← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 134

Sashe 8

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mun shiga daki ya shigo ya gaisa da mahaifiyarsa a lokacin ba hijab ba har riga na cire na ja zanen na zuwa saman kirjina na haye gadon Hajiya ya kwanta, be wuce minti talatin ba yayi mana sallama ya fita da niyar anjima zai dawo ya dauke ni.

A gidan na wuni, da rana Hajiya ta min kwadon kanzo da zogale na ci, da yamma ta siyo min cornflakes na sha da dare kuma ta yi min tuwon shimkafa da miyar ganye na ci iya cina har sai da na rasa gurin numfashi.

Ina gama sallah isha'i na shirya na fito waje kasancewar an dauke nepa, kuma ba gidan masu abun duniya ba ne balle a kunna min engine, na zauna kan tabarmar da Hajiya take zaune na dora kaina a cinyarta.
ajiya solar ku ta lalace?
h Wallahi aikin Bahijja ne, kin san komai ita nata sai ta yi shi da hauka
Dariya na yi Bahijja ma dariya ta yi.
ajiya dan kin ga Zahra kike min wulakanci?
o ga yata me zan yi da ke?
hmmm Hajiya fada mata dai...

Na fada ina hamma.

Shiru shiru har goma na dare Deen be zo ba, hakan yasa na kira shi a karamar wayata, be daga ba.
e daga kiran ba
Na fada ina Kallon Hajiya, sai ta dan kalleni ta dauki wayarta ta kira shi ga mamaki na sai na ji tana magana da shi duk da kasancewar ba zan iya jin muryarsa ba, bayan ta sauke wayar ta kalleni.
ace wai ki kwana nan, dare yayi sosai kuma anyi fada a unguwarku wai police suna kame ba zai iya fitowa ba
Gabana ya fadi, domin a iya sanina Deen baya yarda na kwana a wani guri ba kusa da shi ba.
mman miyasa be daga kirana ba?
ai yaje ya daga sai wayar ta tsinke, zai kira kuma sai na kirashi
Ban sake cewa komai ba, sai dai ina ta kallon wayata ina jiran kiransa ya shigo min domin mun saba idan har na kwana ba gida ba kamar idan tafiya ta kama zuwa wani gari to zai kira ni a waya mu yi hira, amman shiru be kira ni ba, yanayin Hajiya da Bahijja sai ya canja, sai dai ban ce musu komai ba suma kuma basu nuna min wata wani abu ba, sai dai ni na karanci damuwar dake fuskarsu wanda suke kokarin boyewa.

Washe gari bayan Hajiya ta yi min tea kuma ta dumamamin tuwon jiya, ga koko da kosai da ta saka aka siyo min duk ni kadai, amman na kasa cin ko daya saboda ban ji muryar mijina ba, na kai hannu na dauki wayata na kira shi sai ga kiransa ya shigo.
10/1/22, 21:59 - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/IjtvyonRYfu5VBfSh4VRBX
CIWON - SO
By Khadeeja Candy
*For advert contact 08036126660*
na ta jiran ka kira ni tun jiya baka kira ba, kuma ka san idan ban ji muryarka bana oya bachi
Na fada a shagwabe bayan na dauki wayarki.

Sai yayi dariya
abe ayi min afuwa
iyasa baka kira ni Deen
Na tambaya cike da damuwa domin na ji muryarsa ba a yanayin dana saba jinsa ba.

Sai yayi kamar mai tunanin abun da zai fada min.
a je kallon kallo ne sai hankalina ya dauke sosai kuma a lokacin da na dawo na san kin yi bachi so bana son na tashe ki
aka saba yi min karya ba Deen, kallon kallo a daren da kace police za su kame?
eah bayan mun dawo ne muka samu labari kuma a lokacin na san kin yi bachi shiyasa ban kira ba
mman ni na kira ai, kuma na san kallon kwallo be tana hana ka kirana ba
es lokacin wayar tana silent ban sani ba
t the same time Hajiya ta kira ka kuma ka amsa?

Ajiyar zuciya na ji ya sauke, sai ya sassauta muryarsa.
ahra, can you trust me?
es one thousand percent, but that doesn't mean to lie to me...
abe na i don't want to hurt you
urt me like how?
o ba zan ci komai ba sai ka fada min, haka zan wuni da yunwa
Na fada saboda na san shi ne tashin hankalinsa rashin cin abincina, ya san duk yadda na ke fushi bana fushi da abincin, kuma bana bakunta da abincin, idan har na ki cin abinci hakan na nufi damuwar tawa babba ce sosai.
erious bana da lafiya Zahra kuma bana son ki sani ne saboda kar hankalinki ya tashi?
e ke damunka?
iwon kai ne, tun da na aje ki na dawo kaina ke ciwo na sha magani yaki sauka, amman dai yanzu Alhamdulillah
o dan bana kusa da kai ne
amar kar mu rabu Babe na
a ci wani abu?
eah na karya, kuma yanzu zan tafi asibiti
llah ya baka lafiya Deen
min i love you
love you more
Sai da ya sumbanci wayar na ji karar kiss dinsa sannan ya kashe, gaba daya sai jikina yayi sanyi domin komai na mijina ina daukarsa da muhimmanci, ko da kan akaifarsa ya ce yana masa ciwo zan ji kamar nawa ne.

