa aiki ba? Kusan kullum sai na ganshi ya shirya zai je asibiti, hakan na nufin ba aiki yake zuwaba wani wurin daban ya ke tafiya? Ya jefa mashi tambayar yana mai jin aci acikin zuciyarshi. "Ka yi hakuri daddy, Bana son in shiga tsakaninka da shi, sannan ni bansan baku da masaniya akan hakan ba" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Sir mubarak ne ya furta hakan, zuciyarshi tayi matu ar karaya da jin cewa jazz baya zuwa aiki, Ya fara zargin shi akan arairakin da ya ke yi mashi, bai ta6a tunanin Jazz zai yi mashi haka ba, duk da irin aunar da yake nuna mashi. Idanuwan shi tuni sun ka a jawur, zuciyarshi ta motsa. "Bana so Jazz ya san cewa nazo asibitin nan! Ko nayi magana dakai! Kaja baki kayi shiru," dr fawan ya amsa mashi da toh daddy, in sha Allah bazan fa a mashi ba. "Ka share hawayen ka," da sauri dr fawan ya zaro hanky ya soma goge fuskarshi. "Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find out that he's doing something wrong, sai ya ani ku ar shi," rai a6ace ya furta maganar, ya ara da cewa "dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa bakin aikin ka" jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya. Shiru su ka yi babu wanda ya ara magana acikin motar, Lamarin ya aurewa Sir mubarak Kai, Mamakin shi aryar da jazz yai mashi na cewa Sun bu e gidan kaji, da kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk arya ne. Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin kwantar da murya yace"Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba da i mutumin daka yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai hana mu fidda rana aya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya shirya zai tafi aiki," Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon drivern yace "Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya" Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi, sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, aunar da ya ke yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko an shi da ya haifa bai jin su kamar yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan in amincewa da zargin yaron da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa. ANEELERH Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta aga hannu tayi addu'a ta shafa a fuska, kafin ta mi e da sauri ta nufi drawer ta auki wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arzi i ya bayyana akan screen din wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya. Bayan ta aga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar junaid ta katse mata hanzarin ta. "Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny," har sai da ta ji gabanta Ya an fa i, da mamaki tace"junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai itace ta baka wayar don ka yi mini magana" muryarshi da shagwa6a yace"mommy ai bata nan, suna a falo, Ni ka ai ne a akin..." tun kan ya arasa maganar tace"Junaid bana hana ka aukarwa mutane waya ba? Fa amin ya akai ka iya bu e mata waya"? "Mommy wasa nake maki, itane ta bani wayar, ta fita falo, ni ka ai ne a akin" A fa a ce tace" arya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka auka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai," ta yi maganar tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi,
Chapter 91 · 0% Book details