← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 134

Sashe 59

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban san lokacin da na yunkura daga inda nake zaune har tafin hannuna ya kai a fuskarshi ba.
llah ya waddaranka Abiey, ka zo da sunan gaisuwa kuma ka zauna a cikin gidanmu kana aibanta mijina...

Ji na yi an taba ni ina juyowa kanwarshi da suke uba daya Aisha ta dauke ni da mari.
azama dake har kin isa ki daga hannu ki mari Babban mutun kamar
an'uwana, kin san yadda yake fama saboda ke amman yau ki siffanta shi da wasu munanan kalmomi kuma ki daga hannu ki mare shi?

Waye ubanki duk garin nan?

Kiyayya ba hauka ba bace Zahra
an'uwana baya neman komai a gurinki ba ki da abun da zai saka ya yaudareki, macucin mijinki ne ya shirya komai ke kuma da yake wawuyace kin kasa fahimta, Anty tashi mu tafi
Ta mike tsaye ni kuma na bita da kallo baki sake hawaye na sauko min na zafin kalaman da ta jefeni da su.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un
Anty ta fada Mama kam zaunenta take tana kallon ikon Allah, kuma na san ba zata rasa dora min laifi ba wata kila shi ya saka bata ce komai ba.

Abiey ya mike tsaye idonsa har sun kada sun yi ja kamar ba na shi ba cikin wata irin muryar da ban taba sanin yana da ita ba ya fisgo Aisha ya dawo da ita baya.
uka ki bata hakuri Aisha
mman....

Kasa karasawa ta yi sakamakon wani mugun kallo da ya watsa mata.

'm sorry
Ta furta.
neel down
Ya fada tsabar bacin rai jikinsa har rawa yake, sai da ta aje numfashi da karfi sannan ta durkusa kasa guiyoyinta tana watsa min harara ta ce
orry
Tsakamin mikewarta tsaye da wanke mata fuska da yayi da mari biyu ma su kyau ban san wanda ya riga wani ba.
ow dare you raise your hand on her face?

How dare you Aisha...

D muryar dake nuna tsananin bacin ransa ya furta hakan yana kallon Aisha dake dafe da gefen fuskarta tana kuka domin a gefe daya ya sauke mata marin har biyu.

Sannan ya kalli ya Mama ya ce
ama ayi hakuri dan Allah
Ya juya ya fice Aisha ta bi bayansa tana kuka.
n yi na farko an yi na karshe Zahra da yardar Allah indai akan Abiey ne
Shi ne abun da Anty ta fada min sannan ta mike tsaye ta fice daga gidan Narjis na take mata baya, ni kuma kalli Mama ina kuka.
gaishe ki dai Juliet, matar Deen ma'asumin da ba shi laifi, ke ke ke Zahra ba wata ba sai Ciwon son Deen ya kashe ki, mahaukaciyar banza marar tunani ai ni Wallahi wannan bata burge ni da bata miki mugun duka na fitar hankali ba
Runtse ido na yi jin kalaman dake fita daga bakin Mama, sai kuka yace min ta
ho mu hade, tashi na yi da sauri na shige daki na kwanta saman katifa rike da hannun da na mari Abiey, marinsa da na yi a yau ya fi komai yi min zafi har ga Allah ban jidadin aikata abun da ban taba zaton ko a mafarki zan aikatawa Abiey shi ba, duk kuwa na san da cewa ya cancanci haka.
*Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*
10/20/22, 08:02 - Buhainat: *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*
Sauban dake driver side ya bude motar ya fito hango Aisha da yayi ta fito tana kuka kamar karamar yarinya, kamin ya kalli Abiey dake gabanta fuskarsa babu annuri.
iya faru?

Abiey ya jingina da motar yana sauke ajiyar zuciya ba tare da ya amsa masa ba, cikin kuka Aisha ta ce
arina yayi
Sauban ya kalli Abiey da sauri.
arinta ka yi?

Abiey be ce komai ba ya zagaya dayan side din ya shigo, Aisha ta bude back seat ta shiga Sauban na kokarin komawa cikin motar ya zauna sai ga Anty ta fito tare da Narjis, wannan karon be ce uffan ba har sai da suka shiga motar shi kuma ya fara driving.
biey indai na isa da kai...

In dai zan fada maka magana ka ji to daga yau kar na sake jin sunan yarinyar a bakinka, kuma karka sake takurawa kanka da tunaninta
Abiey ya juyo ya kalli Anty dake maganar.
mman Anty ba zaki ga laifin Aisha ba?

Ita ta fara marinta fa?

Akan me zata daga hannu ta mari Zahra tsakani fa da Allah
allai so hana ganin laifi, yanzu duk darajarka da kimarka da yarinyar ta keta ta daga hannu a gaban kanenka kuma a gabana ta mareka baka ga laifinta ba?

