← Book details Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 134

Sashe 127

Ciwon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dakin Yasmin ta shiga ko da ta shiga ta same ta har ta saka hijab dinta tana ganin Momy ta boye fuska tana jin kunya.
e kitchen ki sama masa abun karyawa ki fitar masa da shi
*** *** ***
Abiey na zaune cikin motar yana video call da Zahra ya hango Yasmin ta fito dauke da faranti sai yayi saurin gyara zamansa.
iayatee i will called you back Okay
iya faru?
a komai wani abu zan yi, ina gamawa zan je gurin Mai Martaba idan na dawo sai na zo na dauke ki mu tafi shopping din, i love you
love you more
Ya sumbanci wayar sannan ya daga mata hannu ya kashe, hakan yayi daidai da bude front seat da Yasmin ta yi da dayan hannunta ta shiga ta zauna, amman ta ki yarda ta kalli inda Abiey yake zaune kuma ta ki tace masa komai haka ma ta kasa boye fushinta.

Abiey yayi murmushi mai sauti ya mika hannu ya karbi tray ya dora a jikinsa.
a san na yi laifi, amman neman yafiya na zo fa ko karyawa ban yi ba
Ta nade hannayenta ta juya masa fuska.
in tana ganin mace ta yi fushi da mijinta?

Haba Yasmin ayi hakuri ma, mun shirya abun ne a boye ban yi tunanin abun zai zo mana da sauki har haka ba, Yasmin kin san ya so yake ba ki bukatar na fada miki komai ina jin da ace na rasa Zahra a karo na biyu ke ma da kin rasa ni, amman yanzu Alhamdulillah komai ya wuce
ai a jarida na ni fa Abiey
an san an saka a jarida ba, ban kuma san waya saka ba bayan mun gama waya dake Mai Martaba ya kira ni yake fada min abun da yake faruwa kuma yace min yanzu haka ya saka a kawo masa wanda ya buga labarin daga nan gurinsa zan tafi, domin sun buga labarin ne da nufi bata suna, secondly sune wadanda suka wallafa wacan labarin na rushe gidan da aka yi, ban san inda suke samo labarin ba.

Yanzu ni dai tuba nake a yafe min
Ta dan saki fuska.
na Zahra take?
ana gidansu ko na kawo miki ita?
a na sani ni ko bata son gani na
Ya wara ido.
aboda me?
ata ce ina son mijinta mana
ina son mijinki dai, babu zance ni mijin Zahra ne ko mijin Yasmin ni mijin mace biyu ne a yanzu da dai ace Zahra kawai nake aure to zan zama mijin Zahra ita kadai, amman Allah yayi min kyauta da kyawawan mata har biyu a lokaci daya
Ta yi murmushin jindadi ta sauke kai kasa domin bata yi zaton jin haka daga gareshi ba.

Ya maida hankalinsa gurin abincin ya fara ci.
hhhh waya girka wannan?
i ce
a ban yarda Momy ce
allahi ni ce
aman haka kika iya girki?

I thought Islamiya bata barinki girki ai, i got lucky daman ina son macen da ta iya girki kuma ta iya tsabta
Haka yayi ta zuba santi wani abun da gangan yake yinsa saboda ya saka ta nishadi kuma yayi nasarar yin haka domin ya tafi ya barta zuciyarta fes sai dariya take.

Daga gurin Yasmin Abiey ya wuce gurin Mai Martaba kai tsaye bangarensa ya nufa babu tsayawa neman iso a gurin Anty duk kuwa da ya san yau din ba girkinta ba ne girkin Hajiya Kilishi ne.

Yana shiga da sallama Mai Martaba ya amsa masa yana murmushi da jindadin ganinsa.
12/28/22, 11:23 - Buhainat:
abana
Hajiya Kilishi ta sake waigawa ta kalli Abiey da kyau domin tabbatarwa idan shi din ne ko waninsa, Abiey ya karasa gaban Mai Martaba ya kwashi gaisuwa sannan ya zauna Mai Martaba ya mika masa mug din tea dake hannunsa, sun tattauna abubuwa kadan a ciki har da abun da Mai Martaba yake son yayi handled, sai da Hajiya Kilishi ta fita sannan Abiey ya tambayi Mai Martaba.
n gano maka shi?
h an gano shi, ai ba boyayyen mutum ba ne, kuma ba shi kadai na saka a kama ba har da wadanda suka buga wacan labarin, dole akwai hannun wani a ciki ko dai daga cikin gidan nan ko kuma daga bangaren abokanka ko kuma bangaren ita yarinyar
i ma na yi wannan tunanin, domin wacan karon ma ba ni na saka a rushe gidan ba amman aka rusa saboda a bata min suna kuma a ja min zagi
a mu gane ko waye tsakanin yau da gobe, masara idan ta ji wuta ita ke da
Daga haka Mai Martaba ya rufe babin maganar ya dauko zancen nadin sarautar da za ayi masa cikin satin nan.
amanka ta kawo shawara wai tana ganin kamar ka tare kamin lokacin zai fi armashi a kafin nadin sarautar, tun da bayan nadin sarautar da wata daya za a daura aurenka da Yasmin, ina ganin mu dai daga bangarenmu babu wata matsala idan ka shirya
Abiey ya sauke kansa kasa sosai ya jidadin shawarar da Anty Amarya ta kawo daman ta yi masa wannan maganar tun shekaranjiya.
h to Mai Martaba idan haka yayi muku ni ma ta gurina babu matsala sai dai na tuntubi bangaren ita Zahra na ji
llah ya bada iko, idan kana da matsala da ni ka tunkare ni kai tsaye ka fada min ba sai ka laba da wasu ba
meen, na gode Allah ya kara lafiya
Bangaren Anty Amarya ya shiga ya labarta mata yadda suka yi da Mai Martaba, Anty ta numfasa cikin farinciki ta ce.
i gani nake kamar Lami ta shirya wannan abun, domin wacan karon na kasan a gaban yarta aka yi ina tunanin ita ta bata labarin sai ta saka aka shirya wannan saboda ta kara bata tsakaninka da Mai Martaba sai gashi Allah be cika mata wannan nufin ba, a yanzun ma ta yi haka ne saboda ta ga Mai Martaba be dauki wani mataki a kanka a madadi hakan na sai Allah ya shirya tsakaninku
o ma dai wanene za mu ji Inshallah asirinsu zai tonu
a yardar Allah kuwa, Mai Martaba yayi maka maganar tarewa?

Abiey ya shafa kansa.
ayi min yace kin masa magana
aka na ga ya dace, ace an nada maka sarautar matarka tana gidanka abun zai fi bada kala
ai dai ban san ko ita Zahra zata yarda ba
an gane zata yarda ba?

Kai ne fa mijin karka zama mijin tace mana kai da zaka bata umarni ta bi
Abiey yayi dariya.
i ni tun kan tace ne ma, Zahra haba Anty kamin tace ma na aikata
Haka suka yi ta hira cikin nishadi har suna tunawa da baya Anty tana tsokanarsa.

Sai azahar ya fita gidan ya bayan ya sake wanka ya feshe jikinsa da turare wai kar ya jewa amaryarsa yana karni kamar wanda be yi wanka safe ba.
Chapter 127 · 0% Book details