← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 134

Sashe 13

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai na kasa amsa mata, hawaye na ne kawai suke sanar da ita ba lafiya ba.
nnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, fada min miya faru yar'uwata
Ta fada tana kokarin fashewa da kuka ta jani jikinta ta rumgume.

Ta san ni da saurin kuka idan aka bata min rai ko na nemi wani abu ban samu ba, idan Mama ta min fada lokacin da ina gida gurinta nake zuwa ina mata kuka, sai ta yi ta rarrashina ko ta kira ta bawa Mama rashin gaskiya idan ni ce mai gaskiya, sai dai duk lokacin da nake cikin tsananin damuwa yar'uwata tana fahimtar halin da nake ciki fiye da mahaifiyata, sai dai idan muka tashi fada kamar abokan gaba muke wani lokacin yar yayan ma da nake ce mata sai na ki fada, sai dai ba kasafai take biye ma shirme na ba kasancewar ta fini hankali da shekaru da tunani.
een ba shi da lafiya, ciwon anta yana damunsa
Shi ne kawai abun da na iya furtawa cikin kukan.

Sai ta share hawayenta ta dago da ni jikinta na fuskance ta.
aboda yana ciwon anta ba shi ke nuna zai mutu ba, babu wanda ya san lokacin mutuwar wani sai Allah, karki daga hankalinki da yawa Zahra kina da ciki tsoho
Furucin da ta yi ya tabbatar da ta san halin da mijina yake ciki kenan.
in san Deen be da lafiya daman?
a sani, amman shi ya roki kar a fada miki
Ta amsa min tana daga min kai.
aushe kika sani?
ayan aurenku
iyasa kuka boye min?

All this while Deen ke hidima da ni bayan kuma ni ya kamata na yi masa komai
ijinki na son ki Zahra, ya zauna a inda kika zauna yanzu ya roki na boye miki saboda idan kika sani zaki tashi hankalinki kuma kullum zaki rika yi masa kallon zai tafi ya barki ne, na rantse da Allah Zahra da ace ya san zai aureki da be jefa kansa a cikin shaye-shaye ba, kuma na tabbatar kaunarki na daga cikin abun da ya kara jefa shi a cikin wannan halin, yace yana tausayin halin da zaki shiga idan baya raye, ya fada min cewar ya bani amanarki ko da baya raye saboda ya san na fi shakuwa da ke fiye da kowa
Da sauri na share hawayena na mike tsaye sai ita ta tashi tsaye.
na zaki?
ida zan dauko kudin da yake ajiya zamu biya kudin test 30+ kudin ma ba zai isa ba
awa ne?
shiri
Na amsa ina kara goge hawayena so nake na karfafawa zuciyata cewar ba zata rasa masoyinta ba kuma makusancinta.
kwai kudin da nake ajiya wanda zan miki hidima idan kin haihu zan baki shi ki kara
Tana fadar hakan ta nufi dakinta sai gata ta fito rike da 40k ta miko min.
ubu arba'in ne, ki rike shi kamin mu ga abun da Allah zai yi, domin na san yanzu bayan test din magani za a rubuta masa
a gode Yaya Maryam
Na fada ina juyawa sai ta kira ni.
ar'uwata
Na juyo hawaye na bin fuskata.
an Allah ki kwantar da hankalinki ki bar wa Allah komai Inshallah Deen zai samu lafiya kinji?

Kwantawa na yi jikinta na fashe da kuka, sai ita ma ta fara sabon kuka tana jijjigani alamar rarrashi.
abu abun da zai faru, sau nawa ake ciwo kuma a warke a samu sauki, zai samu sauki kinji
es Inshallah
Na furta daker sannan na sake ta na juya.
ace asibitin aka kai shi?

Ciwon taso masa yayi
minu Kano, eh amman boye yayi sai da na ji a gurin Hajiyarsa
a zaki zauna ki ci abinci ba Zahra?

Dan wake ne fa
Na amsa ina jin cewar ko ruwa ba zan iya kurbawa ba balle abinci, da sauri na fice daga gidan, kai tsaye na juya domin komawa asibitin na san kudin da Yaya Maryam ta bani zai isa na biya na test din, a kafa nake tafiya kamar yadda na je a kafa, ban isa asibitin ba kiran Mama ya shigo wayata, sai na bude jakar na dauko karamar wayata na amsa kiran na kara a kunne.
ello Mama
a'am Zahra, kina ina?
na hanyar asibiti
anzu Maryam ta kira ni ta fada min abun da ya faru, karki je ko'ina gani nan zuwa kin san dai kina da ciki ko?

Karki saka kanki a damuwa kin ji Zahra ta
oh Mama
llah ya miki albarka, ya sauke ki lafiya
Na amsa sannan na kashe wayar, wani teburi na samu na zauna ina tuna irin halin da Mama ta shiga lokacin data rasa mahaifinmu, fadi tashin rayuwa babu wanda ba mu magani ba kamin Allah ya kawo mu a inda muke yanzu, kuka babu irin wanda mama ba ta yi ba na rashin mijin sai da ita ta jure tun da gashi har ta auri mahaifin Deen sai dai ni fa?

Anya zan jure?

