← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 134

Sashe 28

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kazan wahala da zafin da mace take ji idan ta haihu
anta be zo da rai ba balle kuma ace ta siyar da shi?

Jahilcina da talaucina be kai can ba
Ya mike tsaye shi ma yana kallona irin kallonta na babu wasa a maganarsa ko fuskarsa.
annan maganar tsakanin ni da ke, domin Wallahi bayan ke da na fada miki maganar nan a yanzu da ita Jamila babu wanda ya san da ita, ciki kuwa har da matata, saboda ki iya bakinki idan ba haka ba rayuwarki zata shiga tsari, mafita nake nema miki shiyasa na fada miki idan ba zaki iya ba ba zai kowa ya sani ba
mman dai baka da imani
a bani da imani da ban zauna na fada miki haka ba, domin ba cilasta miki na yi ba, mafita kike nema kuma na fada miki
Na girgiza kai ina mamakin yadda zuciyar mutane ta lalace suke son cutar da mutane a take, domin wannan cutarwa ce.
a zan yi ba
oh ko ki iya bakinki
Ya sake gargadina, ban saurareshi ba na juya na fice rai na bace, a yanzu na tabbatar neman taimako yana saka mutane fadawa hali kala kala, tun da gashi har ya samu damar da zai zaunar da ni ya fada min wannan maganar.
10/1/22, 22:03 - Buhainat: *
CIWON - SO
By Khadeeja Candy
Jikin sanyi jiki na shigo dakin na sai na samu Deen a kwance idonsa a bude alamar be dade da farkawa ba kenan.

Da sauri na karasa kusa da shi ina kiran sunansa.
een...

Sai ya kalli detection dina da idonsa kamar baya gani da kyau, na mika hannu na kama hannunsa ina masa murmushin karfin hali da kuma hawaye a lokaci, sai dai na lura kamar kallona kawai yake ba dan ya fahimci ni dince ba, wata kila ba baya ganin komai.

Na saki hannunsa na fita da sauri na zuwa kiran nurse domin bana jin zan iya komawa dakin likita ma, nurse din ta shigo da saurinta dayar kuma ta tafi kiran likita, na tsaya daga gurin kafafuwansa ita kuma tana gurin fuskarsa tana dubawa sai kuma ta karasa gurin da file dinsa yake ta dauka ta bude ta duba sannan ta matso kusa da shi.
aharadeen
Ta kira be amsa mata ba, kuma be yi wata alama dake nuna yana cikin hayyacinsa ba, ta taba hannunsa ta koma gurin idonsa kamin ni da ita mu juya muna kallon likita daya shigo, kallona yayi sannan ya dauke kai ya karasa kusa da Deen ya shiga duba shi, sai ya juyo ya kalleni.
na maganin da na ce a siyo masa?
owa be zo ba, shiyasa ban samu fita ma siyo ba, kuma ban ma san inda ake siyarwa ba ina jiran Baba ya zo ne sai a bashi saboda shi yake siyowa
Ya girgiza kai yana wani guntun murmushi.
alama kina wasa da rayuwar mijinki Wallahi, kika yi wasa kadan zaki rasa shi
i ba kai ne Allah ba, ba kai ke da rayuwarsa ba, na kai ka hallicce shi ba, balle kasan lokacin mutuwarsa, idan Allah yace zai tashi zai tashi Wallahi baka isa ka kashe shi ba
Tun da na fara ban tsaya ba, hawayen dake sauko min kuma ba su tsaya ba, Nurse sai kallona suke domin sun lura kamar fada nake da likitan, be ce min komai ba yayi masa abun da zai masa ya fice.

Sai na durkushe a gurin na fashe da kuka, taya wani zai fada min cewar zan rasa Deen mutumen da yayi min fuka fuka a lokacin da nake tsananin bukatarsu?

Na kai hannu na shafa cikina.
un kwallafa rai da buri da yawa akan cikin nan, taya wani zai zo ya nemi abun da ba zan iya ba
anzu kenan da aka fada miki cewar zaki rasa shi ina ga kin rasa shi? kina son rayuwar mijinki, idan shi ne zai iya bada komai saboda ki rayu cikin kuwa har da danku ko yarku
Wani bangare na zuciyata ya soma karantomin abun da ban yi zaton zai zo min ba.

Na mike tsaye na karasa kusa da Deen hawaye na ta aikinsu a fuskata ina kallonsa har lokacin oxygen na fuskarsa idonsa kuma a bude sai dai ba kallo yake irin an masu gani ba, kuma irin wadanda suke cikin hayyacinsu.
een zai yi komai dan na rayu, Wallahi ba tabbatar ko rai zai iya kashewa saboda na rayu, da shi ba zai jure ganina a cikin wannan halin ba
Na sake kai hannuna ina taba cikin nawa.
mman zai jidadi idan na yi haka?

Na durkusa kasa na kama hannunsa ina tabawa.
dan ka rayu zamu iya samun wasu yayan, amman kai idan na rasa ka na rasa ka har a bada, Hajiya ma ta rasa da har abada, Bahijja ta rasa yaya, yar da za haifa ta rasa uba, kuma na rasa farinciki kenan
Na lumshe ido ina jin wani irin rauni na rashin makama abun da zan yi.
dan kuma ka rayu na rasa
an na ce maka me?
_Zamu baki matacce wanda zaki shaidawa duniya da yan'uwanki cewar abun da kika haifa be zo da rai ba_
Maganar da likitan yayi ta dawo min a rai.
a kamata dai na yi shawara
Na fada ina mikewa tsaye, sai kuma na tambayi kaina.
oh da wa zan yi?

