← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 134

Sashe 97

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karki damu da idon da zan kalli abokina da su ko ya mu'amalarmu zata kasance, kamin na fara zuwa gurinki sai da na sanar da Abiey, after mun fara shakuwa da juna na sanar masa kudina saboda bama boyewa juna sirri ni da shi, kuma ya nuna min ya jidadin haka, har ya fada min zai fi kowa farinciki idan Zahra ta yarda da aureka, ko ba komai kusancimu zai karu kuma na san zaka rika ta tsakani da Allah
ata kila ya fada maka haka ne, saboda yana kaunarka a matsayinsa na abokinka, baya son ya nuna maka damuwarsa ranka ya bace, amman na tabbatar Abiey yana so na, kuma dole zai ji kishi idan aka ce muna soyayya ma balle kuma ace na aure ka, ba zan iya haddasa masa bacikin ba, ba zan iya cin amanarsa ba
Na fada hawaye na rige rigen sauko min, lallai na yarda dan'adam butulu ne yanzu duk amincin dake tsakanin Abiey da Sauban ace Sauban zai iya tunkarata kai tsaye ya fada min cewar yana kaunata wane irin so ne wannan da zai saka ka manta aminci da abotar dake tsakaninka da amininka ka murje ido ka aure budurwarsa.
i tsaya ki yi tunani Zahra karki yanke hukunci cikin bacin rai, kuma ki duba halin da zan shiga idan kika amsa min da a'a
abu wani hali da zaka shiga domin babu komai a zuciyarka sai tsantsar budulci, karka sake ganinka a kusa da ni, kuma kar ka sake kiran wayata ko ka bi a gurin da na bi, idan ka sake min wata maganar sai na sami Abiey da kaina na sanar da shi abun da kake shiryawa
Na bude motar na fice a fusace, sai ya bude bangarensa ya fito.
amin ki sanar da ni abun da kika shirya zan riga ki sanar da Mr Bashir abun da kika shirya ke da matarsa, sannan na sanar da Mahaifan Deen abun da kika boye musu
Cak na tsaya gabana yayi dukan shida shida, na juyo a matukar firgice na kalleshi.
in siyar da
an cikinki saboda ki ceto rayuwar Deen, kin hada kai da matarsa da yayan matarsa kin mallaka masa
anki a matsayin nasa, ya kike tunanin zai ji idan ya gane gaskiyar dan da yake alfahari da tutiya ba nasa ba ne?

Wane irin hukunci kike tunanin zai yanke miki?

Idan ma ya kyale ki yan jaridu da Mahaifan Deen za su saka miki ido ne?

Kin ga daga lokacin kin bata sunanki da sunan danki kuma kin yankawa kanki tikitin zuwa gidan yari, wata kila ma zuciyar Mr Bashir ta buga ya mutu a daureki
Na tako na dawo a inda yake tsaye hawaye na sauko min kamar ba gobe.
ina ka ji wannan?
gurin wanda kuka nemi ta rufa muku asiri ta boye sirrin, wannan abun da kika aikata ya saka Abiey da Ammy da ita kanta Dr Zainab suna murna da yi ma Allah godiya da baki auri
ansu ba, idan kika san yadda Abiey ya tsane ki a yanzu saboda abun da kika aikata sai kin gode Allah da ya saka ba ku ganin juna a yanzu
a da son raina na aikata hakan ba, talauci ne ya saka ni haka
an jarida zaki yi ma wannan bayanin, rai ya fi rai ne da zaki da zaki siyar da ran da be miki komai ba, tun kamin ya zo duniya?

An fada miki talauci hauka ne?

Talauci ke saka rai fita daga jiki ne?

Ko kuma kina tunanin arziki zai hana mutuwa aiwatar da aikinta ne?

Da kika samu kudin kika biya ya tsaya ne?

Sai kika yi biyu babu da ace kin yi tawakkali ki bar wa Allah komai da yanzu ba ki shiga wannan halin ba
Ba ni da wata dabara sai ta kuka har numfashina yana kokarin fin karfina, cikin saldewar halshe na ce.
auban baka da wannan kusanci da zaka nemi wargaza rayuwata ko da Mr Bashir akan abun da be kamata ya shafe ka
a gaske?

Baki san ina da kusanci da mutanen gidan ba?

Ranar da na shiga cikin gidan na zauna a falo har na aika aka kiraki ba ki yi mamaki?

Jamila yaya ce a gurin matar da nake aure a yanzu, ko Matata kadai na sanarwa zata iya ruguza komai naki, saboda haka ina baki shawarar ki yi tunanin abun da zai zame miki mafita tun wuri wanda zai fitar da dake daga taskon dana sani, kwana biyu na baki ki yi shawara
a zan aikata abun da kake bukata ba, ba zan yarda na yi butulci ba
Na bashi amsa da kakkausar murya sannan na juya na nufi kofar gidan na shiga na bar shi a tsaye.

Ina shiga daki sai an samu yancin yin kuka yadda raina yake so, ina nadamar abun da na aikata, gashi sanadin haka na jefa mahaifiyata cikin tashin hankali ni ma kuma na jefa kaina, har ana min bazarana da shi, a cikin kalaman da ya fada min ba wanda ta fi daga min hankali da saka ni bakinciki kamar cewar da yayi Abiey ya tsane ni saboda abun da na aikata.

Na yi zaton Sauban zai sauya shawara ya kyale ni amman sakon karta kwana na gani ya shigo a wayata da sunansa.
i yi shawara da zuciyarki, karki yarda ko Mama ta san da wannan maganar, Wallahi Zahra kin ji na rantse miki da Allah ko?

Son da nake miki zai iya sakawa na aikata komai a yanzu, fiye da abun da Deen ya aikata ya shiga tsakaninku da Abiey, kuma ina mai kara tabbatar miki kwana biyu na baki karki yarda ki bijirewa umarnina, idan ba haka ba zaki jefa kanki a babbar matsala
Ban yi zaton wata matsalar zata bullon min a bayan wannan da nake ciki ba, da san abun da Sauban zai zo min da shi kenan da ban yarda na kira shi ba, kuma a lokacin da ya zo da ban yarda mun hadu ba.

Ko da Mama ta dawo ta tararda ni kwance galala na ci kuka har na gode Allah idanuwana sun yi sundun sundun, daman can bana dauka abu da wasa balle kuma wannan, yaushe Sauban ya lalace ya fara gurbata tunaninsa har zuciyarsa ta daya masa yayi min bazarana da wannan, da gaske zai aikata abun da yake da kudiri akai idan na ki amincewa ko kuma dai ya fada ne!

Na rasa amsar tambayar tunani da tashin hankali suka ki sakin kwakwalwata, duk juyin duniyar da Mama ta yi na fada mata dalilin kuka ban fada mata ba, a lokacin da na lura da ta damu sai na fake da cewar korar da Jamila ta yi mana ne ya saka ni kuka, Mama ta yi ta tausasar zuciyata sannan ta yi min albishir da cewar gobe zamu koma gidansu da zama wato family house dinsu da muka baro, kamin a samu gidan haya.

Ana gama sallah Magariba sai ga Dr Hamid ya shigo gidan, kamin ya shiga bangaren Hajiya Jamila ya kira ya sanar da ni yana waje kuma yana son na nema masa izini gurin Mama zai shigo yayi magana da ita.
Chapter 97 · 0% Book details