Abiey ka girmi yarinyar a shekaru a matsayin ba dan kaddara ta so ba da babu abun da zai saka ka kalleta ma, amman a haka ta daga hannu ta mareka, ta kiraka da kalmomi marar dadi a gaban idona agaban kanenaka saboda abun da bata san gaskiyarsa ba?

Ai ko karya kake yi ba zaka zauna a gaban mahaifiyarta ka zagi Deen ba
nty dan Allah maganar nan zata iya tsayawa a tsakaminmu?
a zata tsaya ba
nty kin fi kowa sanin Ammy bata da hakuri
ole sai ta ji abun da ya faru, kuma ni da ace zaka ji magana ta Wallahi da ka yafe yarinyar domin ta fice min a rai, kuma baikonka da Yasmin ba za a fasa ba
Uffan Abiey be sake cewa ba, balle kuma Sauban da tun da aka fara maganar ba saka bakinsa ba, Anty kuma bata fasa fada ba tana ta munana masa Zahra, har suka isa masarautar Sauban ya faka daidai entrance din shiga part din Anty, Narjis ta bude ta fita tare da Aisha da fuskarta ta kumbura saboda marin da Abiey yayi mata da kuma kukan da ta sha.

Sai da suka shige ciki sannan Abiey ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ta runtse ido, Sauban na ganin haka yayi reverse ya bar gidan yana tukin a hankali.
biey I'm your friend, dole ne na fada maka gaskiya ko da zata maka daci
Abiey yayi saurin bude idonsa ya kalli Sauban.
arka fadi wata magana da zata bata min rai a kan Zahra, ina son yarinyar Sauban ko da zata saka wuka ta yanyanka ni, ina sonta kuma ina son na tabbatar mata da haka
mman ka daina zuwa da yan'uwanka a gurinta
an kiyaye, sauke ni gurin Ammy
Sauban ya kalleshi cike da tausayi sannan ya sauke ajiyar zuciya.

Babu wanda ya sake magana a cikinsu har aka suka isa gidan Ammy, Abiey ya bude motar ya fita, a hankali yake takawa har ya isa bakin kofar falon hannunsa ya kai ya tura kofar ya shiga.

At first yayi tunanin zai same ta a falo, domin tana jiransa a duk lokacin zata yi masa fada ko kuma wata magana.

Sai dai be samu kowa a falon ba cikin har da Jummai mai aikin Ammy, kai tsaye ya nufi upstairs yayi knocking kofar
akin sannan ya tura ya shiga, Ammy da plate din zogale ki kan cinyarta ta dago ta kalleshi, sai ya tsaya jikin kofar kamar mai jin tsoron karasowa.
nty ta kira ki?

Ta tambaya yana ala ala tace masa aa sai ya fara tarar abun tun kamin Anty ta shimfida mata komai.
h yanzu muka gama waya, kuma ta fada duk abun da Zahra ta yi daman
an talaka be iya samun guri ba, saboda ka kai kanka ka nuna kana son ta shi zai saka ta daga hannu ta mareka?

Waye ubanta duk garin nan....

Da fari cikin lalama Ammy ta fara maganar kamar abun arziki sai kuma ta karasa a tsawace alamar ta fusata sosai.

Abiey yayi saurin sakin kofar ya karaso kusa da ita ya zauna.
mmy karki zafafafa please
ar na zafafa?

Wata banza yar banza da bata wuce auren direban gidana ba ta daga hannu ta mareka?

Saboda ta samu dama ka furta kana sonta?
mmy tana cikin bacin rai ne bata gama fahimta ba
ata gama fahimta ba?

Mi zata fahimta?

Kana sonta?

Idan baka somta zaka koma gurinta ne?

Ka kwana ka tashi da son yarinyar nan kamar ibada yanzu kana zuwa yi mata gaisuwa ta mare ka kuma ta kira da azzalumi macuci ai ko dan sanin Zuwaira matar Mai Martaba ce ya kamata ta daga maka kafa ta ji kunyar wulakanta ka, balle kuma har ta san da cewa kai ma
an Sarkin ne, ta manta yadda take zuwa ta hau saman gadona ta kwanta?

Yau zata daga hannu ta mari
ana?

Alhamdulillah da baka aureta ba, kuma ko ita kadai ta rage ya mace ka hakura da ita kenan
A razane ya mike tsaye.
mmy?

No no no no no no!

No please na san ranki daman zai bace amman bana son ki sake cewa komai zamu yi magana daga baya
Be jira abun da zata fada ba ya fice daga dakin da saurinsa, jikinaa har rawa yake numfashinsa na fita da karfi tsabar tashin hankali kansa har tsarawa yake.

ZAHRA POV.

Hannuna na dora akan filo ina da rutsar kuka, ina jin kamar wani ya zo ya bani hakuri ya fada min cewar abun da na yi daidai ne.

Amman ko Mama da muke gida daya bata shigo dakin ba ta kyale na ci kuka har na kusa cinye kaina ina ta jin kamar na yanke hannun nawa da na mari Abiey da shi na jefar.
Chapter 59 · 0% Book details