Duk wanda zan yi shawara da shi zai iya fallasa wannan sirrin ko kuma ya hana ni, idan ba wannan ba ina da wata mafitar ne?

Babu wanda yayi min taimakon da zai ceto rayuwar mijina, wannan ce kadai damata
Sai kuma na girgiza kai.
a zan iya ba, ba zan iya ba be kamata na yi ba
Ina cikin magana da kai Bahijja ta turo kofar dakin ta shigo tare da kawarta, na yi saurin boye fuskata ina share hawayena.
aman Hajiya tace kila kina can kina aikin kuka, shiyasa ta ce na zo na zauna ke ki tafi gida ki huta
na ita Hajiya?
anta yana dan ciwo tace zata dan kwanta
kay Lafiya Kalau
Na karasa ina amsa gaisuwar da kawar Bahijja take min.
na ta jiran Baba ya zo likita yace a siyo magani, gashi ba ni da waya balle na kira na fada masa
ari na kira shi da wayar Basira
oh.

Na kalli Deen sannan na dauki jakata domin ina bukatar hutu da natsuwa a yanzu.
mman kin ci abinci?

Na daga mata kai kawai.

Sai na ji tace
aa kin ga Ya ya bude ido
Na juyo ina kallonta, sai murna take tana kiran sunansa da fatar ya amsa mata.
a Deen Ya Ya ya ya.....

A take yanayin fuskarta ya canja, sai ta dago ta kalleni.
e amsa ba
a zai amsa ba
mman idonsa a bude suke
aka yake tun dazu
o ya mutu ne?

Mun shiga uku, daman ni da Hajiya mun yi mafarkin Ya ya tafi ya bar mu Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, talauci be yi ba, saboda rashin kudi zamu rasa dan'uwana
Ta fashe da kuka sai kawarta ta karasa da sauri tana duba shi.
u kira likita mana ya duba
Sai hawaye ya sake taruwa a idona, na tausayin kaina da kuma Bahijja.
ikitan ya zo ya duba shi, dole sai an hada kudin gaba daya
llah ka yi mana mafita alfarmar Annabinka Allah
min, ki kira Baba ya zo ya siyo maganin
Tayi saurin karbar wayar kawarta, ni kuma na juya na fice ba tare da na sake cewa komai ba, sai da na yi nisa da ward din sannan sai kuma naji kamar ba zan iya fita daga asibitin gaba daya ba, idan ma na fita ina zanje?

Gidan Yaya Maryam ko gurin Mama ko kuma gurin Hajiya?

Ko gidana da nake ganinsa kamar kango a yanzu saboda babu Deen a ciki.

Wasu kujerun da aka jera daga waje gurin karbar kati na nufa sai na zauna a dayan kujerar na jingina ina ta kallon sama, kamin na koma kallon mutanen dake kai da kawo a gurin, tunani ma har na rasa wane zan yi wane zan bari, kama wance kamo wacan, kwance can kulla wacan haka dai har bachin da yafi kama da na wahala yayi gaba da ni.

Babu komai a cikin mafarkina sai Deen saboda bachi ya dauke ni da tunaninsa a raina, kadan daga rayuwar da muka yi ta zo min kamin wata sabuwar rayuwar da ba mu taba yi ba ta biyo baya, a wani katon gidan sama muke rayuwa a dubiyar mafarki, yana ta kuka ni kuma ina dariya sai yayi baya baya yana miko min hannu sai ni ma na mika masa sai dai kamin na kama hannun nasa sai ya fada a kasa cikin wani abu mai kama da giragira kuma kamar hayaki, na leka gurin da saurin sai na gane gidan saman irin wannan ne da bashi da stairs balle na taka na sauka, har kuma lokacin dariya nake sosai na dukushe a gurin ina leken gurin da Deen ya fada kamar ni ma zan fada din, jin na yi an taba kafada ta bayana, sai na juyo da sauri ina kallon wanda ya dafa ni, sai dai kamin na ga fuskarsa wani ya miko min hannu alamar na kama hannunsa na mike tsaye, shi ma ban ga fuskarsa sai na ji an mikar da ni tsaye an share min hawayena an rumgume ni, a take dariyar tawa ta koma hawaye.
e Malama tashi Malama...

Firgigit na farka daga mafarkin ina kallon matar dake rike da danta tana tayar da ni daga bachin da be dade da daukata ba, abun da ban sani ba hawayen da nake a mafarki ashe sun fito a idona da gaske.
uka kike yi da dariya kina bachi
Na yi saurin taba fuska sai kuwa na yi arba da hawayena, saurin sharewa na yi na mike tsaye ina mata godiya, na fara tafiya ina ta tunanin manufar mafarki, a iya sanina mafarkin kana dariya a cikin mafarki to zaka yi kuka a zahiri ne, idan kuma ka yi mafarki kana hawaye a mafarki zaka yi farinciki ne a zahiri kamar yadda masana suke fada, to amman fadawar da Deen yayi daga gidan saman zuwa kasa fa?

Me hakan ke nufi?
utuwa?
Chapter 28 · 0% Book details