Sashe 132
Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da zamu kwanta na yi waya da Mama sai take fada min cewar Mr Bashir yana shirye shirye komawa Abuja da zama, sam ban jidadin hakan ba duk kuwa da kasancewar ban isa na hana hakan ba, sai dai na jidadin fada ma Mama da yayi a inda zai zauna a Abuja, koda be fada ba ma na san ba zai zamu rasa sani ba domin ba boyayen mutum ba ne.
Ina son na tambayi labarin Dr Hamid amman ba dama domin Abiey ya canja min line kuma duk abubuwan nan da suka faru Dr Hamid be kira ni balle ya same ni mu yi magana, haka ma ban sake jin duriyar Jamila ba, ban san a inda take zaune a yanzu ba balle na kuma Dr Hamid, ko a ina yake yanzu a wane hali yake, ko ya samu labarin abun da ya faru Allah masani.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Hausawa suka ce an baro kyau tun ranar wanka.
Domin wadansu hotunan auren Abiey da Yasmin da kuma shagulgulan da aka yi na tabbatar sun wuce ni, irin wucewar da ban iya na dawo da baya ba balle amaimaita min irinsu.
Har aka yi shagulgulan bikin aka gama hankalin mijina yana kaina, nawa kuma yana gurin zaman da zai yi da Yasmin, a dare da aka kawo ta a matsayin abokiyar zamana kamar yadda Ammy take ta nanata min cewar kar na dauke ta a matsayin kishiya, na kasa rike kaina duk wanda zai kalleni ya san bana farinciki da auren, musamman ma mijina da ya kasance a tare da ni kamar ba shi ne angon ba.
Duk wani abu da Abiey zai yi ya kwantar min da hankali yayi, ba ni da tabbacin zai iya adalci a tsaninmu har sai zamantakewarmu ta yi nisa, amman a ina ganin ido da nake masa a yanzu da kuma kyakkyawan zaton da zuciyata take masa ina ganin kamar ba zai iya cin amanata ba.
Sai da aka fara kawo ta a gidana ta gaishe ni Ammy ta yi mana nasiha sannan aka fita da amarya zuwa gidan angonta, kaina na a kasa har sai da Ammy ta fita sannan na dago na dawo dakina sai na fadi kwance akan gado na fashe da irin kuka na bakinciki da damuwa marar misaltuwa, a ranar na ji kamar zuciyata zata fashe, duk irin soyayyar da nake yi ma Abiey sai ya rika ba ni haushi, wata zuciyar na raya min akan me zai hada soyayyata da ta wata, ban zauna da kishiya a gidan Deen ba, saboda haka ban zan zafin kishi da mace take ji ba, sai a yanzu da na hadu da ita a gidan mutumen da a fi kauna fiye da komai a rayuwata.
Kuka sosai nake tun ina yin na hankali har ya fara fita ina ihu kamar zan tashi gida, a lokacin da mijina ya shigo ya same ni a wannan halin sai hankalinsa ya tashi, cikin damuwa ya rumgume ni, yana ta rarrashina da kalamai masu dadi, da kara tabbatar da kaunar da yake min.
Har kusan goma na dare ina tare da mijina har sai da Sauban ya shigo ya fara fada a falon sannan Abiey ya sake ni ya fita bayan ya aje min kayan ciye ciye.
Wallahi hauka ce kawai ban yi a daren ba domin na shiga damuwa da bakinciki marar misaltuwa, da zarar na motsa zuciyata ta raya min cewar Mijina yana tare da wata a yanzu sai na ji babu natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, daker na ga safiya, ina sallah asuba zazzabi ya rufe ni, kanwarsa Aisha yar wajen Anty Amarya da ta kwana a gidan ce ta kira shi a waya ta sanar masa, sai gashi ya isa tun kan duhun asuba ya gama wayewa.
Ina kwance ya yaye mayafin da na rufe da shi ya dago ni ya rumgume yana tambayar jikin nawa, kamin ya saka hannayensa yana buda idona.
a ki yi bachi ba
Ban isa na ce na yi bachin ba, domin idanuwana da suka kumbura saboda kukan da na sha ya nuna haka.
ikinki da zafi sosai, tashi na dauko miki tufafi ki saka mu je asibiti
a su fito ba yanzu
kay then bari na kai ki gurin Dr Zainab ta duba min ke
Ya sumbanci ni cike da kulawa, yadda ya fada haka muka yi, shi ya dauko min tufafi ya taimaka min na saka sannan muka fito ya saka ni a mota ya dauki hanyar gidansu yar'uwarsa.
Kusan mu muka tashe su daga bachi ta taba jikin nawa ta rubuta masa maganin da zai siyo min sannan ta shirya mana abun karyawa, ba dan na so ba na ci kadan sannan na sha maganin na kwanta.
Ko da na farka Abiey ba shi a gidan, sai wayata ya kira yayi min ya jiki bayan na gama karanta sakonsa.
Sai da azahar ya dawo a gidan muka wuni a nan har dare a lokacin da yace zai dauke ni ya maida ni gida sai Labari ya canja domin bana bukatar zama a gidan a yanzu kasancewar ba shi a ciki.
