← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 134

Sashe 101

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan na rufe kur'ane na daga hannayena na yi addu'a bayan na jadda salati ga Annabina.
a ruwan tea ki sha, na lura ba zaki iya cin wani abu mai nauyi ba yau
Na kalleta lallai uwa uwa ce ta fahimci ina cikin damuwa amman gudun takura min ya saka bata tambaye ni ba, daman ni kuma bana son sanar da ita ba.

Matsawa na yi kusa da ita na dora kaina a kan kafadarta.
ama na yi magana da Sauban, mun daidai ta kanmu ina son idan kin samu dama ki yi magana da su Baba sai na fada masa ya fadawa iyayensa
ahra kina ganin haka ya fi miki?
nshallah ina fatar haka, ke dai ki cigaba da yi min addu'a kawai
o Allah yasa alheri ya tabbatar da alherin
meen
Na amsa ina jin addu'ar da ta yi min kamar ta soka min mashi a kirji, domin hakan na kara tabbatar da cewar auren Sauban din zan yi.

Yanzu haka za sake rayuwa a gidan wani da yake da kusanci da Abiey, ni kuma na mutu da kaunarsa?

Na tambayi kaina tambayar da bata da amsa, wata kila kaddara ce a haka na rayu da ciwon so kuma na mutu da shi.

Yadda Sauban ya matsa a lamarin auren sai da abun ya ba ni tsoro, wani dama ya samu da yake iya ta controlling dina yadda yake so, ya fada min cewar zai zo ya tafi tare da ni ya gaishe da iyayena da yan'uwan da ya kamata su san juna da shi, a haka na amince masa domin bana da wani iko a yanzu, ina jin kaina kamar mai mutattaciyar zuciya da bata iya tabuka komai sai yadda aka juya ta, da toh kawai nake amsa duk wani abu da yake fada min ko kuma ya ba ni umarni, a ranar muka je na gaishe da mahaifiyarsa mace mai far'a da son mutane, yadda ta tarbe ni tana haba haba da ni sai na rantse da Allah ni ce da surukarta ta farko, kanwarsa kamar zata cinye ni dan murna, sai dai kowa ya kalli fuskata ya san bana farinciki da auren saboda na kasa sake jiki na kasa annashuwa murmushi ma da nake na dole ne, ashiri ta arziki suka min daga mahaifiyarsa har kanwarsa da sauran yan matan dake gidan, domin kyautar da suka min tafi karfin a kirata da goma ta arziki.

A bakin gate ya tsaya ya rika min ledodin muka shigo da su cikin gidan.

A bakin BQ muka tsaya sallama da shi sai na kasa daga ido na kalleshi domin a halin yanzu ina jin kamar ba ni da wani babban makiyi kamar Sauban idan akwai wanda na tsani gani ko jin sunansa ko mu'amala da shi to Sauban ne.
ahra ki sanar da iyayenki nan da kwana biyu zan turo nawa iyayen, kuma ina son kisan da cewar auren kawai za a daura tarewar kuma sai ranar da kika zaba, sannan bana bukatar komai daga gareki
Wani hawaye mai zafi ya sauko min, na kasa ce masa komai, cikin karfim hali na taka na karasa kofar dakin mu na shige na bar a gurin tsaye.

Kamar yadda Sauban ya bukata haka Mama ta sanar da yan'uwanta da yan'uwan Mahaifina, duk da abun da ya faru tsakaninta da Baba wato mahaifin Deen be hana ta sanar da shi ba, ba dan komai ba sai dan da ba shi hakkinsa a matsayinsa na abokin mahaifinmu kuma uban da ke aurar da mu a duk lokacin da za mu yi aure tun daga kan Yaya Maryam har zuwa kaina.

Babu irin fadan da Yaya Maryam bata yi min ba saboda na gabatar da Sauban a matsayin mijin da zan aura a gurin magabatana, ba dan be cancanci aurena ba sai dan tana ganin hakan da zamu aikata kamar zai taba Abiey, a tunaninta be kamata na aikata hakan ba saboda Abiey ya nuna min soyayya mai karfi, kuma be guje ni ba sai dan shiga tsakani da aka yi mana, sai dai na gagara fadawa kowa boyayyen sirrin da ya saka zan auri Sauban saboda ina gudun abun da fadin zai haifar, na yardar wani lokacin ba ni hikimar neman shawara idan zan yi abu saboda ina tsoron kar a ba ni shawarar da zata haifar min da matsala, wata kila kuma shawarar da na zabawa kaina ba zata wanke ni ba.

