← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 134

Sashe 33

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yake saukowa downstairs din yana gyara hannun rigarsa, Ammy dake zaune a kasaitacciyar kujera ta dago tana dubansa.
ai ina?

Ya dan yi shiru kamar mai tunani.
ai zan je na yi ma Mai Martaba bakwana gobe zan wuce
a kyauta, ka gaishe shi amman ga breakfast din nan yana jiranka
Ammy ta fada tana murmushi.
aybe zan karya a gurin Anty but yanzu bana jin zan iya cin komai
Ya daga kafadunsa shi kansa ba zai iya fadar abun da yake damunsa ba, kawai dai yana jin jikinsa ba dadi haka ma ransa a bace yake for no reason, sai ta nuna masa guri kusa da ita
auna Aliyu
Ba musu ya zauna ana sauke ajiyar zuciya a sirrance.
e yake damunka?
allahi Ammy ban sani ba, kawai dai na farka na ji ni wani iri, and ina son na tambaya ke kika ba Zahra kudin aikin ne?
a ba mun yi da kai cewar zaka saka a bata ba?
eah Sauban ya fada min ko da yaje biyan kudin ya tararda wani ya biya, na kira Dr da Anty sun ce duk ba su suka biya ba
oh ni ma ban biya ba, maybe Allah ya kawo mata wata mafitar ne
aybe
Ya fada yana mikewa tsaye.
a gaishe shi
Ammy ta sake fada sai ya juyo yana kallonta da murmushin da be san inda ya samo shi ba.
au kuma ke da kanki
anar na masa rashin kirki shiyasa
Murmushi yayi ya juya ya nufi kofar fita, da dan kuzarinsa ya sauko entrance din ya nufi motarsa tun kamin ya karasa ya danna key hannunsa sannan ya bude ya shiga motarsa yayi reverse.
10/1/22, 22:06 - Buhainat: Cikin natsuwa yake driving har ya fice daga gidan, be yi nisa da unguwar ba PA ya kira shi sai ya bude Bluetooth din dake cikin motarsa yayi connecting.
anka ya dade komai ya zama ready karfe biyar za su tashi gobe
Ya amsa sannan ya yanke wayar yana jin kamar ya fasa tafiyar, yana faka motarsa harabar masarautar Zahra ta fado masa a rai, ya kan irin wannan yanayin da kuma tunaninta a duk lokacin da take cikin wata matsala ko damuwa, wayarsa ya dauko kamar ya kira Sauban sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a ganinsa hakan be dace ba why zai yi ta neman shiga rayuwarta?

Bayan tana matar wani?

Ya bude motar ya fito da kafa ya taka har bangaren Anty, yana kokarin ya kai hannunsa ya bude kofar falon Aisha ta bude ta fito tare da kawarta, cike da murna ta tarbe shi.
yoyo Big bro daman ina ta nemanka, yau ma zan buga maka waya
kwai wata matsala ne?
h Babba
Ya kalli kawarta dake gaishe shi ya amsa sannan ya sake kallonta.
e ki dawo sai mu yi magana
kay Ya shiyasa na ke sonka
Ta fada cikin murna da jindadi, ya sakar mata murmushi kadan ya shiga cikin falon, kai tsaye ya nufi upstairs kasancewar babu kowa a falon sai Ac da plasma, Bedroom din Anty ya fara knocked sai da ta yi masa izinin shiga sannan ya tura ya shiga, idonta na yin arba da shi sai fuskarta ta cika da kyakkyawan murmushi.
aa Shaa Allah kamar ka san ina nemanka
Ya zauna saman kujera yana kallon yadda ta canja tsarin furniture din.
isha tace min akwai matsala?

Miya faru?
atsala ba yar karama ba, amman dai yanzu ka fara zuwa ka gaisa da Mai Martaba sai ka dawo mu yi magana
aman bankwana na zo masa, gobe zan wuce Abuja daga can zan hau jirgin England
utu zaka je?
o akwai wasan da zamu buga ne, kuma daman ina bukatar barin kasar nan
mman dai ba zaka dade ba ko?
an sani ba for now, wasan dai zai dauke mu for 3 days ban san adadin kwanakin da zan kara ba
llah ya ba ku nasara ya sa ayi a sa'ah
meen
Ya mike tsaye ya fice daga dakin, sai da ya leka dakin Narji duk da ya san ba lallai ne ace tana ciki ba a irin wannan lokacin saboda tana zuwa makaranta, ko bayan haka Narjin ba irin yan matan nan ne masu son zaman daki ba.

Ta cikin kofar falon ya kunna kai zuwa bangaren Mai Martaba, samun kofar yayi a rufe, hakan na nufin Mai Martaba ya fita daga turakarsa kenan yana fada ko kuma falonsa da yake ganawa da baki, a dole ya juya ya dawo ta cikin falon Anty, ya fita ta kofar falon ya fita daga bangaren gaba daya ya shiga bangaren Mai Martaba, jerin motocin Mai Martaba ya tarar a harabar fadar ko ba a fada masa ba ya san Mai Martaba fita zai yi ko kuma ya dawo daga wani gurin.

Yadda fadawa da dogarai suke mika masa gaisuwar suna zubewa kasa sai ka rantse da Allah shi ne dan sarki na fari ko kuma wanda ya fi kauna.

