← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 134

Sashe 43

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamin ta karasa ya tare numfashinta.
o Dr this will be the last favor please
Ta ja dogon numfashi ta sauke ba dan ranta ya so ba.
an je da safe
o yanzu please kamin ki wuce gurin aikin, idan kin gani ko ji wani abu sai ki fada min a waya, but hankalina ba zai kwanta ba yanzu har sai na san halin da take ciki
ai ba mala'ika ba kai ba aljani ba kai ba kowa ba sai ka rika cewa kaji kaza kaza Zahra bla bla haba
iwon so kenan mai hana mai yinsa zama lafiya
Na fada yana murmushin dake nuna shi kadai ya san abun da yake ji.
mman zuwa gidan mutane da dare?
a fi sirri ai, kuma kin ga yanzu ba zan iya bachi ba sai na san halin da take ciki
an biya ta can kamin na je asibiti
Ta fada tana bude motarta ta shiga, shi ma ya juya ya koma gurin motarsa ya shiga sai suka fita a tare sai dai direction din kowa dabam.
murdawa da marata ke yi kamar abun cikina zai fito, na dan motsa saboda azabar ciwon da nake ji sai na ji wata muryar da ban sani ba sunan kiran.
alama Malama Malama
Kalmar nake ji yana ta maimaitawa, kwakwalwata na ta hadawa amman na gagara fahimtar ma'anar kalmar da kuma yaren da yake magana da shi.
ini fa take bukata ta zubar da jini mai yawa...

Na sake jin wata maganar da ban fahimci me take nufi ba, can kuma na ji wani ya ce
u gwada jinina mana idan zai yi sai a saka mata
saboda azabar da nake ji, na maida idon na rufe ina numfashi kamar ba ni ba, bana jin kuzari ko kadan sai azabar murdawar mara, ina jin lokacin da aka daura min wani abu a hannuna aka buga hannu aka shafa min wasu ruwa sannan aka soka wani karfe a cikin jijiyata aka cirewa, komai kamar mafarki nake ganinsa.

Nan ma ban fahimci abun da suke fada ba, ni dai taimako kawai nake nema idan suka ce zasu raba ni da abun da ke cikina ma zan yarda
ankalina ba zai kwanta ba sai matar nan ta tashi she saved my life
Wannan karon da yare biyu akayi magana sai dai hakan be saka na fahimci komai ba.
uje a gwada jinin
Shi ne last sentence da kunnena ya jiyo min, sai kuma numfashin ya tafi dan sauran hankalin daya rage min ya cire gaba daya.

Wannan karon na bude ido da dan kuzarina idon nawa kuma nawa kar ina ganin komai farin ceiling na fara arba sa shi fanka na juyawa a hankali, can kuma na juyo idona gorar jini ce abun da na fara yin karo da ita kamin na kalli hannuna da jinin ke shiga ciki, sai kuma na juy
a dama da ni na kalli
Hafsat dake kwance tana bachi, da alama dare ne sosai domin alamu ya nuna haka
yanayin yadda na ji tsit ta ko'ina ga kuma hudun da nake hangowa ta windows, na kai hannuna na taba cikina sai kuma na dan dago na kalli cikin, wata katuwar rigar ce a jikina sai kuma zanen da aka rufe min kafafuwana da shi.
lhamdulillah
Na furta cike da nauyin baki, ina tabbatar da godiya ta ga wanda shi kadai ke kashewa ya raya, na yunkura ina rika karfen gadon na tashi zaune na mika hannu zan riko gorar ruwa sai gora ta fado kasa wanda hakan yayi sanadin tashin Hafsat.
wani....

Sannu ya jikin
Na daga mata kai ina nuna mata ruwa.
a likitoci sun ce kar a baki komai sai an cire jinin
na jin kishin ruwa sosai
i yi hakuri kin ga dare ne, ba zai yiyu na kira likita ba tun da jinin ma be yi nisa ba gora ta biyu ce aka saka miki, kuma na karya alkawarin da na daukar miki na ji tsoro sosai saboda jinin da yayi zuba na dauka mutuwa zaki yi, na kira Anty na ce ta fadawa Mama kina nan gurina kuma muna asibiti dake
Ban ga laifinta ba, domin ko nice a halin sa take ciki abun da zan aikata kenan.
a ni da kowa a nan likita ina son na koma Kano gurin mahaifiyata a can ma za a iya kula da ni
aki da wanda zai zo zaria yayi jinyarki?
zaria nake?