A dole ya hakura ya bar na kwana a gidan bayan Dr ta cilasta masa yin haka saboda tsoron kar na je can zazzabin ya sake dawowa.
Ba laifi na samu bachi a nan domin mun dade muna hira da Dr ta rage min kewar mijina har sai da na fara jin bachi sannan na shiga daki na kwanta, the following day na koma gidan Ammy da zama bayan Dr ta fada mata abun da yake faruwa, sai dai zama a gidan Ammy sai ya fi min bakinciki fiye da zama a gidana domin sauran bakin da suka rage na biki da ba su tafi ba idan Abiey ya shigo sukan tsokane shi su ce masa ango hakan kuma yana min zafi sai nake ganin kamar da gayya suke min.
Duk yadda Abiey ya zo na koma na cigaba da zama a gidan Ammy bata yarje masa ba, nima kuma hakan yayi min dadi domin bayan tafiyar bakin sai ya rage daga ni sai Ammy sai mai aikinta Jummai ne a gidan, idan zata yi girki ta kan kira ni na taya tana nuna min wasu abubuwan, tana fada min abubuwan da Abiey yake so da wandanda baya so, da kuma kalar abincin da mijina ya fi so, a dan zaman da na yi a gidan na kara karantar halin Ammy mace ce mai matukar saukin kai da kuma son zaman lafiya, domin a duk hirar da zamu yi zata ba ni labarin irin zaman lafiyar da suka yi da mahaifiyar Yasmin ne, da kuma yadda zan kwantar da hankalina kuma na nuna wa mijina yadda zai kwatanta adalci ko da ya kasa yin haka.
A cikin abubuwan da Ammy take yawan nanata min akwai koyon girki da kuma rage yawan kukan da nake da duk wani abu da zai daga hankalin mijina, ta fada min da iya girki ta kara kwance Mai Martaba a lokacin da ta zauna a gidansa, hak
an ya saka na darsa a zuciyata cewar ni ma zan koya ko da na kara samun damar murza kambuna na cikakkiyar mace, sannan ta fada min na rike kamshi daya, wanda zai rika tunawa mijina da ni a duk inda zai ji mai irin kamshi, har ya zamana ba shi dadin kamshi wani turaren mata sai nawa.
Sai da Abiey ya cika sati daya cir a gidan Amaryarsa Yasmin sannan Ammy ta maida ni gidana, a ranar na zage damtse na gyara ko'ina na cikin gidana da kaina na cika ko'ina da kamshi na canja wasu abubuwan.
Abiey na shigowa na danne duk wani zafin kishi da nake ji na rumgume shi ina masa maraba da zuwa, a falo muka fara shiriricewa sannan muka shiga daki, taya shi cire tufafin jikinsa, daga sunan raka shi bandaki sai ya janye ni muka yi wanka a tare, a can ma sai da muka shiririce sannan muka fito, shiga na yi mai kyau irin ta alfamar shi ma ya saka shadda sannan muka fito makalle da hannun juna, tsaye na yi har sai da ya bude min mota na shiga sannan ya zagaya ya shiga muka dauki hanyar gidan Amaryarsa, kamin mu isa ya bi ta shopping da ni na zaba mata turaruka masu kamshi da kyau sannan muka isa gidan.
Na yi mamakin yadda ta tarbe ni a nan na lura ta fini wayo da kuma wayewa domin har ga Allah ni ba zan iya hadeye kishina na sakar mata fuska da jiki kamar yadda ta yi min ba.
Amman sai gata tana jana da hira har da su dauko waya ta dauke mu hoto da Abiey sannan ta yi mana ni da ita daga karshe kuma ta dauke mu a tare gaba daya, da gangan na rike hannun Abiey na shiga dakunanta ina dubawa ita ma dai an narka mata dukiya, ko da yake ba abun mamaki ba ne domin yar manyan mutane ce ba kamar ni ba, hakan kuma be kara min komai ba sai kaunar Ammy wanda ta tsaya ta tsara min komai da na zo na tarar da shi a gidana.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: A falonta Abiey ya tambaye kwana nawa muke ganin zai yi mana a tsakaminmu, a karshe muka zabi kwana biyu biyu domin shi yafi dadi da kuma adalci, da zamu fito ta dauko wasu daga cikin kayanta na lefe ta yi min kyauta da su, Abiey ya rika min jakar muka shiga mota tana daga min hannu har muka fice.
Isowarmu gida da kamar minti talatin ta kira number ta tambaye ni ko mun iso lafiya, na yi mamakin a inda ta samu number wayata sai Abiey ya warware min ta hanyar fada min da yayi cewar ta karbi number tun a shekaranjiya, har yake nanata min wai ban fada miki Yasmim bata kishinki ba yarinyar tana da hankali ai, a nan na gane wayayyiyar yarinya ce Abiey ya auro kuma idan ban tashi tsaye ba zata iya kwance min mijina.
Daren mun kure junanmu da soyayyar da kuma kewar juna da muka yi na tsawon sati daya ba a tare.