Be shiga fadar ba saboda hangota ta yayi a rufe sai ya nufi masaukin bakin Mai Martaba.
dan kuma ya disgani a gaban mutane fa?

Ya ayyana a ransa a tunaninsa zai tararda baki ne a falon, sai dai yana tura kofar falon ya shiga sai ya hango Mama Lami zaune a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba sai wata matashiyar yarinya da zata tofi Aisha kadan tana zaune daga kasa sanye da abaya ash colar sai madaidacitar jakata a gabanta dayan hannunta rike da tabarau.

Ba al'adarwa ba ce yin sallama idan ya shiga bangaren Mai Martaba saboda ya san Mai Martaba ba zai amsa masa ba, domin baya amsa sallamar kowa idan yana cikin mutane sai dai fadawansa su amsa, idan kuma daga shi sai iyalinsa ne ya kan amsa wani lokacin musamman idan zaman be wuce na mutun biyu zuwa uku ba, ko kuma matansa, sai da ko daga shi sai Mai Martaba ne a gurin Abiey yayi sallama Mai Martaba ba zai taba amsa masa ba saboda tsana.
a'alaikassalam
Mama Lami amsa masa sallamar da be yi kamar da gayya, kallonta kawai yayi ya risina har kasa da gaishe da mahaifinsa, be amsa masa ba sai ma dauke kai da yayi ya maida wani gefen kamar wanda yayi arba da makiyinsa, Abiey be damu ba daman inda sabo ya kamata ace ya saba da wannan yanayin.
aman na zo ne na yi maka bankwana za mu tafi England gobe da yardar Allah
Nan ma Mai Martabarta be ce masa komai ba, sai Mama Lami ce ta amsa masa.
aa Shaa Allah, Allah ya tsare ya kaiku lafiya kuma ya bada nasara
meen
Ya amsa da kamar dole.
tashi lafiya
Na fada yana kokarin tashi sai Mama Lami ta ce
biey baka gane wannan ba?

Ya kalli matashiyar budurwar da Mama Lami ta nuna masa sai ta dago ta kalleshi da manyan idonta, baka ce wulik sai dai irin bakin nan mai kyau mai shining irin na yayan manyan masu kudi.
an santa ba
Ya amsa a takaice.
mmiter ce kanwar Engr ce
Cewar Mama Lami.
thought ba Engr data muke da shi a Kano ba
ngr Bashir Alkali Auta daya ne dai a Kano
Mama Lami na fadar haka sai matashiryar da aka kira da Ummiter ta gaishe shi.
ood afternoon
ow are you
Ya amsa mata ba tare da ya jira ita ko Mama Lami sun sake magana ba, ya kalli Mai Martaba yana dan rankwafawa cikin girmamawa ya ce.
mmy ta ce a gaishe ka
Sai a lokacin Mai Martaba ya daga masa hannu ya daga masa kai a lokaci daya alamar yana amsawa, Mama Lami ta dan sauke kai kasa Abiey kuma yayi murmushi kadan sannan ya ya juya ya fice.

Mama Lami ta bishi da kallo kamin ta kalli Ummiter.
ashi ki tafi tun da kun gaisa, daman dai tace duk zuwan da take bata taba ganin Mai Martaba ba shiyasa yau ta zo ta kana nan na ce ta zo ta gaisheka
Ya mike tsaye tare da jakarta ta yi ma Mai Martaba a tashi lafiya sannan ta fice.

Wannan karon a karamin falo ya samu Anty zaune tana jiransa ita da Aisha, sai da ya karewa fuskokinsu kallo sannan ya zauna.
a yi breakfast ma kuwa?

Anty ta tambaya sai ya girgiza mata kai alamar aa, tun kamin tace komai Aisha ta tashi ta fito daga falon ta nufi dinning.
10/1/22, 22:06 - Buhainat: ZAHRA POV.

Duk yadda zan bayyana yadda mace take ji idan ta rasa miji sai na ga kalmomin kamar ba za su hadu su wadatu na isar fassarar yanayin ba, shiyasa wasu suke cewa mutuwar miji ta fi ta uba ciwo, sai dai ni a yanzu na kasa banbancewa tsakanin rashin uba da muka a shekarun baya da kuma rashin miji da na yi a yanzu.

Musamman da dare yayi zan kwanta sai yanayin yadda muke kwance ya dawo min a rai, ko tufafinsa na kallo wani abun nake ji yana ta so min, sai dai fa kam hawaye Allah ya dauke min su, ba sakafai suke zubo min a ido ba idan dare yayi bana kwana sai na tashi na raya dare da addu'a ina rokon Allah ya yafewa mijina ni kuma ya bani juriyar cin jarabawar da na fada.

A haka dai har aka yi sadakan uku a ranar kan na shiga tashin hankali sosai domin na tabbatar Deen ya tafi ya bar ni kenan har abada, ba laifi mun yi ta samun abinci daga abokansa yan'uwa da makota kowa yana ta kawo mana daidai gwargwadon hali, har mai gidan da muke haya sai da ya kawo mana abinci kuma yace idan muna bukatar wani abun na fada, duk wata soyayyar irin ta bahaushe da kuma dangantaka ta musulunci an nuna min ita sosai kuma na yaba domin ba ko wane musulmi ne yake samun irin gatan da na samu ba a cikin yan'uwan miji da makota na nesa da na kusa.
Chapter 33 · 0% Book details