Na tambaya ina kallon Hafsat sai ta daga min kai.
a ma dauka haihuwa ce sai suka ce ba haihuwa ba ce wai matsala dai kika samu
Na koma na kwanta na lumshe ido sai hawaye suka ce sallamu alaiki, idon da ban sake budewa ba kenan har safe, shi ma saboda na ji ana kokarin cire robar jinin dake hannuna ne.
annu Madam
Likitan ya fada yana sakar min murmushi sai na amsa masa da kai na tashi zaune.
ikita za a iya sallamata a yau?
a gaskiya muna bukatar mu tabbatar da kin samu lafiya sosai
h ke da shi nan aka kawo ku saboda a baku taimakon gaggauwa, amman shi mutune na ji ance ya koma kano tun jiya saboda ba wani ji rauni sosai ba
Na kalli likitan.
a taimaka min da Allah, hankalin mahaifiyata zai tashi idan ba a kano nake ba
oh indai haka ne sai dai mu miki transfer daga nan zuwa asibitin dake Kano
h na yarda hakan zai fi min sauki ma
Da wannan ya yarda sai ya fita ya bar wata nurse tana balla magani ta bani, sai na karba na aje har sai da na karya da lafiyayyen abinci da aka kawo mana daga wata babbar hotel dake zaria sannan na sha maganin, ina gama sha likitan ya shigo tare da Nurse din dazun ya mika min takardar transfer.
ashi sannan maganinki idan aka miki allura ba zaki sha magani ba, kuma ki tabbatar kije aaibitin da muka turaki, sannan Alhaji Bashir yace idan kika farka a asanar masa, na fada masa kin farka har kin nemi transfer yace a miki kuma ya vada umarnin daukar nauyin duk wani ciwo na ki, saboda haka na kira likitan dake Aminu Kano na sanar da shi komai idan kin isa sai ki nemi Dr Hassan ki ba shi wannan file din wannan kuma number wayarshi ce
Ya karasa yana miko min number da kuma file dina.
a gode Likita
Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleni.
hm yace ki dan jira za a kawo miki sako kamin ki tafi
Na daga masa kai.
llah ya bada lafiya, ko da yake dai mun yi solving din komai sai dai dan a kara tabbatarwa
Wannan karon Hafsat ce ta yi masa godiya, ya fice tare da nurse din yana murmushi, kana ganinsa kasan irin likitocin nan ne masu saukin kai.

Yana fucewa na kalli Hafsat na ce.
na jakata?
ata nan na aje miki karkashin gado, daman na zo da ita ne da tunanin ko za a kashe kudin magani sai gashi mutumen ya dauki nauyin komai ba a taba kudinki ba
an Allah ki raka ni na hau mota kin ji
in ji fa abun da likitan ya fada yace mutumen yace ki jira za a kawo miki sako, kuma ba ki sani ba ko su Mama suna hanya
ama ba zata zo nan
aboda me?
a san wacece mahaifiyata Hafsat, ba zata zo nan ba, muje ki raka ni na hau mota
Na share hawayena na tashi tsaye tare da gyara daurin zanen dake jikina.
ufafinki fa suna gida na bada a wanke saboda zanen duk ya lalace da jini, amman ga hijab dina nan na kawo miki
a gode
Na furta ina jin wani abu kamar kwallo yana min yawo a zuciya, duk yadda Hafsat ta so na tsaya dan karban sakon da likitan yace za a kawo ban tsaya ba, saboda zuciyata ba a can take ba, kuma ban san wane kalar sakon ba ne.

Ina takawa a hankali har muka fito cikin asbitin tun daga yanayi da tsarin aaibitin ya isa ya sanar maka cewar asibitin ta kudi ce irin wannan mai zaman kanta, domin an tsara asibitin da kyau kai kace ma a garin Abuja kake ba Zaria ba, muna fitowa Hafsat ta tare min mai Napep ta saka yan komatsan data kwaso na tabarma da sauran abincin da muka rage da kuma yan kayanta, sannan na shiga ita ma ta shiga ta fadawa mai Napep din inda zai kaimu, yana fara tafiya na bude jakata na kirga 5k a cikin kudina na mika mata.
a wannan ki bawa Inna
Na sake kirga 5k na mika mata.
annan kuma na ki
aba Uwani ni ban baki ba kuma zan karba?
a bani da su ai ba zan baki ba
a gode Allah ya saka da alheri, kuma dan Allah ki yi hakuri da kiran Mama da na yi na rikice ne shiyasa
a ki yi laifi ba ni ma abun da zan aikata kenan idan kika samu kanki a cikin wannan halin na gode da kulawa kuma ki min godiya a gurin Inna
e muka miki na godiya, ai kin fi haka idan ma mun yi
Muna isa tashar na fita, sai ita ma ta fito.
i koma Hafsa ai zan iya shiga mota da kaina na gode
Bata ce komai ba sai ta rumgume ni ta fashe da kuka.
llah ya yaye miki damuwarki kawata ya miki mafita
meen
Na furta ni ma cikin kuka sannan na sake ta.
ai wata rana Hafsat idan muna da rabon ganawa
an da kwana biyu zan zo Kano na dubaki da yardar Allah, Allah ya kaiki lafiya
Na ciro kudin mai napep na mika masa sannan na nufi gurin da aka faka motar Kano.
Chapter 43 · 0% Book details