Anya zan iya rayuwa idan na rasa mijina?

Abokin rayuwata?
a zan ma rasa shi ba, babu abun da zai faru zamu yi rayuwa kamar yadda muka saba nothing will ever change
Na fada a fili ina share hawayena sannan na tashi na karasa cikin asibitin, sai da na fara kiran Hajiya na ji inda suke sannan na nufi ward din.

Katon gurine da ake aje marasa lafiya kowa da gadonsa da kuma number gadonsa an saka lalule a ko ne gafe gaba dayan dakin maza ne, sai wadanda suke jinyarsu wasu mata ne wasu kuma maza.

Tun na doso inda suke yana kallona har na karaso.
a jikin?

A maimakon ya amsa min sai ya sakar min murmushi ya nuna min gurin zama saman gadon kusa da shi Hajiya kuma tana zaune saman kujerar roba.

Zaunawa na yi kamar yadda ya bukata sai ya kurawa fuskata ido yana kallon yadda idona ke nuna na sha kuka.
uwa kika yi kika samu guri kika zauna kina kuka?

Ta tambaya da kamar fada, abun da be saba min ba.

Sai na sauke kaina kasa ina jin wasu hawayen na cika min ido.
ahra ko fada aka mata ai zata iya kuma balle kuma ta samu dalili
hiyasa tun farko ban so ki sani ba, saboda ina ciwo sai aka ce miki mutuwa zan yi, idan ma mutuwar ce kukanki zai hana ta zuwa ne hala?

Ban ce masa komai ba na bude jaka na dauko kudin da Yaya Maryam ta bani na mika masa.
aya Maryam ce ta bani dubu arba'in ka tashi muje a yi awon
a zan je ba
Na kalleshi ina hawaye sannan na kalli Hajiya, sai ta daga min hannu.
annan kuka da kike yi shi ke kara daga masa hankali
Na yi saurin share hawayen da suka ki tsaya min.
a bari tohm
Ya kalleni.
un yi shawara da Hajiya idan mun je an yi test din an fada mana matakin da ciwon yake zamu koma gida mu nemi kudin magani idan mun tara sai mu dawo asibitin
h hakan zai fi, kin ga shi ma sai ya tashi tsaye da neman magani
mman ba zaka samu matsala ba idan ka cigaba da zuwa aiki kuma ga ciwo
a mu bincike likitoci mu ji
Na daga masa kai.
hikenan
Ya fada yana min murmushi, Hajiya ta fara mikewa tsaye sannan Deen nima na sauko ba tare da jin kunya ko tunanin komai ba ya rika hannuna muka fice daga gurin Hajiya na gaba, mutane sai kallona suke.
na mask dinki?
an sani ba
Sai a lokacin na tuna da na fito gida da mask, be sake min hannu ba sai da ya ga Hajiya zata juyo sannan na yi saurin fisge hannuna, idan ta shi ba saki zai yi ba.

Sai da muka fara zuwa gurin test din sannan muka biya aka masa hoton, kamin mu dawo dakin da aka ba shi gadon Mama ta kirani ta tambaye inda nake na fada mata sai ta same mu a can.

Nurses din da suke gurin sai suka fada mana inda zamu kai hoton, a tare da ni da Hajiya da Mama da shi kansa Deen muka nufi office din likitan.

Muna daf da shiga Deen ya tare ni sai da Mama da Hajiya suka shiga sannan ya ce.
i jira mu a nan
aboda me?

Na tambaya ina daga kai na kalleshi.

Sai ya ce
marni nake baki
Ba da wasa yake bani umarnin ba domin fuskarsa ta nuna haka.
oye min da ka yi a can baya be isa ba Deen?

Na fi kowa kusanci da kai, kuma na fi kowa hakkin sanin abun da yake damunka da komai na ka, hakan da zaka min zaka kara tayar min da hankaline kawai
Runtse ido yayi ya bude.
ahra na san halinki tashin hankalin da zaki saka kanki zai fi daga min hankali fiye da ciwona
aya sani ko idan suka duba za su ce maka ka samu sauki ne gaba daya?

Ba zan tayar da hankalina ba i promise
Ya sakar min murmushi, sannan ya rika hannuna wannan karon ban hana shi ba duk kuwa da kasancewar na san Hajiya da Mama za su gani sai dai hankalina ba akan su yake ba yana akan abun da likitan zai fada.

ABIEY POV.

Anty na shigo falonta ya mike tsaye sai ta yi murmushi daman ta san ita yake jira.
ow what?
ow what Anty?

Bayan kin hana ni magana a gaban Mai Martaba
Ta nuna masa kujera.
auna Abiey
Baya son musa mata shi kawai dalilin daya saka shi zaunawa.
annan wata nasara ce, kuma kauna ce kawai dai an duburbuce Mai Martaba ne ba zai iya maka magana cikin lafazi mai dadi ba, kuma ba zai iya nuna maka soyayyar ba, amman ni na san Mahaifinka yana kaunarka Abiey, ka fada min a cikin gidan nan akwai wanda ka taba jin Mai Martaba ya ba shi dogarawa da sunan a tsare shi?
Chapter 13 · 0% Book details