Daman kamin iyayen Sauban su tafi gurin nawa iyayen ya fada min cewar jumma'ar da zata zo ta jibi za'a daura auren tarewa kuma sai lokacin da na zaba, shi dai muradinsa a daura auren.

Ko ba a fada maka ba kasan auren yayi gaggawa ace an zo neman aurena a yau kuma ana bukatar daure auren a jibi idan da hali, sai dai ba kowa ya kula da haka ba ganin cewar bazawara ce ni a yanzu ba budurwa ba, musamman da ya fada musu cewar tare ba a yanzu za'ayi ba, sai da yayan mahaifina ya kira wayata ya tambaye ni sadakin da nake ganin ua kamata su yanka, sai na ce na bat masa wuka da nama a hannu su yi abun da ya kamata, sannan suka tambayi cewar ko mun amince a daura auren a jumna'ar nan mai zuwa ta jibi kamar yadda iyayen angon da kuma mijin suka bukata.

A daren ranar da aka yi tambayar auren, Mama ta tsare ni da tambaya domin ita ma kanta ta fara zargi kamar akwai cilastawa a amincewar da na yi saboda rashin sukunin da nake da yawan kuka musamnan ma cikin dare ga kuma daurin auren da Sauban ya bukata a kusa kusa, ban yarda na nuna mata fuska da zata fahimci akwai wani abu a kasa ba balle har ta cilastani fada mata.
aga baya na sake shawara, ina ganin a daga auren nan zuwa wani lokaci nan gaba, ko da wata daya ne
Na daga idanuwana da suka kara bayyana ramar da na yi na kalleta.
ama wata daya yayi nisa, sun ce basa bukatar komai daga gurinmu
o da basa bukatar komai, ai ya kamata ayi komai cikin natsuwa ba a gaggauce kamar haka ba, wasu da ya kamata su sani ba ba kowa ya sani ba
dan an daura auren wata kika tarewar zata dauke mu tsawon lokaci, kin ga mu na da wannan damar ta sanarwa duk wanda ya kamata, kuma ina ganin kamar be kamata acs mun daga maganar ba bayan da har mun fadawa su Baba cewar mun amince da haka
e dai kin matsa kina son auren nan a kusa Zahra, ni kuma ina ganin kamar akwai damuwa, kawai dai kin ki fada min ne
Na kirkiri murnushin da ya tsaya min a iya lefe na ce.
abu komai Mama
u ma ai ya kamata ace sun daga ko dan su bincika, ko da auren Abiey ma da na Deen duk ba su saka bincike ba, balle wannan, amman na tabbatar da ace mahaifinki yana raye zai bincika komai, Allah SarKi Allah ya jikan rai
meen
Na amsa ina wasa da yan yatsun hannuna ina jin wani irin ciwon zuciya marar misaltuwa, wata kila ma idan an daure auren ba zan yi wani tsawon kwana ba domin ciwon ya matsa min sosai tun daga lokacin da na amince zuwa yau.

Mama ce ta sanar da Hajiya Jamila zancen auren tsabar murna da farinciki sai ta ji kamar ta kama ni ta saka zane ta goya, hankalinta ya kwanta a yanzu ta samu sukunin cewar ba mijinta zan aura ba, a lokacin ne take sanar da Mama cewar ta san Sauban kanwarta yake aure wanda suke uba daya da ita, har take fadar auren na su ma be dade ba.

Da yamma lis Dr Hamid ya shigo gidan, sai da ya fara isa bangaren Hajiya Jamila sannan ya sanar min cewar na fito yana son magana da ni, ban yi mamakin zuwansa ba duk da kasancewar ya kwana biyu be shigo gidan ba, wata kila a yanzu ya zo ya taya ni murnar auren da zan yi ne, domin na san Hajiya Jamila zata sanar masa.
Chapter 101 · 0% Book details