Haka na tasa kayan karyawa na saka a gabana na kasa taba komai, gaba daya na ji bana sha'awar cin komai.
ahra baki ci abincin ba?

Ko wani abu kike so a dafa miki?

Na dago cike da damuwa na kalli Hajiya da shig
owarta kenan take min maganar tana rike da kofin koko da alama kanta ta zubawa.
ajiya kin san Deen ba shi da lafiya kuma ba ki fada min ba
Wani irin dauke numfashi ta yi ta sauke ajiyar zuciya, a take idonta ya cika da kwalla, sai ta zo kusa da ni ta zauna ta aje kofin kokon.
dan ma na fada miki ai ba magani zaki masa ba, muna gudun ki shiga damuwa ne shiyasa muka boye miki, a kullum tsoronsa kar ciwonsa ya jefa ki cikin wata damuwa
Hawayen da na gani yana sauka a idon Hajiya, da kuma kalamanta sai suka ba ni mamaki kuma suka tabbatar min cewar ba a yanzu Deen ya fara ciwon nan and that's mean akwai abun da suke boye min, ina tsaka da tunanin abun da zan fada ko na tambaye ta da zai kara fito min da ainahin abun da yake damun mijina sai na ji ta yi sara a gabar da nake so.
duk lokacin da na yi masa maganar neman magani, sai Hajiya dan Allah a boye maganar nan saboda Zahra, mijinki yana sonki Zahra, irin son da ban taba gani ko jin wani yayi ma matarsa a tahirin rayuwata, ni kuma dole na so abun da yake so
Ta karasa min daker kuka na cinta, wanda hakan yayi sanadiyar shigowar Bahijja dakin da sauri.
afiya?

Na kalleta da danuwa da babu kuka kuma babu alamunsa a kusa da idon na ce.
e ma kin san Deen be da lafiya?

A take yanayinta ya canja sai ta matsa kusa da ni ta zauna.
a sani...
i miyasa kuka boye min me hakan zai amfana min?
hi ya bukaci a boye miki, cewa ya yi idan kika sani hankalinki zai tashi shi kuma baya son abun da zai daga miki hankali
un yaushe yake fama da ciwo?

Ta share hawayen da suka zubo mata.
ai bayan ya aureki muka sani, amman yace mana tun kamin ya aureki yake fama da ciwo
iyasa ba a nemi magani ba?

Na tambaya ba dan na sani ba, sai dan na kara ba su damar fito da abun da suke boye min.
eman magani Zahra ba na mai karamin karfi ba ne, ya je asibiti ance ciwon hantar ya kai wani mataki da yake bukatar naira miliyan bakwai ko sama da haka ma inda hala
Wallahi ban san lokacin da na sake duban Hajiya dake maganar ba, ina kokarin sauke numfashi sai ya makale min a kirjina ya ki sauka.
iliyan Hajiya?

Hajiya Mijina?

Na kama hannayenta na rike abun da ke cikina sai motsi yake da karfi, a lokacin ne na gane hawaye ma kala kala ne.
a cire rai daga rayuwa ko?

Shiyasa kuka rumgume hannayena ke da shi kuka saka ido kuna jiran mutuwarsa?

In ya so ni na shiga duk halin da zan shiga?

Ina magana muryata na rawa saboda numfashina yaki ya daidai ga kuma cikina sai haye min yake saman zuciya, da sauri na kwanta a gurin wasu hawaye masu mugun zafi na sauko min.

Hajiya ta yi saurin kai hannu ta taba ni
ahra?

Lafiya?

Shiyasa ya ce kar a fada miki saboda zaki shiga tashin hankali
ashin hankalin da zan shiga idan na rasa mijina ya fi gaban duk wani tashin hankali a duniyar nan!

Hajiya ina son mijina
Na fada kuka na fin karfina sai na yi saurin saka hannu na rufe bakina, na lumshe ido ina jin kamar na bude na gan ni a kusa da mijina.

Daker nake iya hade yawun dake tararmun a baki.
ahijja dauko ruwa
Hajiya ta fada ganin ina numfashi daker.

Da sauri Bahijja ta miko mata ruwan da aka kawo min na ci abinci sai na karba da sauri na fasa pure water na sha daga kwancen da nake, a lokacin ne na ji na samu sa'ida, a take na zabura na tashi zaune.
ahijja samo min Napep kofar gida
na zaki je?

Na amsawa Hajiya ina dannar zuciyata.

Sai Bahijja ta jefo min wata maganar da ban san lokacin da na daka mata tsawa ba.
oh ki ci abincin mana ki karya
a zan ci ba...

Na amsa mata da karfi hawaye na sauko min.

Tashi ta yi tana share hawayenta ta dauki hijab dinta ta fice, cikin karfi hali na mike tsaye na nufi inda Hijab dina yake na dauka na saka ban tsaya bin ta kan niqab ba na dauki jakata na nufi inda talkamina suke ina kokarin sakawa wani irin kuka marar misaltuwa ya subuce min har sai da na jingina da kofa ina jin zuciyata na mini wani irin zafi kamar an hura wuta.
Chapter 8 · 0% Book details